Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Maziyyi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Me ya kamata mutum ya aikata idan maziyyi ya fito masa sanadiyyar ƙaramar shaawa, kamar yin waya da mace da sauransu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Da farko in ban da fitsari akwai abubuwa guda uku da suke fitowa daga mafitan fitsarin, su ne: Wadiyyi da Maziyyi da Maniyyi. (Ibn Abi-Shaibah: 1/89)

Maziyyi ruwa ne tsararo mai yauƙi da yakan fito saboda ƙaramar shaawa, ba da tunkuɗar juna ba, kuma ba tare da samun sakin gaɓoɓin jiki a bayan fitowansa irin na maniyyi ba. Wani lokaci ma ba a sanin fitowarsa.

Maziyyi najasa ne, ba kamar maniyyi wanda malamai suka yi saɓani game da shi ba, kuma sahihiyar magana a wurinsu a kansa ita ce: Shi (maniyyi) ba najasa ba ne. (Fiqhus Sunnah)

Maziyyi ana samunsa ne yawanci ta hanyoyin da suke motsar da sha’awa, kamar haka

1. Yin tunani a kan al’amarin saduwa a tsakanin masoya.

2. Sauraron maganganun sha’awa a tsakanin masoya.

3. Kallon sha’awa ga jiki ko al’aurori a tsakanin masoya.

4. Murmushi ko dariyar sha’awa a tsakanin masoya.

5. Magana ko hirar sha’awa a tsakanin masoya.

6. Keɓantuwa a wani wurin tsakanin masoya.

7. Sansanan ƙamshin juna a tsakanin masoya.

8. Shafar wani sashe ko dukkan jiki a tsakanin masoya.

9. Haɗuwar al’aurorin masoya ba tare da zarcewa ko nutsewa ba. (Sabon Saurayi)

Wajibi ne ga wanda maziyyin ya same shi ya wanke dukkan al’aurarsa gaba ɗaya (azzakarinsa da marenansa), kuma ya sake alwala. (Al-Bukhaariy: 269, Muslim: 303, Abu-Daawud: 208)

Idan kuma maziyyin ya shafi tufa ne, to shari’a ta yi sassauci in aka ɗebi ruwa aka jiƙa wurin da ya shafan kawai, ya yi. Kamar dai fitsarin jariri. (Abu-Daawud: 210, At-Tirmiziy: 115, kuma ya ce: Kyakkyawa ne, ingantacce).

 WALLAHU A'ALAM

Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments