Ticker

6/recent/ticker-posts

Gurbin Da Sarauta Ta Mamaye A Cikin Fitattun Tatsuniyoyin Hausawa

Takarda da aka gabatar a taron ƙara wa juna ilimi na Ɗalibai masu karatun Digiri na Uku (PhD) a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, Satumba, 2023

Fayyace Gurbin Da Sarauta Ta Mamaye A Cikin Fitattun Tatsuniyoyin Hausawa

Haruna Umar Maikwari

Tsakure

Tatsuniya hanya ce ta koyar da rayuwa ta yau da kullum. Kuma ita wani sashe ne daga sassan adabi. Sarauta kuma tsarin mulki ne na gargajiya da aka sani tun kaka da kakanni. Wannan jinga, tana da manufofi da suka hada da: Bayyana sarautu da ayyukansu a cikin tatsuniyoyin Hausawa. Fito da ayyukan fadawa da zaman fada duk a cikin tatsuniyoyin Hausawa. Fayyace neman auren ‘ya’yan sarakuna da yadda ake ganinsu a tatsuniyoyin Hausawa. Hanyar da aka bi don gudanar da wannan bincike ita ce ta karance-karancen littattafan matanoni na tatsuniyoyin Hausawa, da wasu littafai da suka taimaka wajen samun makamar aiki da wasu mujallu da aka buga na ilmi daban-daban da sauraron tatsuniyoyi daga wasu mutane. An zaɓi a ɗora wannan bincike a  (Literary theory wanda wasu suke ce ma cultural theory). Shi dai wannan ra’in wani Baturen Jamus ne kuma masanin ilmin Falsafa (Philosophy) mai suna Friedrich Wilhelm Nietzsche wanda ya yi rayuwarsa a tsakanin shekarun (1844 – 1900) ya samar da shi.. Sakamakon wannan binciken kuma ya fito da ayyukan sarakunan dauri da fadawansu a cikin tasuniya da kuma neman auren ‘ya’yan sarakuna.  

1.0 Gabatarwa

Al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa. Al’ada ita ce mutum, duk mutumin da ya rasa al’ada, to ra yi hasarar abu mai muhimmanci na gudanar da rayuwa. Shi kuwa adabi, shi ne hoton rayuwar al’umma. Idan al’ada ita ce rayuwa ta zahiri, adabi shi ne hoton rayuwar zahiri. Kenan za a iya cewa al’ada ita ce mutum, shi kuma adabi shi ne inuwarsa. Duk inda ka ga mutum ba za ka rasa ganin inuwarsa ba. Sai ko wani dalili na daban. Ita kuma tatsuniya wani reshe ne daga rassan adabi wanda ake samun cikin zube. Ita dai tatsuniya, ita ce hanyar da mutanen dauri suke amfani da ita wajen koyar da ‘ya’yansu tsarin tafiyar da rayuwa kama daga zamantakewa, jarunta, aure haihuwa mutuwa, buki, soyayya, hani da horo, tsarin mulki, hukunce-hukunce, shari’a da makamantan su. Sarauta tsari ne na shugabanci da ake gudanarwa tun lokaci mai tsawo. Wannan tsari shi ne wanda aka sani tun kaka da kakanni. Sarki dai shi ne shugaba. Akwai waziri da sarkin fada da shamaki da sallama da majikira da sarkin yaƙi da dai sauran sarautu da suke kewaye da sarki. Kowane mai riƙe da sarauta yana da irin rawar da yake takawa daidai matsayinsa.

1.2 Manufar bincike (Jinga)

Manufa dai ita ce jigo ko abin da mai rubutu ya ƙudurci bayyanawa ko saƙo da mai rubutu ko magana ya ke son ya isar ta hanyar da yake son ya isar. Wannan jinga tana da manufofi da suka haɗa da:

a.       Bayyana sarautu da ayyukansu a cikin tatsuniyoyin Hausawa.

b.      Fito da ayyukan fadawa da zaman fada duk a cikin tatsuniyoyin Hausawa.

c.       Fayyace neman auren ‘ya’yan sarakuna da yadda ake ganinsu a tatsuniyoyin Hausawa.

1.3 Ra’in Bincike (Jinga)

An zaɓi a ɗora wannan bincike a kan ra’in (Literary theory wanda wasu suke ce ma cultural theory). Shi dai wannan ra’in wani Baturen Jamus ne kuma masanin ilmin Falsafa (Philosophy) mai suna Friedrich Wilhelm Nietzsche wanda ya yi rayuwarsa a tsakanin shekarun (1844 – 1900) ya samar da shi. Wannan masani an haife shi a ranar 15 ga watan Oktoba a 1844. Shi ɗa ne ga Karl Ludwig da Franziska Nietzsche. Mahaifinsa ya mutu tun yana ɗan shekara biyar, kuma ya mutu ya bar shi da ƙaunarsa mai suna Elisabeth da wani ƙane ƙarami mai suna Friedrich, wanda shi ma bai jima ba ya mutu ba zato ba tsammani. Haka kuma shi Nietzsche ya kasance yana amfani da kayan kiɗa na Fiyano yana rera waƙa musamman waƙar Emerson da Friedrich da ta Holderlin.

A shekarar 1864, Nietzsche  ya shiga jami’ar Bonn. A 1865 kuma ya kasance mabiyin Farfesa Friedrich Ritschl. Nietzsche ya samar da wannan ra’i tare da taimakon wasu ‘yan ajinsu (Classmates) waɗanda suka haɗa da Paul Deussen, (wanda ya kasance cikin sanannun masanan tsohon harshen nan na Sanskrit da Indic). Nietzsche ya samu zama Farfesa a fannin ilmin harshen Girkanci da adabi a Jami’ar Basel ta Switzerland.

 Shi wannan ra’i ya kasance yana mayar da hankali kan dalilin da ya sa a aka yi rubutu da kuma marubuci tare da al’adar marubuci domin yanke hukunci game da abin da aka rubuta. Masu bin wannan ra’i suna da ra’ayin cewa, ana gane haƙiƙanin ma’anar rubutu ne ba ta hanyar duba gundarin rubutu ba, sai dai ta hanyar fahimtar al’adun mai rubutun, da dalilin rubutun da kuma tarihin rubutun gaba ɗaya.

Wannan ra’in yana da dangantaka da aikin da za a gudanar, musamman idan aka lura da cewa wannan aikin ana ƙoƙarin a fitar da al’adu a cikin rubutacciyar waƙa ne. A wannan aiki ana ƙoƙarin fito da al’adu a cikin wasu zaɓaɓɓun rubutattun waƙoƙi ne, yayin da wannan ra’in shi kuma yana goyon bayan cewa, nazartar al’adar marubuci dole ne kafin a gane haƙiƙanin manufar rubutu. Lura da wannan, za a ga cewa ra’in yana jaddada ra’ayin cewa akwai makusanciyar dangantaka tsakanin abin da aka rubuta da kuma al’adar marubuci. Wannan ya nuna al’ada na da tasiri kan rubutun marubuci, kuma rubutu na da tasiri kan al’ada.

An samu wasu waɗanda suka assasa wannan ra’in da suka haɗa da:

a.       Terry Eagleton 1983, 1996 FOR Charles Swann And Raymond Williams: Literary Theory- An Introduction Second Edition.

b.      Vince Brewton: Literary Theory

c.       Andrew Bennett and Nicholas Royle: Introduction to Literature, Criticism and Theory. Third Edition.

1.4 Hanyar Gudanar da bincike (Jinga)

Wannan jinga za ta yi amfani da hanyar sauraron wasu tatsuniyoyi daga wasu mutane tare da fito da abin da ake nema a ciki. Haka kuma za a yi amfani da karance-karancen littattafan matanino na tatsuniyoyin Hausa da suka haɗa da Jagoran Nazarin Tatsuniya na Hadiza Salihu Koko da Tatsuniya a rubuce na Sa’idu Muhammad Gusau da Kunne ya Girmi Kaka da Taskar Al’ada da Tarihi da Nishaɗi na Salisu Ahmed Yakasai da Tatsuniyoyin Hausawa na Bukar Usman da dai sauransu. Akwai kuma littattafai da suka taimaka wajen gudanar da wannan bincike da mujallu da dai sauran abubuwan karantawa kamar kundaye da makamantansu.

 

1.5 Ma’anar Tatsuniya

Yahaya (1971) yana cewa “Tatsuniya ko gatana, wani ƙagaggen labari ne wanda al’adu da tunanin al’umma suka ƙirƙiro daidai da tunanin ‘ya’yansu (yara) domin tarbiyantar da su, cikin nishaɗi da kuma halayyar da ta dace da irin tarbiyyar”. Abin nufi a nan shi ne ita dai tatsuniya ta tafi kan daidai da yadda al’umma ke kallon rayuwa gaba ɗaya. Sannan kuma tunanin da ake cikinta da halayyar da aka ganta da ita, kai hatta da salon da ake yin amfani da shi domin isar da saƙon da take ɗauke da shi, duk masu dacewa ne da tunani na duniyar yara.

Umar, (1987), ya bayyana cewa, “Tatsuniya ƙagaggen labari ne da magabata kan shirya musamman don tarbiyya bisa ga tsarin gargajiya”. Muhammad, ya ƙara da cewa “romon kai ce ko ba da labarin wani bai ɗaya, da bai faru ba a zahirin haka nan kuma a wannan labarin yana da tsohon tarihi saboda kaka da kakanni suka ƙirƙira shi suka sadar da shi zuwa gare mu a tsawon lokaci. Wani abu muhimmi da ma’anar ta zo da shi, shi ne ƙagaggen labari na kaka da kakanni. Sun ƙirƙira shi ne a matsayin wata hanya ta cusa wa ‘ya’yansu tarbiyya domin su ta shi a matsayin Hausawa masu tunani da ɗabi’u da halaye masu bin al’adun waɗanda al’ummar ƙasar Hausawa ta yarda da su.

A CNHN (2006) kuwa an bayyana cewa “tatsuniya labari ne da ake ba wa yara na hikima na hikima don hira.”

Bisa ga ma’anonin da aka tattara za a iya cewa “tatsuniya ƙagaggen labari ne da Bahaushe ya tsara domin ya tarbiyantar da ‘ya’ya a kan lamurran duniya da kuma al’adunsu.

1.6 Sarauta a Ƙasar Hausa

Babu shakka ƙasar Hausa kamar sauran ƙasashe na duniya akwai tsarin mulki. Wannan tsari na sarauta tun asali shi aka sani. Shugabanci ne da aka fara sani a ƙasar Hausa. Ita sarauta kamar yadda Alhassan, (1985:74) ya bayyana cewa “sarauta ita ce wata dama ko sarari ko iko ko mulki ko jagoranci da wani ko wasu ke da shi a kan wasu mutane musamman abin da ya shafi bayar da umarni bisa kyakkyawa ko kuma hani bisa aikata mummuna.” Shi kuma Zarruƙ, da wasu (1988), sun bayyana cewa” sarauta ita ce a yi wa mutane jagoranci ko jan ragama.”

Shi kuwa Yahaya, (1992), yana ganin “sarauta ita ce mulki ko iko, wato ɗaukar nauyin jagorancin a’umma, wanda ya haɗa da yi masu shugabanci ta hanyar tsara hanyoyin kiyayewa da lafiyarsu da ta dukiyarsu da ma shirya masu ƙa’idojin zaman tare ta fuskar shari’a da gudanar da hulɗar ƙasarsu da ƙasashen maƙwabta da ƙasashen waje.

Shi kuma Gulbi (2000) yana ganin sarauta ita ce sababbiyar hanyar da Hausawa da ma waɗanda ba Hausawa ba suka gada tun kaka da kakanni ta amfani da wakiltar wani mutum daga cikinsu domin ya jagorance su tare da ƙoƙarin ƙwato haƙƙin wani idan buƙatar hakan ta taso.  

Sarauta tsarin mulki ne na gargajiya da aka san al’umma da shi tun farko. Wannan tsarin mulki wani daga al’ummar ke shugabanta. Kuma galibi yana da mataimaka da su ke taya shi gudabar da sarautar. Daga cikin mataimakan akwai; waziri, sarkin fada, jakada, maji kira, shantali, shamaki, sarkin yaƙi, dogari, da dai sauransu. Kowace sarauta na da tsarin yadda ake tafiyar da ita. Kowane daga cikin masu riƙe da sarautar yana da aikin da yake yi wato yana da rawar da yake takawa daidai da matsayinsa.

1.7 Sarautu a cikin Tatsuniyoyin Hausa

Babu shakka sha’anin sarauta al’ada ce da ta cuɗanyi al’umma. Duk da cewa a yau akwai tsarin mulkin siyasa wannan bai hana a samu masu sarauta ba. Hasali ma kusan dukkan shugabannin da ake yi na siyasa, sai da sa hannun masu riƙe da sarautu. A wasu yankunan ma masarauta ke bayar da ɗan takara.

Wannan tsari na sarauta ya yi tasiri har a cikin adabinmu na gargajiya. Ana ganin sarauta a dukkan sassan adabin kowace al’umma.[1] A al’ummar Hausa kuwa, kusan dukkan al’adunsu na bayyana a cikin adabin su. Wannan tsari na al’ada, wato sarauta ana ganinsa a cikin tatsuniyoyin Hausawa kamar dai yadda za mu gani.

1.8 Bayyanar Sarauta da Aikin Sarki a Cikin Tatsuniyoyi

Tatsuniyoyin Hausawa cike suke fal da tsarin sarautunsu. A zamanin dauri sarakuna su ke tafiyar da mulki kuma komai yana ƙarƙashin kulawarsu. Wannan ya sa kusan tatsuniyoyin da ake yi a dauri duk suna ɗauke da hotunan sarautu a cikinsu. Akwai tatsuniyoyi irin su; tatsuniyar Yara da Kada, Ɗan Naturke, Daskin Dariɗi, Jarumin Sarki, Sarauniya, Ɗan Agwai da Kura, Marainiya da sauransu.

1.8.1 Adalcin Sarakuna

A tatsuniyar Yara da Kada an nuna cewa wasu yara suka je rafi wajen wanka kuma ga shi a wannan rafin akwai kada mai haɗiye mutane. Da zuwan su sai kadan ya fito ya fara da rabon su da waƙa yana cewa:

 Maraba-maraba da yara,

 Yara sun zaka wanka,

In ci kwai-kwai, in ci kwai-kwai.

 

Sai kada ya haɗiye su.

 

Bayan an jima ba a ga yara ba sai Innarsu ta ce wa yannan yaran nan su je su dubo yaran nan a rafi wajen wanka da suka je ba su dawo ba. Da suka je sai su ma kadan ya fito ya tare su da waƙar kamar haka:

 

Maraba-maraba da yannai,

Yannai sun biyo ƙannani,

Ƙannai sun zaka wanka,

In ci kwai-kwai, in ci kwai-kwai.

 

Sai kada ta haɗiye yannan yara.

 

Su ma yannan da aka ga ba su dawo, sai Innar su ta biya. Ita ma kadar ta fito ta tarbe ta da waƙa ta haɗiye. Baban ya je ya bi Innar shi ma kadar ta haɗiye shi sai sarkin garin ya tura fadawa, da suka je sai kadar ta haɗiye su. Daga ƙarshe dai sai sarkin ya je da kansa don ya ceto su. Da kadar ta fito sai ta fara waƙar:

 

Maraba-maraba da Sarki,

Sarki ya biyo fada,

Faada ya biyo baaba,

Baaba ya biyo Inna,

Inna ta biyo yannai,

Yannai sun biyo ƙannai,

Ƙannai sun zaka wanka,

In ci kwai-kwai, in ci kwai-kwai.

 

Sai sarki ya fito da sandarsa ya kwaɗa wa kadar. Da ta ƙara sai ta ce na tuba ka yimin rai, sarki ya ce to fito da mutane na. Ta amayo fadawa, ya ƙara kwaɗa mata sai ta amayo baban yaran, ya ƙara kwaɗa mata, ta amayo Innar yaran, ya ƙara kwaɗa mata, ta amayo yannan yara, sai ya ƙara kwada mata ta amayo yaran da ta haɗe da farko.

Wannan tatsuniya ta fito da hoton adalcin sarakuna. Domin kuwa a madadin sarki ya kasance yana mai zaluntar al’ummarsa, sai ga shi da kansa ya tafi wajen taimakon talakawansa.

A wata tatsuniyar kuma, an samu sarki ya yi adalci wajen yanke hukunci a kan wanda ya kashe ɗan uwansa shi ma aka kashe shi. Misali:

Sai sarki ya ce to, a kira yaron wato yayan wanda aka kashe, ya zo aka ba shi ƙashin ƙanensa, da ya fara busawa sai ƙashin ya ce:

“...Kai yayana, kai yayana,

Ƙashi na  ne kake hurawa,

Baba ya aike mu a daji,

Mu samo huranni,

Wana sun fi naka kyau,

Sai ka ɗauke nawan ka kashe ni.

Sai sarki ya ce to a akama yaron shi ma a kashe shi. Aka kama shi aka kashe. Shike nan an yi maganin wanda ya ci amana.

1.8.2 Jaruntar Sarakuna

Daga cikin abin da ke sa a gane sarki ya cancanta a dauri akwai jarunta. Idan sarki na da jarunta, yanada da duk abin da ake so a wancan lokaci. Bukar Usman ya zo da wata tatsuniya mai suna Jarumin Sarki. Wannan tatsuniya ta fito da jaruntar sarakuna inda suke fita yaƙe-yaƙe domin faɗaɗa ƙasarsu. Wannan jarumin sarkin ya fita fagen daga inda yake ta famar kashe abokan gaba.

“.......wannan sarki ya shahara wajen yaƙe-yaƙe. Domin kuwa da ya fita fagen daga sai kashe abokan gaba yake yi......”

 (Tatsuniyar Jarumin Sarki na Bukar Usman)

 

Jarunta ke sa a yi sarauta a lokacin dauri. Haka kuma yin yaƙi wani abin bugun gaba ne ga duk wanda ya yi nasara a kansa.

1.8.3 Zaluncin Sarakuna

A wancan lokaci duk wani abu mai kyau a gidan sarki ake kai shi kama daga mata, dabbobi, hatsi, wata dukiya da makamantan su. Wannan zalunci ya bayyana a tatsuniyoyin Hausawa kamar: Tatsuniyar ‘Yar Amana, Ɗan Naturke da makamantan su.

1.8.3.1 Zaluncin Sarakuna a Cikin Tatsuniyar Ɗan Naturke

A wannan tatsuniya an bayyana cewa akwai wata tsohuwa wadda ta turke wani bajinin sa (Maraƙi) ya girma har ya kai maƙura. Ga misalin abin da ya bayyana a wannan tatsuniya:

“.....A lokacin da almajiri ya je bara gidan wannan tsuhowa, sai ta kira shi ta ba shi abinci. Da ya shiga sai ya ga wannan babban sa a turke. Yana fita sai ya nufi gidan sarki. Da shigar sa sai ya ce “sarki-sarki yanke min kunne na”. Sai sarki ya ce, “idan na yanke maka kunne da me za ka jiyo mini labari?” sai ya ce, “Na ga wani sa a gidan wata tsuhuwa wanda bai dace da kowane gida ba sai da gidanka.” Nan take sarki ya ce a je a zo masa da wannan sa.

 

Da suka zo ɗaukar san sai suka fara kwance shi, ashe san baya kwantuwa.

Sai aka bugi tsohuwar aka sauɗa mata bulala ta ce:

Kwantu-kwantu Naturke,

Ban so rabuwa da kai ba,

Sarakan bana kwaɗai gare su,

Abu kaɗan su kai ka fada,

Can fada, can fada garkar sarki.”

(Tatsuniyar Ɗan Naturke)

Wannan tatsuniya ta fito da zalunci sarakuna a fili. Da yake a wancan lokaci sarakuna suna ƙarfi da ikon karɓe duk abin da yake ga talaka kamar yadda ya bayyana a tatsuniya.

1.8.3.2 Zaluncin sarakuna a Tatsuniyar Azzalumin Sarki

Ko shakka babu da jin sunan tatsuniyar cewa “Azzalumin Sarki”. Akwai zalunci a ciki. A wancan lokaci sarakuna sukan yi zalunci ga talakawansu. Babu mamaki idan shugaba ya zalunci talakansa, domin kuwa ko a wannan zamani zalunci ya zama ruwan dare ga shugabanninmu. A wannan tatsuniya an bayyana cewa akwai wani sarki azzalumi da yake aikawa a kamo masa baƙi ya ƙwace duk abin da suka samu su kuma ya kai su ga zaki da ke ɗaure su canye. Ga dai yadda abin yake:

.... a wani zamani an yi wani azzalumin sarki da yake sa fadawa su tare masa baƙi ya amshe masu dukiya su kuma ya kai su ga zaki da ke ɗaure sai zakin ya canye mutanen daga nan dukiya ta zama tasa. Wata rana sai fatake suka biyo ta wannan garin sai sarki ya sa aka kama su, ya ƙwace dukiyarsu, ya kai ya aje da nufin su kuma idan safiya ta waye sai ya kai su ga zaki. Ashe a cikin jikkuna fataken nan akwai biri, sai birin da ke ciki ya kwance jikka ya fita ya nufi inda zaki yake sai ya kwance zaki. Zaki ya fita ya afka fada ya cinye sarki. Su kuma fatake suka kama birinsu, suka ɗauki kayan su daga nan sai aka kawo ƙarshen zalunci wannan sarki.

Wannan tatsuniya kai tsaye kamar yadda na faɗa tana nuna zalunci sarki ne. Akwai tatsuniyoyi ire-iren waɗannan da ke bayyana zaluncin sarakuna.

1.8.3.3 Zalunci Fadawa.

Bafade shi ne wanda yake zaune a majalisar fadar sarki a kodayaushe ana zaman fada da shi. Su dai fadawa suna da sarki wanda ake kira da sarkin fada.[2] Fadawa sun bayyana a cikin wasu tatsuniyoyin Hausawa. Galibi halayen Bafade da aka sani su ne yin sharri da nisanta wani ga sarki a wancan zamani. Idan aka ce ma mutum Bafade an siffanta shi da wata halayya marar kyau kenan. Fadawa sun bayyana a cikin tatsuniyoyin Hausa kamar: Tatsuniyar Mugun Bafade.

1.8.3.3.1 Zaluncin Bafade a Tatsuniyar Mugun Bafade

Da jin sunan wannan tatsuniya, ya bayyana mina zaluncin ne wani Bafade ya yi. Kamar yadda aka sani akwai fadawan da suke ba wa sarki shawara musamman idan suka ga cewa za su ribatu da wani abu.  Duba misali a wannan tatsuniyar:

... A wani gari wai shi Katano, an yi wani sarki da wazirinsa. Wannan waziri Bafillace ne kuma maƙetaci. A kusa da fadar sarki akwai wani gina na wani attajiri. A bayan gidan attajirin akwai wata ƙatuwar itaciyar kuka wadda ke da kogo. Akwai tururruwa, maciji, shamuwa da shaho da aljani. Kullum safe sai attajirin nan ya je sun gaisa da wadannan abubuwa kuma ya ba su abinci.

Waɗannan ƙwari sun nemi wannan attajiri da su riƙa yi masa bauta ya ce “a’a”. Ana nan, ana nan sai wazirin sarkin nan ya kai suka attajirin nan ga sarki kuma ya riƙa ƙulla masa makirci kala-kala. Ran nan sai waziri ya ce wa sarki ya kamata a nuna wa attajirin nan ba kowa ba ne. Sai sarki ya amnita. Aka haɗe buhuwan gero da dawa da masara da wake aka kira shi ya rarrabe su. Mutumin nan ya ɗauka zuwa rarrabewa sai tururruwa ta gani ta ce ya bari ta yi wannan aiki. Ta kira sauran danginta suka zo suka rarrabe kafin safe sun gama. Da aka kai sai kuma wazirin bafaden nan ya ce a ce masa ya nemo tumu, kuma ga shi ga rani ne. Sai shamuwa ta je wani yanki inda ke da damana ta samo tumu. Da ya ga bai yi nasara ba, sai ya ce a ɓoye zoben sarki aka kira shi aka ce zoben sarki ya ɓata ya je ya nemo shi. Sai aljani ya nemo ya kawo. Ana haka sai maciji ya ce shi zai sari ‘yar sarki, idan aka ce meye magani sai ya ce a kawo antar Waziri Bafillace......”[3]

1.8.4 Neman Auren ‘Ya’yan Sarakuna

‘Ya’yan sarakuna kamar sauran al’umma, sukan nemi aure. Galibi sukan auri wasu ‘ya’yan sarakuna ko daga cikin talakawansu. Ana samun ‘ya’yan sarki su nemi wanda yake talaka ko mummuna ce. Amma kuma galibi idan suka nema daga baya abin kan zamo alheri gare su. Wasu sukan yi aure ta hanyar gasa, wasu kuma sukan yi ta hanyar bin maganar iyaye ko ta hanyar haƙuri da dai makamantansu. Tatsuniyoyin gasar auren ɗiyan sarakuna misalinta shi ne tatsuniyar “Daskindariɗi.” Ita wannan tatsuniya ta zo da gasar sai an faɗi sunan ɗan sarkin, kafin ya aminta da wadda za shi aura.

A wannan tatsuniya an bayyana cewa wannan ɗan sarki ya ce shi zai zaɓi matar da zai aura da kansa. Don haka sarkin ya ba shi damar haka, ya kuma ba shi dukiya. Ɗan sarkin nan ya bar garinsu ya nufi wani gari kuma ya sauka a gidan wata tsohuwa. Ya gaya wa tsohuwar nan abin da ke tafe da shi. Da tsohuwa ta ji haka sai ta shiga gari wajen cigiyar mata. A daidai wannan lokaci akwai wasu mata da suke a gida guda. A wannan gidan akwai Dawa, Gero Maiwa Shinkafa da Burtuntuna. A cikin waɗanan ‘yan matan Burtuntuna ce ba ta da gata, saboda ba ta da uwa a gidan.

Muhallid shahid dai ita ma ta samu zuwa gasar da aka shirya duk wanda ya zo sai ya shiga daga ciki ya yi waƙa kamar haka:

Dawa:  Ahuwanka dai ɗan yaro,

 Ahuwanka dai,

Ɗan sarki:  Wace ce nan take mani, ahuwanka dai?

 

Dawa: Dawarka ce take maka ahuwanka dai,

          : Mai tuwo da daɗi,

          : Ni Dawa mai fura da daɗi.

Ɗan sarki: Na ji naki suna yarinya, ba ni nawa suna.

Dawa:  Ban san ka ba, ɗan yaro,

 Ban san ka ba.

Ɗan sarki:  Da ba ki san ni ba, yarinya,

 Koma da baya ki sha kuka.

 

Bayan da Dawa ta shiga ɗaki don gabatar da gasar, sai ta fito ba ta yi nasara ba don ba ta san sunansa ba. Sauran duk sun shiga abin da ya faru da dawa shi ya faru da su. Ana nan sai ga Burtutuna ta shigo sai suka fara tsegumi cewa wa ma ya ara mata kaya. Da ta shiga sai ta faɗi sunan. Ga dai yadda gasar ta kaya ita da shi ɗan sarkin:

Burtuntuna:  Ahuwanka dai ɗan yaro,

 Ahuwanka dai,

Ɗan sarki:  Wace ce nan take mani, ahuwanka dai?

 

Burtuntuna: Burtuntunarka ce take maka ahuwanka dai,

          : Mai ɓata tuwo,

          : Ai ni ce mai ɓata fura.

Ɗan sarki: Na ji naki suna yarinya, ba ni nawa suna.

Burtuntuna:  Daskin-da-Riɗi ɗan yaro,

Daskin-da-Riɗi

Ɗan sarki:  Buɗe ki shigo,

Yarinya buɗe ki shigo.

Wannan gasa dai ɗan sarki ne ya shirya ta don ya samun matar da zai aura. Sharaɗinsa na cin wannan gasar kuma shi ne wanda ya san sunansa. Ita ma wadda ta san wannan sunan ta sani ne ta hanyar taimakon da ta yi wa wata tsohuwa. Wannan tatsuniyar dai ba gasar ce jigonta ba amma kuma ita ce ta fi haska tatsuniyar.

 

Bayan ta fannin gasa kuma, akwai ta hanyar biyayya ga iyaye. Wato a wannan tsari. Idan muka duba abin da ya faru a tatsuniyar Gwaidayara. A wannan tatsuniya dai anbayyana cewa wani mutum ne yake da mata huɗu, kuma duk yana son su ban da ta huɗun. Sai suka samu ciki suka haihu aka samu yara mata har huɗu. ya raɗa wa ukun suna: ga dai misali daga abin da ya auku:

“...Da matan nan huɗu suka haihu sai ya raɗa wa ukun suna wato Halima da Jummai da A’isha. Ita kuma ‘yar matar ta huɗun bai raɗa mata suna ba. Da uwar yarinyar nan da ba a raɗa wa suna ba ta matsa da tambaya sai ya ce ta tafi sunan ɗiyarta Gwaidayara. Kuma haka aka ci gaba da kiranta. Da yaran nan suka kai munzalin aure, ya yi wa kowace aure, amma ban da Gwaidayara. Da mahaifiyar ta ga haka sai ta tambayi dalili. Inda mahaifin ya umarci yarinyar da ta riƙa binsa a jeji. Wata rana a cikin jejin sai suka ga wani baƙin maciji ya wuce, sai uban ya ce ta bi wannan maciji. Haka kuwa aka yi saboda ɗa’a da biyayya da yarinyar ta ke yi wa mahaifinta ta bi shi sau da ƙafa. Da ta bi macijin sai ya rikiɗa ya koma mutum saurayi kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa kuma ga shi ɗan sarki. Da ganin yanayin da Gwaidayara take ciki, sai ya yi alƙawarin zai aure ta. Haka ko aka yi.

Wata rana mahaifinta ya zo garin da take aure sai ya same ta cikin ni’ima da walwala a sanadiyyar ɗa’a da biyayya da ta yi wa mahaifinta. Da ya dawo gida sai ya sa aka kira dukkan ‘ya’yansa da mazansu aka tarar kowace na cikin halin talauci da ƙunci ita da maigidanta....”

Wannan aure da ɗan sarki ya yi na Gwaidayara, ya yi sa ne ba don komai ba sai don biyayyar da ita yarinyar ta yi wa mahaifinta. Haka dai al’adu suke bayyana cikin tatsuniyoyin Hausawa. Da ma dai adabi shi ne hoton rayuwar al’umma. Don haka ba abin mamaki ba ne idan aka ga wata rayuwa ta bayyana a cikin wani reshe na adabi.

1.9 Kammalawa

Tsarin mulkin Hausawa wani reshe ne daga cikin rassan al’adunsu. Su kuma al’adun suna bayyana ne a cikin dukkan sha’anonin rayuwa na Hausawa. Al’adun sun mamaye adabinsu kusan dukkan rassan adabin Hausawa suna ƙunshe da al’adunsu. Tatsuniya hanya ce ta koyar da tarbiyya tun a zamani dauri. Don haka al’adun da suka shafi sarauta sun ka bayyana a cikin tatsuniyoyin Hausawa. Wannan bincike ya gano cewa akwai sarautun Hausawa ƙunshe cikin tatsuniyoyinsu. Kama daga adalci shugabancinsu da akasinsa, da ayyukan fadawa da auren ‘ya’yan sarakuna. Binciken ya ratsa wasu tatsuniyoyi da suka haɗa da: Tatsuniyar yara da kogi, tatsuniyar jarumin sarki, tatsuniyar Gwaidayara, ‘Yar Amana, Azzalumin Sarki, Mugun Bafade, Daski-da-Riɗi da da makamantansu.

Manazarta.

Alhassan H. da Zarruq, R. (1985). Zaman Hausawa. Lagos: Academy Press Limited.

CNHN (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.

Gulbi, A. S. (2000) “Sarautar Gargajiya a Ƙasa Gummi Jiya da Yau”, Kundin Digiri na  Ɗaya. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

Ibrahim M. S. (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci a Kan Rayuwar  Hausawa ta Gargajiya.” Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.  Jami’ar Bayero Kano.

Umar M.B. (1987), Dangantakar adabi da al’adun Gargajiya. Triumph Publishing Company Kano.

Umar , M. B. (1982) “Dangantakar Adabi da Al’ada”. BA Dissertation BUK.

Vince, Brewton (ND). Literary Theory. Alabama: University of North. Ciratowa a shafin google  a  Ranar 5, ga Febrairu, 2019.  https://www.google.com/2017/11/

Yakasai, S. A. (2012) Taskar Al’ada da Tarihi da Nishaɗi

Yahaya, I.Y. da Wasu (1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. Littafi Na Ɗaya. Ibadan: University Press Plc.

Yahaya I.Y. (1971), Tatsuniya Da Wasannani 1-6, Ibadan Oɗford University Press.

Yahaya I.Y. (1992) Darussan Hausa Dom Manyan Makarantun Sakandare. University  Press Ibadan.

Zarruk R.M. da Wasu,(1988), Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don {ananan  Makarantun Sakandare, University Press Ibadan.



[1] Sanin al’umma ne cewa kowace al’umma tana da shugaba wanda ke shugabantar ta. Haka kuma suna da adabi wanda da shi ake gane wannan al’ummar.

[2] Akwai wasu mutane da suke zaune a majalisar sarki. Kuma su wadannan mutane su ke aiwatar da umarnin sarki. Wasu sukan ba sarki shawara ko kuma sarkin ya haɗa da su wajen aiwatar da wani abu mai kyau ko akasinsa.

[3] A duba Jagoran Nazarin Tatsuniya na Hadiza Salihu Koko wanda aka yi a shekarar (2009) a shafi na 61-62.

Post a Comment

0 Comments