Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene Ne Gaskiyar Maganar Jabun Kudi Na Shehu Ahmad Tijjani

TAMBAYA (100)

Mene ne gaskiya akan cewar Shehu Ahmad Tijjani ya buga kudin jabu. Muna buqatar amsa amman da hujjoji pls

AMSA

Bismillahir Rahmanir Rahim

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah SWT. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga cikamakon Annabawa, Annabi Muhammad SAW

Kowanne musulmi na gaskiya yasan cewar addinin musulunci addini ne wanda yake komai akan tsari, na koyarwar Qur'ani da hadisi, tareda ruguza bidi'a da tsayar da sunnah

Yanzu haka wasu sunyi nutso a cikin tekun bidi'a ta hanyar fifita shehunnai da kuma allantar da wasunsu. Buri na wannan amsar ta fargar da wasu yan bidi'a akan tarihin abinda ya faru ga shehun da suke bi alhalin sun gafala da abinda mutane masu binciken tarihi suka sani

Littafin Prof. Dahiru Maigari (Daga Islamic Dept. BUK, mawallafin littafin "Shaikh Inyass as-Singali da kuma littafin "ad-Dariqatut Tijjaniyya"), zai taimaka sosai wajen fito da hujjojin

Kamar yanda marigayi Shaikh Albany Zariya ya binciko, yace musamman Prof. Maigari yayi thesis din sa na PhD a wannan bangaren ma'ana shi a gidansu ya dingire. To amman abin mamakin shine, a lokacin da yayi wannan littafin saida yan dariqa suka so su kashe shi, saboda a cikin littafin yayi bayani da hujja cewar Shaikh Ahmad Tijjani ya taba buga kudaden jabu (forgery), hukumar kasar su ta kama shi, aka yi masa dukan tsiya, aka daure shi a kotu a karshe aka koreshi daga kasarsa

Yan dariqa sukai musun wannan labarin, (suka ce karya ne) nan da nan sai hukuma ta bincika kuma ta tabbatar da cewar anyi hakan (kuma yan kasar su Shehu Ahmad Tijjani din shaidu ne akan hakan). A karshe aka qarqare cewar indai aka kashe Prof. Dahiru Maigari to da sa hannunsu (yan dariqa) indai ba mutuwace irin ta Allah ba, dukkan yan dariqa suka sa hannu, Professors na BUK ma suka sa hannu. To ammanfa wai a hakan shi wannan Ahmad Tijjani din yake da mabiya miliyoyi a kasar da take da EFCC! Shaikh Albany Zariya yace "Da ni dan majalisar (tarayya) ne da sai na taso da wannan zancen wataran". Ku kula cewar Prof. Dahiru Maigari fa a gidan kaulaha ya girma, don haka babu kokwanto akan abinda ya faru tunda su ganau ne ba jiyau ba

~ inji Shaikh Albany Zariya (Rahimahullah)

Na tambayi Ambassador Muhammad Arab akan hukuncin dan Nigeria wanda ya buga kudin jabun, sai ya bani amsa kamar haka;

Toh, Shidai jabun kudi a tsarin dokokin kasa da Sharia ana masa laqabi da "Counterfeit" Wanda yake haramun ne a cikin dokokin Nigeria Wanda kowacce hukuma zata Kama mutum ta gurfanar dashi a ganaban Court domin hukunci.

A cikin kundin dokokin wato "CBN Act (2007)" Sashi na 20 hudu cikin baka wato (4) tayi magana a takaice kan cewa dukkan wanda aka Kama da Buga kudin bogi ko Amfani dashi ya zama wajibi a hukuntashi ta hanyar turashi zuwa gidan gyaran, Kuma kada yayi kasa da Shekara Biyar cikin wa'adin zaman da zaiyi acan.

Ga Yanda turancin yake a CBN Act 20027 👇

For the avoidance of doubt, Section 20(4) of the CBN Act (2007) as amended, states that: “It shall be an offence punishable by a term of imprisonment of not less than five years for any person to falsify, make or counterfeit any bank note or coin issued by the Bank which is legal tender in Nigeria.”

GA WASU KADAN DAGA HUKUNCE HUKUNCEN DA AKAYI BADA JIMAWA BA DA YADDA SUKA KASACE👇 

     21 August 2021

Wata Babbar Kotu dake zamanta a karamar hukumar Birnin Kudu ta nan Jihar Jigawa ta yankewa Farfesa Steve Uchella da Bonafice Afifa Oru hukuncin daurin shekaru 5 a gidan Yari bisa zargin su da laifin yin Jabun kudade.

An gurfanar da masu laifin a gaban alkali mai shari’a Musa Ubale, bisa laifuka guda uku da suka hada da hada baki da aikata laifuka da cin amana da buga jabun kudi.

kuma Kotun ta yanke musu hukuncin daurin shekaru 5 bisa Laifin hada baki da aikata laifuka da cin amana da buga jabun kudi, ko kuma su biya tarar Naira dubu 500,000 kowannen su.    

   23 February 2020

Wata kotun tarayya da ke zamanta a Yola, babban birnin jihar Adamawa, ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin daurin shekara 60 a gidan yari bayan an gurfanar da su bisa tuhumarsu da mallakar jabun kudi.

Jastis Abdulazeez Anka ne ya yanke wa mutanen hudu, da suka hada da mace guda daya, hukuncin bayan hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rasha wa ta gurfanar da su. Alkalin ya bayyana cewa zasu shafe shekaru 10 a gidan yari a kan kowanne laifi da suka aikata, kuma kotun ta same su da aikata guda shidda.

Allah swt ya karemu ya tsare mu daga mugunji da mugun gani tareda Mummunan Aiki.

Fatan Alkhairi

Bissalaam

©Boss Mohammed Arab (Saturday 23.12.2023)

Sannan kuma munsan a musulunce wannan laifin zamba ne kuma aikata zamba haramun ne

A bangaren littafin "Jawahirul Ma'ani" da yan Tijjaniyya suke kafa hujja kuma, Prof. Dauda Ojobi yayi bayani sosai akan asalin littafin. Kafin karanta bayanansa yakamata a fara sanin wanene Prof. Dauda Ojobi

Ya kasance Bishop ne kuma shine Former Secretary of Northern Christian of Nigeria (CAN) wato tsohon sakataren kiristocin arewacin Nigeria. Retired Professor Faculty din Law dake Jami'ar jihar Benue. Haka kuma shine Third Reverend Father daga arewacin Nigeria bayan Paul Gindri da GG Ganaka. Shine tsohon Commissioner of Justice a jihar Bauchi kuma tsohon shugaban Baptist Church na farko a Kaduna. A karshe Allah Azzawajalla ya shiryar dashi bisa tafarkin musulunci, daganan ya koma makarantar allo, a hankali a hankali ya samu ilimin addinin musulunci kuma ya zama silar musuluntar da dubunnan Christians ta hanyar amfani da Qur'ani, hadisai da kuma Bible. Professor Dauda Ojobi yana da PhD dai dai har guda 4. Ma'ana yanada BSc guda 6, MSc guda 6, PhD guda 4. Gaba daya Degree dinsa 16 kenan

Prof. Dauda Ojobi tsohon dan Tijjaniyya ne domin kuwa saida yayi shekaru 19 a dariqar Tijjaniyya, a karshe ya fita daga dariqar bayan ya gano illolinta ya koma Ahlus Sunnah, kamar yanda ya shaidawa al'umma a wani karatu da sukai tare da marigayi Shaikh Albany Zariya mai taken: "A INA GASKIYAR TAKE?". A karatun ne yayi bayanin cewar shi (Prof.) da kansa yake yiwa Ibrahim Kaulaha tausa idan yana hutawa, a lokacin da ya zauna a gidan Kaulaha, sannan kuma yayi bayani akan "Wanene Reverand Peter Jatau" da kuma "Wanene Mai Tatsine" sannan kuma yayi tsokaci akan "Salatil Fatih" da yan Tijjaniyya suke yi

Prof. Dauda Ojobi yace

"Akwai wani littafi mai suna Jawahiril Ma'ani wanda jahilai suke ta kashe kansu akansa, wanda ya wallafa wannan littafin Bishop ne kamar ni wato ba musulmi bane ba, dan kasar Misra ne (Egypt)"

Ya ci gaba da cewa: "Emperor Habacus na Rome, shi ya bashi ijara yaje ya fitarda abinda zai batar da musulmai ta hanyar tusa musu wani ra'ayin a zuciyarsu. Sunansa Bishop Salvan Gregory. An wallafa littafin Jawahiril Ma'ani a shekarar 1892 A.D wanda yayi daidai da 1260 A.H a karkashin censorship na Emperor Habacus dake kasar Rome. Idan zaka tabbatar da wannan zance sai kaje ka duba littafin Roman Catholic Encyclopedia 1940 Volume 8, page 109"

"Littafin Jawahiril Ma'ani sashin Antagonism ne, sannan kuma (duk dalibin ilimi yasan) Annabi SAW baiyi maulidi ba, hakama sahabbansa da tabi'ai da atba'ut tabi'in duk ba wanda yayi, amman wanda yayi Maulidin Naby da farko a shekarar 597 A.H (Anno Hegira) wanda yayi daidai da 1211 A.D (Anno Domini) shine Bishop Hezakaya Volak ya qirqiro Maulidin Naby a karon farko, mutumin kasar Turkey ne. Don haka idan kana son ka kara nazari sannan ka tabbatar da hakan saika duba cikin littafin Roman Catholic Encyclopedia 1940 Volume 8, page 18,112"

"Idan maulidi musulunci ne to me zai kai asalinsa cikin littafin Roman Catholic Encyclopedia, har ma ya samu fassararsa daga wajen?"

Anan maganar Prof. Dauda Ojobi ta tiqe

(Ka duba kaset din marigayi Albany mai taken: "A INA GASKIYAR TAKE?")

Wancan "Jawahirul Ma'ani kenan to ina kuma ga idan ka duba littafin "Jawahirul Masa'id" wallafar Ibrahim Inyas?

Ni dai a iya dan karamin sani na, idan mutum ya buga kudin jabu (forgery) babban laifi ne, wasu kasashen ma kashe mutum suke yi.

To yanzu tambaya ta farko anan itace; su yan dariqa me yasa basa binciken asalin abu saidai kawai su dinga aiwatarwa ba tare da neman ilimi akan abin ba. Sannan kuma tambaya ta biyu itace; me yasa shehunnansu suka boye musu wannan al'amari na jabun kudi da Shehu Ahmad Tijjani ya taba bugawa har aka koresa amman a haka miliyoyin mutane suke bin dariqarsa ta Tijjaniyya?

Muna roqon Allah ya rabamu da bidi'a ya tabbatar damu akan musulunci bisa sunnar Annabi SAW kan fahimtar Salaf (Magabatan farko)

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments