Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazari a Kan Hausar 'Yan Kurkura a Kasuwar Kantin Kwari Kano

Sashen Nazarin Harsuna Da Al’adu,  Tsangayar Fasaha Da Nazarin ƊAbi’un ƊAn Adam, Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara State, (Nuwamba, 2021)

NAZARI A KAN HAUSAR ‘YAN ƘURƘURA A KASUWAR KANTIN KWARI, KANO

NA

YUSIF MUHAMMED 

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aiki ga matata Maimuna Umar Gulu da ‘yata Amina Yusif Kwalli Kano. Ina fatan Allah Ya saka masu da alkhairi alfarmar Shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W).

GODIYA

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki, Mai kowa Mai komai da ya ba ni rai da lafiya da ikon gudanar da wannan bincike.

Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Fiyayyen halitta wato Annabi Muhammadu (SAW) tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da duk magoya bayansa tun farko ya zuwa ranar ƙarshe.

Godiya ta musamman ga dukkan bayin Allah da suka taimaka domin ganin wannan bincike ya kammala, musamman iyayena Malam Mamuda Mai Hula da Hajiya Suwaiba da Hadiza da Hajiya Habiba ‘yan uwana da abokan arziki maza da mata.

Bayan haka, ina godiya ta musamman ga malammaina, tare da yin jinjina garesu a kan irin yadda suka tarbiyantar da mu a fagen ilimi, musamman jagoran duba wannan aikin watoMalam Bashir Abdullahi yadda ya jure yin gyara har wannan bincike ya kammala. Allah Ya saka masu da gidan Aljannah, Allah ya faranta masu rayuwar su duniya da lahira amin. Malaman sun haɗa da; Prof. M. T. Yakawada Zaria, Prof. M. L. Amin Zaria, Prof. A. Balarabe Zaria, Prof. Aliyu Muhammadu Bunza UDUS, Prof. Aliyu Musa B.U.K, Dr. R. M. Tahir Zaria, Dr. Adamu Rabi’u Bakura, Mal. Rabi’u Aliyu Ɗangulbi, Dr. Musa Fadama Gummi, Mal. Isah S Fada,  Mal. Arabi Umar Mal. Abu Ubaida da kuma Malama Halimatu Kurawa da ma duk wani malami da ya koyar da ni wanda ban samu damar saka sunansa ba a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu da ma inda na yi aron kwas don cika sharuɗɗan karatu da wanda na sani ya taimaka da ban san ma ya taimaka ba ko da a tsaron jarabawa. Allah Ya saka masu da alheri, amin.

Godiya ga abokan karatuna da suka taimaka a fagen karatu, musamman Bilyaminu Abubakar Gusau, Aminu Muhammad Gusau, Abdulrashid Isma’il Kaduna, Mahadi Mustapha Gusau, Ibrahim Garba Gusau, Saudatu Ɗalhatu Sokoto, Binta Gambo Gusau, Asiya Sulaiman Gusau da Khadija Ɗanbuba Gusau da ma wanda bai ji na ambaci sunansa ba saboda rashin samun damar rattaba su a cikin wannan bincike. Na gode, Allah Ya saka masu da alkhairi, kuma Ya ƙara muna son juna. Allah Ya nuna muna wannan karatu ya amfani kowa daga cikin mu amin.

TSAKURE

Karin harshen Hausa ya ƙunshi yadda wasu rukunin mutane sukan aiwatar da lafuzansu. An kasa karin harshe zuwa gida biyu akwai manyan kashi: wato karin harshen yakin wanda ya ƙunshi Gabas da Yamma, sai kuma karin harshe na rukuni wanda ya ƙunshi rukunin wasu al’umma masu sana’a iri ɗaya. Wannan bincike ya mayar da hankali ne a kan karin harshe na rukuni,haka kuma an yi nazari ne a kan Hausar masu sana’ar tuƙa motar nan ‘yar ƙurƙura a kasuwar Kantin Kwari ta jihar Kano.Manufar wannan bincike ita ce, binciko sana’ar tuƙi na wasu rukunin matuƙa motocin nan da suke ɗaukarkaya a kasuwar Kantin Kwari da ke birnin Kano da bayyana yadda waɗannan matuƙa sukan yi amfani da harshen Hausa, musamman abin da ya danganci karin harshensu na sana’ar tuƙi.Fito da irin gudummuwar da wannan sana’ar ta bayar wajen bunƙasa harshen Hausa da samar da wani abin dogaro ga manazarta musamman waɗanda suke da ƙudurin gudanar da nazari a fannin al’adun da suka shafi sana’a da makamantansu.Sannan kuma an bi hanyoyin da suka dace wajen yin hira da masu sana’ar da kuma masu ilmi a kan sana’ar tare da bitar wasu abubuwan karatu da suka haɗa da littattafai da kundaye da mujallu. Haka kuma binciken ya gano cewa, akwai nau’in Hausar da matuƙa wannan mota ‘yar ƙurƙura sukayi amfani da ita. An yi bayanai a kan wannan a inda aka zo da wasu misalai da za su tabbatar da haka.

ƘUNSHIYA

TITTLE PAGE     -   - ii

TABBATARWA -   -      iii

AMINCEWA -   - iv

SADAUKARWA -   -     v

GODIYA -   -                  vi

TSAKURE -   -               vii

ƘUMSHIYA -   -   viii

BABINA ƊAYA

GABATARWA

1.0 SHIMFIƊA - -  - 1

1.1 MANUFAR BINCIKE -  - - 3

1.2 HASASHEN BINCIKE - -  - 4

1.3 FARFAJIYAR BINCIKE - -  - 4

1.4 MATSALOLIN BINCIKE - -  - 5

1.5 MUHIMMANCIN BINCIKE - - 6

1.6 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE  - 7

1.6.1 HANYOYIN TATTARA BAYANAI NA FARKO -  - 7

1.6.1.1 HIRA - -  - 8

1.6.1.2 ZIYARA - -  - 8

1.6.2 SAURAN HANYOYIN TATTARA BAYANAI -  - 9

1.7 NAƊEWA - -  - 9

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0 SHIMFIƊA - -  - 10

2.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA  - 10

2.1.1 BUGAGGUN LITTAFAI - -  - 11

2.1.2 MUƘALU DA MUJALLU - - 14

2.1.3 KUNDAYEN BINCIKE - -  - 16

2.2 HUJJAR CIGABA DA BINCIKE - - 17

2.3 NAƊEWA - -  - 18

BABI NA UKU

HARSHE, KARIN HARSHE, KANO, DA KANTIN KWARI.

3.0 SHIMFIƊA - -  - 19

3.1 HARSHE - -  - 19

3.2 KARIN HARSHE - - 21

3.2.1 MA’ANAR KARIN HARSHE - - 23

3.2.1.1 IRE-IREN KARIN HARSHE - - 24

3.2.1.1.1 KARIN HARSHE NA YANKI -  - 24

3.2.1.1.2 KARIN HARSHE NA RUKUNI -  - 25

3.3 TSOKACI A KAN TAƘAITACCEN TARIHIN KANO  - 27

3.3.1 KANTIN KWARI - - 30

3.4 NAƊEWA - -  - 32

BABI NA HUƊU

BAYANI A KAN SANA’AR TUƘI, MOTA ‘YAR ƘURƘURA, MATUƘANTA DA HAUSARSU

4.0 SHIMFIƊA - -  - 33

4.1 SANA’AR TUƘI - - 33

4.2 MOTA ‘YAR ƘURƘURA - -  - 35

4.2.1 IRE-IREN MOTA ‘YAR ƘURƘURA -  - 37

4.2.1.1 HOMA - -  - 38

4.2.1.2 ƁAUNA - -  - 38

4.2.1.3 ƘARAMIN KAI - - 39

4.2.1.4 ƁAUNA BI - - 40

4.2.1.5 RAWUN FITILA - - 40

 4.3 GUDUMMUWAR MOTA ‘YAR ƘURƘURA  - 41

4.4 HAUSAR MATUƘA MOTA ‘YAR ƘURƘURA -  - 42

4.5 HAUSAR MATUƘA ‘YAR ƘURƘUR DA MA’ANARTA A DAIDAITACCIYAR HAUSA -  - 45

BABI NA BIYAR

SAKAMAKON BINCIKE

5.0 SHAMFIƊA - -  - 47

5.1 SAKAMAKON BINCIKE - -  - 47

5.2 SHAWARWARI - - 49

5.3 NAƊEWA - -  - 50

MANAZARTA - -  - 53

HIRARRAKI - -  - 55

RATAYEN HOTUNAN MOTAR JIGILAR KAYA TA ‘YAR ƘURƘURA - - 56

Keke Napep

Post a Comment

0 Comments