Ticker

6/recent/ticker-posts

Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III

Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III

"Dauri mun ji daɗin zama da kai,
Yanzu mun ji zahin rabo dakai,
Garba Ɗan Hassan ko da baka nan dud darajak ka ta jicce duniya" 

Inji Makaɗa Abdun Inka Yarkofoji, Bakura a faifansa na Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III mai amshi 'Sarkin Musulmi Abubakar, Allah ya gammai da gahwara'. Yau, 1/11/2023 shekaru 35 Cif da wafatin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III domin ya rasu ne Ranar 1/11/1988. Allah ya jaddada masa rahama shi da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

Post a Comment

0 Comments