Karya Azumin Nafila

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wanda ya saba yin azumin Litini da Alhamis sai ran nan ya kwana da kishi, kuma sai ya tashi a makare, da tashinsa sai ya sha ruwa, to wai ko zai iya cigaba da azumin ranar?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

    A cikin Ayar Azumi abin da Allaah Ta’aala dai ya ce, shi ne

    وَكُلُوا۟ وَٱشۡرَبُوا۟ حَتَّىٰ یَتَبَیَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَیۡطُ ٱلۡأَبۡیَضُ مِنَ ٱلۡخَیۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ ثُمَّ أَتِمُّوا۟ ٱلصِّیَامَ إِلَى ٱلَّیۡلِۚ

    Kuma ku ci, kuma ku sha har sai farin zare ya bayyana muku daga baqin zare na alfijir, sannan sai ku cika azumin zuwa dare. (Surah Al-Baqarah: 187).

    Wannan ya nuna

    1. Tsawon lokacin yinin azumi yana farawa ne daga hudowar alfijir na-gaskiya har zuwa farkon dare, wanda ke tabbata da faduwar rana a yamma.

    2. Kuma wajibi ne ga mai azumi ya kame daga cin abinci ko shan abin sha ko saduwa da sauran abubuwan da suke karya azumin a iya tsawon wannan lokacin.

    3. Duk wanda ya sha wani abin sha ko ya ci wani abinci ko ya yi saduwar jima’i da gangar a cikin tsawon wannan lokacin, to azuminsa ya ɓaci.

    4. An ce ‘da gangar’ ne a nan, domin akwai nassoshin da suka nuna cewa: Idan mutum ya karya azumin ne da mantuwa ko kuskure ko tilasci, to azumin bai ɓaci ba.

    5. Sannan kuma wannan ka’idar haka ta ke ko azumin na farilla ne ko na nafila, ba mu san wata magana da ta bambanta azumin nafila da na farilla a cikin hakan ba.

    A wurin maganar kwana da niyyah ne malamai suka nuna cewa akwai sassaucin mai azumin nafila ya fara daga hantsi, amma da sharaɗin bai ci komai ba tun daga asubahin wannan yinin.

    Don haka, abin da ya wajaba a kan wanda ya sha ruwa a bayan ketowar alfijir na gaskiya ko da kuwa a azumin nafila ne, shi ne ya a jiye wannan azumin nasa.

    Idan kuma daga baya ya samu dama sai ya rama shi a wani yinin, idan ya ga dama, tun da dai nafila ce.

     WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.