Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Gyara Ubangijina,Ya Allah Sarkin Gabas
da Yamma.
Gyara Ubangijina,
Gyara Allah Sarkin
Gabas da Yamma,
Allah mai Kudu mai
Arewa,
Ya Allah Ubangijinmu,
Gyara.
Ku doka tambura,
Ku ƙara tambura,
Ku doka tambura,
In ka ji tambura,
Ai an ga babba zaune,
In ka ji tambura,
An game da manya.
Wamako za ni gobe,
Don darajar Alun
Magatakarda,
Huta da lafiya lau.
Wamako za ni sauka,
Don darajar Alun
Magatakarda,
Ya Allah kyauta
zamaninka,
Ka kyauta wa Sani mai
kalangu,
Abin da kake min,
Na yaba da kyauta.
Ya Allah ya kyauta
zamaninka,
Huta da lafiya lau,
Mijin Arziki sai
godiya nake ma,
Mijin su Atika,
Na yaba da kyauta,
Ya na Atika Alun
Magatakarda,
Ya Allah ya kyauta
zamaninka,
Alun Hassa yana nan,
Ya kyauta wa Sani mai
kalangu,
Dan Darajar Alun
Magatakarda.
Ada mai fetur,
Ada mai fetur
Arkilla,
Na yaba mai,
Dean darajar Alun
Magatakarda a fili.
Huta da lafiya lau,
Ya Allah ya kyauta
zamaninka,
Huta da lafiya lau,
Jan zaki Alun
Magatakarda.
Allah shi ma, Ah!
Shekaran jiya,
Na yi mafarki
Ya maƙi garaje,
Ya Allah ya kyauta
zamaninka,
Na Audu Sifika godiya
nake ma,
Yayan Audu,
Yayan Audu na yaba da
kyauta,
Audu sifika ina yaba
ma,
Don darajar Alun
Magatakarda.
Ya ba ni kuɗi,
Ya ƙara kuɗi,
Ya ba ni kuɗi,
Kuma yaaa haɗa da riga,
Don darajar Alun
Magatakarda a fili.
Marigayi Dingyaɗi na yaba ma,
Sannu diji na yaba da
kyauta,
Sannu na Tambari maƙi garaje,
Ya Allah ya kyauta
zamaninka,
Ka kyauta ma Sani mai
kalangu,
Alun Magatakarda.
Haƙin sama sai raƙumi,
Akuya na so ba ta
iyawa,
Akuya na so wuyanta
bai kai ba,
Ta koma ta ci hakin
da lasa dole.
Ya gyra gida,
Ya gyara dawa,
Ya bai wa gida,
Ya bai wa dawa,
Na gode Alun
Magatakarda.
Ya gyra gida,
Ya gyara dawa,
Ya bai wa gida,
Ya bai wa dawa,
Na gode Alun
Magatakarda.
Ya bai wa ‘yan gida,
Ya bai wa baƙi.
Ya Allah shi biya ka
darrajan ma’aiki,
Sannu Diji Alun
Magatakarda,
Allah ya kyauta
zamaninka,
Godiya nake yi,
Ina Alun Hassan?
Ina Alun Hassan?
Na yaba da kyauta,
Dan darajar Alun
Magatakarda.
Ada Arkilla,
Na yaba ma,
Domin darajar Alun
Magatakarda,.
Audu kamsila, kakakin
majalisa ne,
Audu kamsila,
Kuma kakakin majalisa
ne,
Mai ba ni kuɗi,
Ya ba ni kuɗi,
Ya ƙara kuɗi,
Ya haɗa da riga,
Don darajar Alun
Magatakarda a fili.
Huta da lafiya lau,
Hakin sama sai raƙumi mutane,
Akuya na so ba ta
iyawa,
Ta koma ta ci hakin
da lasa.
Yi musu hairan,
Ka mai da sharri,
Kar ka damu.
Gyara Ubangijina,
Gyara Allah Sarkin
Gabas da Yamma,
Allah mai Kudu mai
Arewa,
Ya Allah Ubangijinmu
gyara Allah.
Ku doka tambura,
Ku ƙara tambura,
Ku doka tambura,
Da ka ji tambura,
Ai an ga babba zaune,
In ka ji tambura,
An game da manya.
Wamako za ni gobe,
Domin darajar Alun
Magatakarda,
Huta da lafiya lau.
Wamako za ni sauka,
Domin darajar Alun
Magatakarda,
Ya Allah ya kyauta
zamainka,
Ka kyauta wa Sani mai
kalangu,
Abin da kake,
Na yaba da kyauta.
Ya Allah kyauta
zamaninka,
Huta da lafiya lau.
Mijin su Arziki sai
godiya nake ma,
Mijin su Atika na
yaba da kyauta,
Ya na Atika
Magatakarda,
Ya Allah ya kyauta
zamaninka.
Alun Hassan yana nan,
Ya kyauta wa Sani mai
kalangu,
Don darajjar Alun
Magatakarda.
Ada mai fetur,
Ada mai fetur,
Arkilla na yaba mai,
Don darajjar Alun
Magatakarda.
Huta da lafiya lau,
Ya Allah kyauta
zamaninka,
Huta da lafiya lau,
Jan zaki Alun
Magatakarda.
Allah shi yi ma,
Eyeh!
Shekaran jiyua,
Na yi mafarki,
Sannu na Atika maƙi garaje,
Ya Allah ya kyauta
zamaninka.
Na Audu sifika godiya
nake ma,
Yayan Audu,
Yayan Audu na yaba da
kyauta,
Audu sifika ina yaba
ma,
Don darajjar Alun
Magatakarda.
Ya ba ni kuɗi,
Ya ƙara kuɗi,
Ya ba ni kuɗi,
Kuma ya yaɗa da riga,
Don darajjar Alun
Magatakarda.
Maigari Dingyaɗi na yaba ma,
Sannu Diji na yaba da
kyauta,
Sannu na Tambari maƙi garaje,
Ya Allah ya kyauta
zamaninka,
Ka kyauta wa Sani mai
kalangu.
Alun Magatakarda,
Hakin sama sai raƙumi mutane,
Akuya na so ba ta
iyawa,
Akuya na so wuyanta
bai kai ba,
Ta koma ta ci hakin
da lasa dole.
Ya gyara gida,
Ya gyara dawa,
Ya bai wa gida,
Ya bai wa dawa,
Na gode Alun
Magatakarda,
Ya gyara gida,
Ya gyara dawa,
Ya bai wa gida,
Ya bai wa dawa,
Ya bai wa ‘yan gida,
Ya bai wa baƙi.
Ya Allah shi biya ka
darrajar Ma’aiki,
Sannu Diji Alun
Magatakarda,
Ya Allah ya kyauta
zamaninka,
Godiya nake yi.
Ina Alun Hassan,
Ina Alun Hassan,
Na yaba da kyauta,
Don darajjar Alun
Magatakarda.
Ada Arkilla,
Na yaba ma,
Domin darajjar Alun
Magatakarda.
Audu kansila,
Kakakin majalisa,
Audu kansila,
Kuma kakan majalisa.
Mai ba ni kuɗi,
Ya ba ni kuɗi,
Ya ƙara kuɗi,
Ya haɗa da riga,
Don darajjar Alun
Magatakarda.
Huta da lafiya lau,
Hakin sama sai raƙumi mutane,
Akuya na so ba ta
iyawa,
Ta koma ta ci hakin
da lasa,
Ah!
Ka musu hairan,
Ka mai da sharri,
Kak ka damu da su
Magatakarda,
Ka san yaro ba ya kai
ga babba.
Canjin rauji da kiɗa
Yaƙi noman sarki,
Tafiya noman falke,
Yaro kauce a faɗa maka,
Manya sun zo da
shiri.
Mu koma BK don in ga Habu babana,
Mu koma BK don in ga Habu babana,
Sannu DG ka kyauta min da yawa,
Allah shi yi ma
sutura,
Yadda kau wa Sani
bahago,
DG na gode ma,
DG ka kyauta min.
Manya kanun gayya,
Mu koma BK don in ga Habu babana,
Sannu DG ka kyauta min da yawa,
Allah shi yi ma
sutura yadda kau wa Sani bahago,
DG na gode ma,
Baban Lawal Habu,
Ah!
Baban Lawal Habu mai
kwana da shiri,
Yadda kai wa Mamman
gaishe ka nake,
Allah shi yi ma
sutura yadda kau wa Sani Bahago.
Ranan Alhaji Mamman
Sani,
Na zo in wuce ishe DG Garba,
Da nas same shi,
Eyeh!
Rananan a ofis naz
zo,
Wani a yag ga Mamman
Sani,
Sai yac ce mani
Mamman Sani,
Mi ya sa ba ku bar roƙo ba,
Ah!
Sai nac ce,
Sha’anin duniya kowa
da abin da ya dame sa,
Sha’anin duniya kowa
da abin da ya dame sa,
Wasu sun ce roƙo zunubi ne,
Wasu sun ce roƙo zunubi ne,
To amma ba mu musu,
Mun yadda da roƙo zunubi,
Amma matambayi ba ya ɓata,
Don haka na yi
tambaya,
A faɗa mini rowa ladarta
nawa?
Wai shi mai rowa ladassa
nawa?
Mai rowa maƙiyin Allah ne,
Ba shi ganin Annabi,
Saboda azaba ɗai anka yi shi.
Kowas sami abin
duniya,
Yaz zama ya cinye shi
ɗai,
Da ya mutu ya san
wahala –
Ta ɗauko gammo ta kai shi
ƙasa.
Shi ɗai zai mutuwa,
A kwasai a saka rami,
A ƙyale shi ciki,
Walakiri ya iske shi
gida,
Ya sa mishi sarƙa ta wuta,
Ya lanƙwashe hannunsa ciki,
Ya huje gaba nai
hannun ya shige,
Ya huje baya,
Sai a faɗa mashi rowa tak kai
shi haka.
DG na gode ma,
DG Garba,
Wanda ya samu kuɗi,
Ko da yaushe ya sauka
gida,
Ka kama mu ƙwarai ka riƙe,
Yadda Allah ya yi ma
sutura.
DG Garba,
Garba da ya samu kuɗi,
Ko da yaushe ya ɗauki ɗiyan jama’a,
Ka kama mu ƙwarai ka riƙe,
Yadda Allah ya yi ma
sutura.
Awaikin dutsi ka gagari ‘yan yara ado,
Awaikin dutsi ka gagari ‘yan yara ado,
Kuma ka yi wa
manyansu gwaram ga wuya.
Arna tsoron ka suke,
Ga yaƙi kai an ka sani.
DG na gode ma,
Sannu Habu ka kyauta,
Yadda kai wa Mamman
Sani bahago.
Allah shi yi ma
sutura,
Habu mai kwana da
shiri,
Ah!
Alƙali Mustafa uban ɗakina,
Yadda yai mini ya
kyauta min da yawa,
Domin Baba mai kwana
da shiri.
Audu na Binji ya
kyauta min,
Bam mance da Bala
zaki ba,
Bala zaki ya kyauta
min,
Bala zaki ya kyauta
min da yawa.
Allah shi yi mai
sutura,
Yadda yai wa Sani
bahago,
Ah!
Almu na Jega ka
kyauta min,
Alhaji Almu na Jega
ka kyauta min da yawa,
Allah shi yi ma
sutura yadda kau wa Sani bahago.
Da uban gari na gode
ma,
Yusuf ka kyauta min.
Mu koma BK don in ga Habu babana,
Sannu DG ka kyauta min da yawa,
DG Garba,
Yadda kai wa Mamman gaishe
ka nake,
Allah shi yi ma
sutura yadda kau wa Sani bahago.
Yaƙi noman sarki!
Canjin rauji da kiɗa
Taimaka Rabbana,
Ya Jalla ka ceci ‘yan
zamani,
Ikon Allah ka tserad
da mu,
Ka Hana mu ɓata,
Ka ganad da mu
gaskiya.
Taimaka Rabbana,
Ya Jalla ka ceci ‘yan
zamani,
Inji mai waƙa uban Zainaba, Sani.
Abin mamaki bai kamaƙ ƙarewa malam,
Abin mamaki bai kamaƙ ƙarewa,
Sai kullum ƙaruwa za ya yi,
In kana yawo
gari-wa-gari,
Inda duk ka shiga.
Taimaka Rabbana,
Ya Jalla ka ceci ‘yan
zamani,
Ikon Allah ka tserad
da mu,
Ka hana mu ɓata ka ganad da mu,
gaskiya.
Abin mamaki bai kamat
ƙarewa,
Inda duk kash shiga,
In kana yawo
gari-wa-gari,
Sai ka iske mutum
cikakken mutum,
Ka sami mutum kamak
kamili,
Hannu na mutum, ƙafafun mutum,
Kai nai na mutu,
idanun mutum,
In ka duba cikin
zuciya tai,
Sai ka ga gwamma kura
da shi,
Ka gane irin harkag
ga sai Rabbana,
Sha’anin duniya wuya
ag garai,
In ka yi kure akwai
‘yar ‘yar wuya.
Sai ka samu mutum
kamaj jarumi,
In ka duba cikin
zuciya tai,
Sai ka ga gwamma
raggo da shi,
Sha’anin duniyag ga
sai Rabbana.
Taimaka Rabbana.
Yo gaba malam in yi
zance da kai don Allah.
Yo gaba malam in yi
zance da kai don Allah,
Amma inji mai waƙa uban Zainaba,
Sha’anin duniya wuya
ag garai.
Idan ka ga mutum kana
ra’ayi nai, malam,
Wai kan da ku zan
jiki dai da shi,
Na so ka yi bincike
nai kaɗan,
Kuma ka bar dubin
huska da kaurin jiki,
Kai dai ka yi
binciken zuciya,
Da irin halin da duk
ag garai,
Ka san cinikin ɗan Adam wuya ag
garai,
Ko an bar ma sule
goma,
A cikin naira rage
‘yab biyar,
Ka gane kana zaton faɗuwa wata rana.
Wasu sun yi gamon
katar,
A cikin suɗi sun tsinci guru
guda,
Ku tsaya ku raba shi
kowa ya ci,
In anka raba a sam
min ƙashi ni dai.
Wasu sun yi haƙo cikin rijiya,
Wai sun aza gargaza
ta shiga,
Suka kamo talibambam
guda,
Da anka taɓa shi yak kumbure.
Taimaka Rabbana,
Ya Jalla ka ceci ‘yan
zamani,
Sha’anin duniya wuya
ag garai, Sani.
Wasu sun ce roƙo wuta ag farai,
Zunubinsa yana da
dama cike,
Amma in anka yi
binciken zuciya,
Han na san, Ah!
Na san wani Sani,
Gwamma Sani da shi.
Ni na san wani gwamma
dai,
Na san wani gwamma
Sani da shi,
Taimaka Rabbana,
Ya Jalla ka ceci ‘yan
zamani,
Ikon Allah ka tserad
da mu,
Ka hana mu ɓata ka ganad da mu,
gaskiya.
Ka ga ana wata,
Ga wata ta fita,
Inji mai waƙa uban Zainaba,
Wai mutum shi yi ma
rowa ya yi fushi da kai,
Don Allah kak ka yi
min rowa ka yi fushi da ni,
Idan kai min rowa kai
fushi da ni,
Komi yaf faru kai kab
biɗa,
Babu ruwan Mamman
uban A’isha.
Kyauta sai Allah
cikin lokaci malam,
Kyauta sai Allah
cikin lokaci,
Shi ya ba ka uwa ya
ba ka uba,
Shi yi ma mata ta yi
ta haihuwa,
In an ce wane ɗan wane ne,
Kuma sai an ce uban
wane ne,
Irin hikiman ga sai
Rabbana,
Shi ɗai.
Taimaka Rabbana,
Ya Jalla ka ceci ‘yan
zamani,
Ikon Allah ka tserad
da mu,
Ka hana mu ɓata ka ganad da mu,
gaskiya.
Alhaji Garba na
Gwaggo ka taimaka,
Na gode ma,
Habu jikan Jatau a
gaishe ka dai,
Ɗan Tabawa kana da
halin yabo,
Allah ya biya ka don
Rabbana,
Amin, inji mai waƙa uban Zainaba.
Magajin Ƙirgi Sani,
A gaishe ka na gode,
Wanda ban taɓa raina irin
kuzarinsa ba.
Ummaru Boɗinga ya taimaka,
Yanda yai wa Aliko,
Wanda ban taɓa raina irin
kuzarinsa ba.
Taimaka Rabbana,
Ya Jalla ka ceci ‘yan
zamani.
(canjin rauji la kiɗa)
Gyara Jalla mafi
girma,
Ya Allah ka kiyaye
mu.
Yaƙi noman sarki,
Tafiya noman falke,
Ku riƙa dai ‘ya’yana,
Kowa ya gaji bai saba
ba,
Dole wan naƙi.
Tafiya noman falke,
A gwada domin noma,
Kowa ya san kowa.
Haba yara mu koma
Agwada ya fi,
Haba yara mu koma
Agwada ya fi,haba yara mu koma Agwada birni.
Tun ban zo Agwada ba,
Ana labarin Agwada
kullum.
Tun ban zo Agwada ba,
Ana labarin Agwada
kullum.
An ce Agwada dawa,
Kuma an ce Agwada
gero,
An ce Agwada naira,
Kuma an ce Agwada
maiwa,
An ce Agwada ilimi,
Kuma an ce Agwada
shanu.
Da na je Agwada,
In gwada musu waƙa da kiɗa tsantsa.
Da na je Agwada,
In gwada musu waƙa da kiɗa tsantsa.
Mutanen Agwada,
Sun gwada mana
aikinsu zuwa gona.
Dubi da mai ɗari hadda bakwai
daidai,
Dubi da mai ɗari hadda bakwai
daidai,
Suka bai wa Bahagon
Indo,
Kuma ga wan tauzan ka
daɗa,
Domin nono da siga
Sani.
Ba ni koma zuwa gona,
Ba ni koma zuwa gona,
Na futa da yini rana,
Ah!
Idan na ji yunwa
Agwada nay yi.
Ko ba ni ba,
Ni mai waƙa da kiɗa Sani,
Kowa ya ji yunwa,
A gwada masa hanyar
Agwada birni,
In ka ji yunwa a
gwada maka hanyar Agwada birni,
Da ka zo Agwada,
Su gwada maka shago
da dawon gero,
Da nono da siga kai ɗai.
Haba yara mu koma
Agwada ya fi.
Yaƙi noman sarki,
Inji Sani bahagon
Indo.
Yaƙi noman sarki,
Inji Sani bahagon
Indo.
Yaƙi noman sarki,
Inji Sani bahagon
Indo.
Aikin tafiya,
Falke aka bar wa da
mutane nai.
Sha’anin duniya,
Kowa ya bi hanyar da
yake tsira.
Sha’anin duniya,
Kowa ya bi hanyar da
yake tsira.
Ko waƙ ƙi ka da ɗa,
Ya gane ka da jikanka
kana tawai,
Kuma ba ya da halin
ya taɓa ma shi.
Sha’anin duniya,
Kowa ya bi hanyar da
yake tsira,
Sakkon sallai,
Ba shi ke maishe ka
Musulmi ba.
Mutum na salla,
Zuciyarsa ta zam ba
ta Musulmi ba.
Amma inji Mamman
bahagon Indo,
Amma inji Mamman
bahagon Indo.
A bayar a rasa,
Ita ke hana yaro ka
ji motsi nai.
A bayar a rasa,
Ita ke hana raggo ka
ji motsi nai.
Allah wadaran samun
raggo,
Bai ci ba bai sha ba,
Bai tsere wa abokai
ba.
Amadun Rikiji ɗan Cindo,
Allah ya kiyaye ka,
Na gode ka taimaki
gangata.
Yadda kai mini,
Ka taimaki gangata.
Sannu Audu Magajin
Agwada sakko,
Tsartsatsa bahagon gulbi,
Ka ci gwani dud da
jirage nai,
Na san ba ka barin
bami.
Yara ina ɗan mutuwa Ada,
Mai fetur,
Na Haɗiza ka taimaki
gangata.
Sale ɗan mai daji,
Allah ya kiyaye ka.
Mijin Manga na gode,
Ka taimaka wa ƙanin Indo,
Ban raina maka kyauta
ba,
Ya Allah ya kiyaye
ka.
Kansilan Agwada Umar,
Ya taimaki gangata,
Na gode.
Sani hayaƙi na gode,
Allah ya kiyaye ka.
Ummaru mai zani na
gode,
Karkarak ku karakarar
mata ce,
Inda kag ga maza to
katarike su,
Alkla ya kiyaye ka,
Ka kyauta wa ƙanin Indo,
Sarkin maƙera na gode,
Eyeh!
Sani na Sarkin Maƙera na gaishe ka,
Ka taimaki gangata,
Haba yara mu koma
Agwada ya fi,
Haba yara mu koma
Agwada birni.
Ado mai shayi yadda
yai mini,
Allah ya kiyaye ka,
Ya kyauta wa ƙanin Indo,
Allah ya kiyaye ka.
Mani DPOn Kwatarkwashi,
Mani DPOn Kwatarkwashi.
Sannu jijin Zainab,
Mijin Hajiya Rabi a
gasihse ka,
Mani mai Allah.
Mijin Hajiya Rabi a
gaishe ka,
Mani DPOn,
Mani DPOn Kwatarkwashi.
Eyeh!
Yara mu je yawo,
Kwatarkwashi ga Mani DPOn da gaishuwa.
Yara mu je yawo,
Kwatarkwashi ga Mani DPOn da gaishuwa.
Ya Allah shi yi ma
sakayya,
Abin da kake malam.
Ya Allah shi yi ma
sakayya,
Abin da ka wa Mamman,
Sannu mijin Zainab,
Mijin Hajiya Rabi,
Mijin Binta,
Gira sai Allah.
Mijin Hajiya Rabi,
Mijin Binta,
Gira sai Allah.
Dattijo sannu mijin
Zaiban,
Na Adamu na gode da
gaskiya.
Mani DPOn,
Sannu nake kun na
wace,,
Sannu nake kun na
wuce,
Riƙa ƙwarai,
Mani DPOn,
Yadda kai wa Sani na
gode,
Riƙa ƙwarai.
Ku sa mana tamburan,
Ku sa mana tamburan,
Amma saboda Mani DPOn,
Ku sa mana tamburan.
Nahuce mu je yawo,
Nahuce gariu za ni,
Amma saboda mani DPOn,
Nahuce gariu za ni,
Amma saboda mani DPOn,
In ba shi a Nahuce,
Haba yara ku zo hanya
mu wuce.
In ba shi a Nahuce,
Haba yara ku ɗau hanya mu wuce,
Kwatarkwashi.
Ina Mamman Rikiji?
Yara ina Mamman
Rikiji Kwatarkwashi?
Yara Mamman Rikija,
Na Sa’adatu Sani ya
gode,
Na Sa’adatu giwa sai
Allah,
Yadda kai mini na
gode da gaskiya.
Mani DPOn.
0 Comments
Rubuta tsokaci.