Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mafarkin Saduwa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum mallam inada tambaya idan mutum yayi mafarkin Yana saduwa Amma ko a mafarkin bai zubar da maniyyiba shin wankan janaba ya wajabta a kansa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Walaikumus salamam Warahmatalahi wabarkatahu

Fitar maniyyi a cikin bacci ko a farke, daga namiji ko mace ta hanyar lafiya da jin daɗi, saboda hadisi Idan ruwa ya fita ayi wanka, Muslim da Abu Dauda, wato idan ruwan maniyyi ya fita ayi wankan janaba.

Idan Mutum yayi mafarki yana saduwa da mace amma da ya farka babu alamar fitar maniyyi babu wanka akansa.

Idan mutum yayi mafarki yana saduwa da mace bayan ya farka sai yaga maniyyi a jikinsa wajibi yayi wanka.

Idan ya tashi daga barci sai yaga maniyyi a jikin sa amma bai yi mafarkin saduwa ba, wajibi ne yayi wanka saboda samuwar maniyyi a tare da shi, wanda fitarsa tana jawo wanka.

Idan mutum yaga maniyyi a jikin kayansa amma bai tuna lokacin da yayi mafarki ba sai yayi wanka ya rama sallar da yayi daga lokacin da ya kwanta wannan baccin da yayi mafarkin.

Saduwa tsakanin mace da namiji ya shigar da gabansa a cikin gaban mace, wajibi suyi wanka ko da maniyyi bai fito ba.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace Idan Kaciya biyu ta haɗu wanka ya wajaba, ko maniyyi bai fito ba.

Idan mutum ya rungumi matarsa suka yi wasa kawai babu saduwa kuma maniyyi bai fito ba babu wanka akansu saboda rashin dalilin wanka guda biyu fitar maniyyi ko Kuma shigar da kaciyar namiji cikin farjin mace. Idan ba'a sami ɗayan biyu ba babu wanka.

Idan maniyyi ya fitowa mutum ta hanyar rashin lafiya ko wata larura ko aka yi masa wata allura domin a ɗauki maniyyi a jikinsa, duka wannan babu buƙatar yin wanka, saboda rashin fitar maniyyi ta hanyar sha'awa.

Idan mutum ya ga wani abu a jikinsa, amma yana shakka maniyyi ne koba maniyyi bane sai ya shinshina idan ya sami yakini ko zato mai ƙarfi cewa maniyyi sai yayi wanka domin ya fita daga kokwanto.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments