Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Shan Fitsari

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam, wai menene hukuncin mutum ya sha fitsarinsa a matsayin magani?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Ya zo a cikin siffofin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa: Kuma yana halatta musu daɗaɗan abubuwa, kuma yana haramta musu munana. (Surah Al-A’raaf: 158).

Kuma tun dayake fitsari ƙazanta ne kuma mummuna, to ya shiga cikin haramtattun abubuwa kenan.

Shiyasa malamai suka haɗu a kan cewa: Fitsari da kashin mutum duk najasa ne.

Shi kuma najasa wajibi ne kowane musulmi ya nisantar da jikinsa da tufafinsa daga gare shi.

Kuma haram ne musulmi ya yi amfani da najasa ta fuskar ci ko sha ko shafawa a jiki ko a tufafinsa ko mazauninsa.

Sannan ko da da sunan magani ne, hakan ɗin bai halatta ba saboda maganar malamai da Al-Imaam Al-Bukhaariy ya kawo a cikin Kitaab Al-Ashribah a farkon Baab na: 15 cewa

وَقَالَ الزُّهْرِىُّ : لاَ يَحِلُّ شُرْبُ بَوْلِ النَّاسِ لِشِدَّةٍ تَنْزِلُ ، لأَنَّهُ رِجْسٌ ، قَالَ اللَّهُ تَعَالَى : ( أُحِلَّ لَكُمُ الطَّيِّبَاتُ )

Az-Zuhuriy ya ce: Shan fitsarin mutane bai halatta ba saboda wani tsanani da ya sauka, domin shi ƙazanta ne. Allaah Taaala ya ce: An halatta muku daɗaɗan abubuwa.’ (Abdurrazzaaq ya riwaito shi da isnadi ingantacce).

Sai kuma ya ce

وَقَالَ ابْنُ مَسْعُودٍ فِى السَّكَرِ : إِنَّ اللَّهَ لَمْ يَجْعَلْ شِفَاءَكُمْ فِيمَا حَرَّمَ عَلَيْكُمْ .

Kuma Ibn Mas’ud ya faɗa a kan kayan maye: Haƙiƙa! Allaah bai sanya warakar ku a cikin abin da ya haramta muku ba. (Ahmad a cikin Kitaab Al-Ashribah da At-Tabaraaniy a cikin Al-Kabeer suka riwaito shi da ingantaccen isnadi).

Wannan maganar ta zo marfu’iyah daga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) sai dai ba ta inganta ba, kamar yadda Al-Haafiz ya kawo a cikin Fat-hul Baariy: 12/634, kuma Al-Albaaniy ya bayyana matsayinta a cikin Da’eef Al-Jaami’: 1637.

Kodayake malamai sun tattauna a kan darussan da su ke cikin waɗannan atharan, amma dai a ƙarshe abin da Al-Haafiz Ibn Hajr ya nuna shi ne, maganar nan ta Al-Imaam Az-Zuhuriy ita ce ingantacciya, matuƙar dai ya tabbata cewa shan fitsari ba ya kore ƙishirwa. (Fat-hul Baariy: 12/633).

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments