Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Daga Hannu Lokacin Addu'a

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum mallam ina da tambaya mallam ya halatta kana addu'a kana ronkon Allah ka ɗags hannunka sama?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam.

Eh lallai ya halatta mutum ya ɗaga hannunshi lokacin addu'a, hadisai da yawa sun nuna hakan kamar hadisin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ke cewa " lallai Ubangijiku mai kunya ne, mai karamci ne, yana kunyar bawa ya ɗaga hanunshi ya roqeshi amma ya mayar dasu batare da komai ba" haka manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya lissafa ɗaga hannu yayin addu'a cikin sabbuban Amsa addu'a, dan haka ya halatta, sai dai inda manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam bai ɗaga hannu ba bazamu ɗaga ba, kamar lokacin da liman ke huɗubar jumma'a, ko tsakanin sujjada biyu, kenan inda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ɗaga 7Uuu ɗaga, inda bai ɗaga ba bazamu ɗaga ba, a addu'oinmu na yau da da kullum zamu ɗaga matuqar shari'a bata hanamu ba.

Allah ne mafi sani

Amsawa:🏻

ABDULLAHI ISMAIL AHMAD.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IqsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments