Ticker

6/recent/ticker-posts

Hana Aure Domin Yana Da Yara

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Budurwa ceTa kawo wanda take so ta aure shi wanda ba ya shaye-shaye ba ya komai, amma sai iyayenta suka ce a’a, domin wai ya taɓa yin aure kuma yana da ’ya’ya. Yaya za su yi ita da shi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Abin da za su yi guda biyu ne: Haƙuri da ƙoƙari

Su yi haƙuri wurin bin maganar iyaye da yawaita adduoi ga Allaah Tabaaraka Wa Taaala.

Kuma su yawaita ƙoƙarin yin bincike kan gaskiyar dalilin rabuwarsa da uwar yaran nasa.

Idan an gano cewa rabuwarsu da ita ba zai iya cutar da zamantakewarsu ba, sai su ƙara yin haƙuri tare da ƙara ƙoƙarin sanar da iyayenta hakan, kuma da ƙara rarrashin su ta hanyar da ta dace cikin ladabi, har su fahimci gaskiyar alamarin.

Amma idan aka gano cewa iyayen ba su son yarinyar ta auri wanda ya taɓa aure ne kawai, to wannan da farko dai ba abu ne da shari’a ta hana ba. Hasali ma a halin da ake ciki yanzu, wanda ya taɓa yin aure na iya zama shi yake iya riƙe matar fiye da wanda bai taɓa ba, matukar dai mutumin kirki ne. Don haka, a nan ma dai sai a ƙara ba iyayen haƙuri, a ƙara ƙoƙari wurin rarrashin su cikin ladabi da kyawawan kalmomi.

Sannan kuma da haƙuri wurin ƙara yawaita adduoi.

Idan ba za su iya tinkarar iyayen su da su kai-tsaye da maganar ba, suna iya sanya wasu abokanan iyayen ko malamansu ko danginsu ko ƙawayensu ko dai saoinsu da suke mutuntawa, su wuce musu a gaba, har su iya fahimtar da su irin abin da suka kasa ganewa a cikin matsalar.

Wannan yana daga cikin illolin fara neman aure ba tare da sanar da iyaye tun da farko ba. Domin in da yarinyar ta fara sanar da iyayenta tun kafin ta amince da wannan namijin a matsayin masoyinta wanda take son aurensa, kuma in da iyayen sun fara gudanar da bincikensu a kansa tun nesa-da-ƙofa, to da kuwa, in shà Allâhu ba a samu wannan matsalar ba.

Dole ne matasa a yau su san cewa, shari’a ba ta amince da irin waɗannan halayya na matasan zamanin yau ba: Inda yarinya take yin gaban kanta wurin nema wa kanta namijin da take so ita da kanta kaɗai. Wai sai a bayan sun gama ‘fahimtar juna’ da shi ne sannan za ta kawo shi wurin iyayenta! Kuma ta ɗauka sai kawai su amince da ita kuma su sanya mata hannu, ba tare da bincike ko dubawa ba, saboda kaɗai, a ganinta: Ai ‘ba ya shaye-shaye, ba ya yin komai’.

Dole ne matasa su san cewa, kamar yadda mawaƙin Hausa yake cewa

Aure ba abu ne ba na wasa,

Bar neman kyau, nemi nagarta.

Watau: Shi aure wani ƙullin zamantakewa ne na har-abada. Don haka yana buƙatar a samu gogewa da zurfafa bincike da tunani da hangen nesa a cikinsa kafin a ƙulla shi.

Irin gogewa ko ƙwarewar da matasa ba su da ita, ko da kuwa sun haɗa ƙarfi da ƙarfe a tsakaninsu don kai wa ga hakan.

Allaah ya faɗakar da mu, kuma ya ƙara mana ilimi mai amfani.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments