Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sakin Mace Mai Juna Biyu (Ciki) Ko Mai Haila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam! Mutum ne ya saki Matarsa tana da juna biyu, To ya hukuncin wannan sakin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullah Wabarkatuh.

Mutumin da ya saki Matarsa tana da juna biyu Matsala biyu ce a taƙaice

1. Matsala ta Farko:- shin saki ya yuwu ko bai yuwuba? Alal haƙiƙa saki ya yuwu, kuma saki a lokacin da mace take da juna biyu; saki ne wanda ya halatta duk da cewa a cikin malaman fiƙihu akwai masu cewa saki da juna biyu bai halatta ba suna ƙirgashi a cikin Adɗalaƙul bida'i.  Amma a cikin nafsin ƙur'ani za a fahimci cewa ya halatta, wanda wannan shi ne fatawar sauran malaman.

Dalilin faɗin Allah maɗaukakin sarki: " Mata ma'abauta juna biyu iddarsu shi ne su haife a binda ke cikin cikinsu"

To kaga da sakin bai halitta ba; da Allah ba zai shagalta wajen faɗin yadda za su yi idda ba, yadda Ubangiji ya tsaya ya yi sharhin yadda za suyi idda, wannan dalilin ne a kan cewa sakin ya yuwu, wannan dalilin ne kan cewa sakin ya halatta, to dan haka duk wadda aka saka da juna biyu sakin ya halatta kuma ya yuwu ( ta saku ).

Yanzu abinda ya rage shi ne iddarta ba za ta fita daga ciki ba, har sai lokacin da ta haihu, ko yau aka saketa sai ta haihu gobe ko jibi, ka ga kwana biyu kenan to ta fita daga idda ya halatta tayi Aure.

2. Sannan abu na gaba:- wajibi ne ga miji ( wanda ya sake ta ) ya zamanto ciyar da ita, shayar da ita, tufar da ita, duk suna a wuyansa gidan da za ta zauna ya biya haya, in gidan iyayen ta ne ciyarwa da shayarwa duk suna a wuyansa har lokacin da za ta haihu, idan ta haihu kuma dole ne ya ciyar da ita dan ta shayar da ɗansa, sai dai in ya samu wata mai shayarwa su kai ittufaƙin yadda zai biya, ya karɓe ɗan ya kai mata, saboda a shari'ance a kwai wannan, amma in ba haka ba shi zai riƙa ciyar da ita saboda shayar da ɗansa."

WALLAHU A'ALAM

✍️ Abu Rukayya Falale

HUKUNCIN SAKIN MACE MAI CIKI DA MAI HAILA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum warahamatullah malam barkammu da dare ya aiki Dan Allah inada tambaya guda biyu:

1. Aka ce idan aka saki mace tanada ciki wai sakin Bai yiwu ba hakama idan aka saketa tana jinin Al'ada shi ma sakin Bai yiba na gode Allah y karawa malam lpy?

2. Idan namiji Yasaki macce da kwana biyar sai yarasu Kuma saki ukku to tana da takaba akanta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa AlaikisSalaam Wa Rahmatullah:-

1. Toh Idan an sake Mace tana da Ciki, toh Sakin ya Tabbata Ma'ana Sakin ya yi Wannan shi ne Fatawar Malaman Fiƙhu da Manyan Malaman Hadisai.

Kuma iddar ta zai Zama shi ne Haihuwar ta, Misalin an sake ki a Yau da Safe Anjima ko gobe da safe sai Kika Haihu, toh Shi ke nan har kin fita daga Iddar ki idan kin so ko kafin Nan da sati za ki iya Ɗaura Auren ki da wani idan kin so Kuma sai kin yaye Yaran ki. Amma dai kin Gama iddar ki Ma'ana kin fita daga Matar wancan Mijin da ya Sake ki.

2. Matar da Aka Sake ta, Saki ɗaya ko Biyu sai Kafin ta gama Idda Mijinta ya Mutu, toh za ta yi Masa Takaba Kuma za ta Ci Gadon sa.

Idan kuma ya Zama Saki daidai har guda Ukku ne, sai Kafin ta gama Idda sai ya Mutu, toh za ta ci gaba da iddar ta ne bawai Takaba ba, kuma ba ta Ci Gadon sa ba.

3. Malamai Sun Yi Sabani akan wannan Matsalar, Idan an Sake Mace tana cikin Jinin Haila, Wannan Kuma ba ta Saku ba, an Yi Sakin Bidi'a, Domin Zamanin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasalam akwai wani Lokacin da Abdullahi Ɗan Umar Allah ya Kara Yarda gare shi, wata Rana ya sake Matar sa tana Cikin Jinin Haila sai ya Zo ya samu Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce shi ya sake Matar sa tana Jinin Haila sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Masa ya dawo da ita domin Babu Sakin Mace ga Wadda take Jinin Haila har sai tayi Tsarki kafin a Sake ta wannan shi ne Shari'a ya ce ayi.

Toh anan sai wasu Malaman Suka Ce tun da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce ya dawo da ita ke nan Sakin Bai Yi ba, Wasu kuma Suka Ce Sakin ya yi Misalin idan ya taɓa Yi Mata Saki 1 a baya Can, toh yanzu ga 1 ya Zama 2 ke nan saura Masa Igiya 1. Wasu Kuma Suka ce A'a Kawai Sakin Bai yiyu ba tun da Dai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Bai Yi ba to Babu Sakin.

Sabida Haka Duk Wadda aka ɗauka Ya yi, idan an ɗauki Sakin Ya yiyu, toh akwai hujjar Malamai Cewa duk Wadda ya sake Matar sa, Ko da Wasa yake Yi ta saku domin ba a Wasa da Saki, Kuma abun da ya yi Niyyar sa a Zuciyar Sa shi ne ya fitar ya ce ya sake Ta shiyasa Suka ce Sakin Ya yi, Sa'annan Daman shi Saki Niyya ce daga Zuciyar namiji idan ya yi Niyya ya ambata shi ke nan ya yi Ma'ana Sakin ya Tabbata. idan Kuma an ɗauki Cewa Sakin Bai yiyu ba, toh shi ne Maganar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da Abdullahi Ɗan Umar. Fatan kin Gane Koh??

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

𝐅𝐀𝐂��𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments