Ticker

6/recent/ticker-posts

Zai Iya Yin Addu’a Allah Ya Fitar Da Tsohuwar Budurwata Daga Gidan Mijinta Domin Na Aure Ta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Mun yi soyayya da budurwata6 amma a ƙarshe sai ta auri wani, ni kuma na auri wata. A yanzu kuma bana jin daɗin zama da wacce na aura, ita ma haka. To, ko zai iya yin addu’ar Allaah ya fitar da tsohuwar budurwarta daga gidan wancan mijin domin na aure ta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul Laah

1. Da farko: Lallai ya san cewa, yana daga cikin Imani da Ƙaddara ya amince tun daga zuci har baki zuwa ga gaɓoɓinsa cewa: Duk abin da ya same shi, da ma can ba a ƙaddara cewa zai kuskure masa ba. Haka kuma duk abin da ya rasa shi, to da ma can ba a ƙaddara cewa abin zai same shi ba ne. An gama rubuta komai na ƙaddara tun shekaru dubu hamsin (50,000) kafin a halitta duniya, an ɗauke alƙalamin rubutun kuma takardun sun bushe.

2. Na-biyu: Bayan an ɗaura wa tsohuwar budurwarsa aure da wani, babu sauran alaƙa a tsakaninsa da ita. Don haka haram ne ya riƙa hira da ita ta waya ko kuma ta wata hanyar kamar ya zauna da ita suna hira a wani wuri, ko da me, ko don me. Kai! Ko komawa da yin bincike a kan yadda take rayuwa a cikin gidan mijinta ma bai kamace shi ba.

3. Na-uku: Wajibi ne iyaye da waliyyan ma’aurata su daina barin masu neman auren juna suna ƙulla soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu, ta yadda rabuwa zai zama musu alaƙaƙai daga baya. Kodayake a galibi su masoyan ne suke ƙulla soyayyar a tsakaninsu ba tare da sanin iyaye ko manya ba. Amma dai dole a hana su, a ja musu kunne a duk lokacin da aka gano hakan, musamman ma idan an san ba za a amince da aurensu ba.

4. Na-huɗu: Lokacin da aka aura mata wani mijin, shi kuma aka aura masa wata matar, to abin da ya kamace su shi ne haƙuri da juriya kawai, tare da adduar fatan ɗorewar zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin kowannensu da abokin zaman aurensa. Sai kuma yin tsayin daka domin gyara zaman iyalinsu a halin da suka samu kawunansu da gwargwadon ƙarfi da iyawa.

5. Na-biyar: Babu wata addu’a a tsakaninsu sai ta fatan alkhairi da neman Allaah ya sanya wa kowannensu albarka a cikin rayuwarsu ta duniya da barzahu da lahira, ita ma sai in ta zama dole. Amma neman wai Allaah ya fitar da ita daga gidan wancan mijin domin shi kuma ya aure ta, wannan ba daidai ba ne. Domin dalilai kamar haka

(i) Ana iya shiga haƙƙin wancan mijin da aka ɗaura mata auren da shi, haka ma haƙƙin yayanta idan Allaah ya sa suna da su. Rabuwarsu a irin wannan halin kuwa cutarwa ce gare su.

(ii) Soyayyar da ake samu kafin aure ba lallai ta zama irinta za a samu a cikin gidan auren ba. Don haka babu tabbacin ko da ta fito ya aure ta cewa, za su samu jin daɗin zamantakewa a tsakaninsu.

Daga ƙarshe: Abin da ya kamata dai kawai shi ne: Ya cigaba da adduar Allaah ya daidaita tsakanin shi da matarsa ta gida, ya sanya albarka da fahimtar juna a tsakaninsu. Amma kar ya kuskura tunanin waccan tsohuwar budurwar ya dame shi, har ma wataƙila ya kai shi ga taimaka mata don ta rabu da mijinta. Domin idan ya sanya hanunsa ko bakinsa ko shawararsa a cikin hakan, to ya aikata mummunan haram. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« مَنْ خَبَّبَ خَادِماً عَلَى أَهْلِهَا فَلَيْسَ مِنَّا، وَمَنْ أَفْسَدَ امْرَأَةً عَلَى زَوْجِهَا فَلَيْسَ هُوَ مِنَّا »

Duk wanda ya lalata wata baiwa a kan masu ita ba ya tare da mu. Haka wanda ya lalata wata mace a kan mijinta shi ma ba ya tare da mu. (Ahmad ya riwaito shi. Kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi a cikin As-Saheehah: 324-325).

Amma idan ta su ta haɗa su a tsakaninta da mijin, kuma ya sake ta don zaɓin ransa, ba tare da sanya hannu ko bakinsa a ciki ba, to a nan yana iya neman aurenta, a bayan ta gama idda.

Allaah ya ƙara mana shiriya.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments