Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Shafa Ƙirji Da Fuska A Lokacin Salati

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Malam Nakan ga waɗansu musulmi a lokacin da aka ambaci sunan Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) idan suka yi masa salati, sai kuma su ƙara da shafa fuska da shafa ƙirji. Wai mene ne matsayin wannan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul Laah

Asali dai addinin musulunci addini ne da ya ginu a kan sallamawa da miƙa wuya gaba-ɗaya ga Allaah Ubangijin Halittu a cikin komai na rayuwar mutum. Don haka musulmi na-gaskiya shi ne wanda ba ya yin duk wani abin da yake da alaƙa da ibada sai yadda Allaah Maɗaukakin Sarki ya nuna masa a kan harshen Manzonsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), kamar kuma yadda magabatan al’ummar nan mai albarka suka fahimta kuma suka yi aiki da shi, gwargwadon iyawarsa.

Sannan ayyukan addini malamai sun kasa su gida biyu ne: Akwai ayyukan ibada tsantsa waɗanda ba a bai wa musulmi daman yin komai a cikinsu da ra’ayi ko ganin dama ba, sai dai yadda shari’a ta fayya ce kawai.

Akwai kuma ayyukan al’ada waɗanda aka yarda musulmi ya yi abin da yake so a ciki, matuƙar bai ci karo da wani hani na sharia ba.

Shi kuma babin salati da sallama ga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a addini yana ƙarƙashin bauta (ibada) ne kamar sallah da zikiri, waɗanda ba a yin su sai yadda shari’a ta nuna kawai. Ba a cikin babin al’ada ne ya ke, kamar cin abinci da sanya tufafi ba.

Shiyasa a nan dole ne kafin a fara wannan aikin na shafar goshi da ƙirji a lokacin yin salati, sai an saurara tukuna, an binciki yadda sharia ta koyar da yadda ake yin salatin a gare shi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). A binciki nassoshi daga cikin hadisai sahihai, da ayyukan Sahabbai da Tabiai a gani ko akwai irin wannan abin a cikinsu? Idan an samu hakan daga ayyukan magabata shikenan, sai a ɗauke shi a cigaba da yin aiki da shi a matsayin wani ladabi a lokacin salatin. Idan kuma ba a samu ba, to sai a koma ga ƙaidar da malamai suka shimfiɗa a kan yadda ake gane bidi’a

Daga cikin hanyoyin da ake gane cewa abu bidi’a ce akwai cewa: Ya zama akwai yiwuwar a aikata aiki a zamanin farkon wannan al’ummar, amma kuma sai ba a ga sun aikata shi ba. Don haka idan aka aikata shi a bayansu to ya zama bidi’a, rashin aikatawar kuma ya zama Sunnah kenan. Misali: Kiran sallah domin sallar Idi da Jana’iza. Ko kuma ɗaga murya da zikiri a lokacin raka gawa. In da Sunnah ne da an yi su a zamanin farko, irin yadda aka yi a wadansu wuraren da shari’ar ta yarda. Don haka in da wani zai yi kiran sallah ko zikirin a lokacin raka gawa a yau, to da kuwa ya aikata bidi’a, bai yi Sunnah ba.

A iyakan bincikenmu da tambayarmu a wurin malamai, ba mu ga inda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya aikata irin wannan isharar ko shafar goshi da ƙirji a lokacin yin salati gare shi ba. Haka kuma ba mu ga aikata hakan daga Sahabbansa ko ɗalibansu da mabiyansu da kyautatawa ba. Abin da suka aikata kuma suka karantar da na-bayansu kawai shi ne yin salatin a gare shi kaɗai, a duk lokacin da aka ambaci sunansa, illa iyaka!

Kasantuwar kiristoci suna nuna alamar gicciye (cross) da hannuwansu a kan goshi da ƙirji a lokacin ambaton sunan Yesu (Annabi Isaa (Alaihis Salaam)), wannan bai bai wa musulmi daman su ƙirƙiro irin wannan isharar su ma a cikin addinisu ba. Domin abu ne sananne cewa addininsu daban, addinin musulunci kuma daban. Bai halatta musulmi su ƙirƙiri kiɗa da waƙa da rawa ko rangaji a cikin masallaci ba, domin su ƙalubalanci abin da kiristoci suke yi a cikin coci. Kamar yadda bai halatta Ahlus-Sunnah su ƙirƙiri murna da farin ciki a ranar Ashura ba, domin ƙalubalantar abin da Shia suke yi na nuna baƙin ciki a ranar. Ba a gyara bidia da bidia. Sunnah ce ake amfani da ita domin ta kawar da bidia.

A irin wannan wurin ne ake jawo maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« مَنْ أَحْدَثَ فِى أَمْرِنَا هَذَا مَا لَيْسَ فِيهِ فَهُوَ رَدٌّ »

Duk wanda ya ƙirƙiri wani abin da ba ya cikin alamarin nan namu, to shi abin mayarwa ne. (Sahih Al-Bukhaariy: 2697, Sahih Muslim: 4589).

A wata riwaya kuma ya ce

« مَنْ عَمِلَ عَمَلاً لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ »

Wanda ya aikata wani aikin da babu umurninmu a kansa, to shi abin mayarwa ne. (Sahih Muslim: 4590).

Wato ko aikatawa mutum ya yi, ba shi ya ƙirƙiro ba, ba za a karɓa masa aikin ba. Domin ya zama irin aikin ’yan Wuta, saboda maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« وَكُلَّ مُحْدَثَةٍ بِدْعَةٌ، وَكُلَّ بِدْعَةٍ ضَلاَلَةٌ، وَكُلَّ ضَلاَلَةٍ فِى النَّارِ »

Kuma kowace ƙirƙira bidia ce, kuma kowace bidia ɓata ce, kuma kowace ɓata tana cikin Wuta. (Sahih An-Nasaa’iy: 1578, Sahih Ibn Maajah: 45)

Allaah ya ƙara mana shiriya da ƙarin tabbata a kan bin Sunnah, ya kare mu daga afkawa a cikin komar sheɗanun mutane da aljanu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments