Ticker

6/recent/ticker-posts

Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Na 18, Alhaji Ibrahim Dasuƙi

Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Na 18, Alhaji Ibrahim Dasuƙi
Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Na 18, Alhaji Ibrahim Dasuƙi ya cika shekaru 7 da wafati. Allah ya jaddada masa rahama shi da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
****
Ibrahimu zauna lahiya
Gidan Shehu annan ka rike 
Amshi; Maimartaba dan Amadu
Sarkin Musulmi zani bi
👆🏽Wakam Maidaji ga Sarki Dasuki
*****
"Bai hito wurin banza kuma bashi batun banza
Hali nai halin Buharin Shehu ya kan yi

Daga alheri sai addini sai kau ya kwan salati da tasbaha tai

Allah shi baka albarka Shehu dan Fodio, Ibrahim 

Allahbshi baka albarkat Buhari dan Shehu, Ibrahim 

Allah shi baka albarkat Bara'u dan Buhari, Ibrahim 

Allah shi baka albarkat Haliru dan Bara'u, Ibrahim
Ka samu albarkak kakannin ka 
Allah Ya hukunta
Haka nan kowa yaka rok'o 
Kullun haka nan kowa yaka rok'o 

Tsakani nai da Shehu Usmanu ba nisa garai ba

Barade, tsakani nai da Shehu Usmanu ba nisa garai ba

Shehu shi yah haihi Buhari 

Buhari shi yah haihi Bara'u 

Bara'u shi yah haihi Haliru 

Haliru shi yah haihe ka

Ba nan duniya ba hal lahira darajjag gidan ku kowa ya kata rok'o" - Dankwairo

Daga:
Zauren Makaɗa da Mawaƙa

Post a Comment

0 Comments