Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Farin Ruwa Da Ke Fitowa A Gaban Mace

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Akwai wani farin ruwa ne da ke fitowa daga mace. Shi najasa ne ko kuwa? Sannan kuma yaya mace za ta iya magance shi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Abubuwan da suke fitowa ta gaban mace nau’i biyu ne: Jini da abin da ba jini ba.

Jinin nau’i uku ne: Haila da Nifasi da Istihaala. Dukkansu najasa ne, sai dai an yi sassauci ga mai sallah, ko da yana cigaba da zubowa ba laifi.

HAILA ita ce jinin da ke fitowa saboda dalilin balaga kawai, ba domin wata matsala ba.

NIFASI kuwa shi jinin da ke fitowa saboda dalilin haihuwa.

ISTIHAALA kuma tana fitowa ne saboda dalilin rashin lafiya ko fashewar wata jijiya, ko kuma zungurar wani shaiɗanin aljani.

Abubuwan da ba jini ba kuwa, in ban da fitsari akwai: Maniyyi da maziyyi da kuma wadiyyi.

MANIYYI yana fitowa ne a lokacin babbar sha’awar jima’i a barci ko a farke. Shi ba najasa ba ne a maganar da ta fi inganci a wurin malamai.

MAZIYYI kuwa yana fitowa ne saboda ƙaramar shaawa, kamar a lokacin wasanni soyayya a tsakanin maaurata. Shi najasa ne, sai dai an yi sassauci ga matasa a wurin jiƙa tufafin da ya shafa kawai maimakon wankewa.

WADIYYI kuwa yana fitowa ne yawanci a ƙarshen fitsari a maza. Ban san yadda ya ke ga mata ba. Amma dai shi ma najasa ne, kamar fitsari.

Waɗannan su ne abin da na sani game da ruwa mai fitowa daga gaban mace.

Sai dai kuma a cikin littafin Zuwa Ga Sabuwar Budurwa 1, na ambaci magana a kan danshin gaba, wanda ya ke ba najasa ba ne a magana mafi ƙarfi a wurin malamai. Ga abin da na ce

Masana sun nuna cewa, samuwar wannan (danshin gaba) da yawaitarsa daga ‘gaban’ yarinya a daidai wannan lokacin (na balaga), ba wata matsala abar damuwa ba ce. Abin da suka ce dai shi ne

(i) Yana taimaka wa mace ne wurin hana bushewa ko ƙeƙashewar gaban nata.

(ii) Yana hana ta kamuwa da waɗansu ƙwayoyin cuta ta wannan wurin.

(iii) Alama ce mai ƙarfi na cewa yarinya ta kusa soma yin alada! Don haka sai ta kiyaye.

(iv) Amma idan ruwan ya zama mai kauri, mai duhu ko rawaya-rawaya, mai wari-wari kuma mai jawo ƙaiƙayi ko raɗaɗi a jiki, to wataƙila ƙwayoyin cuta sun shiga ne. Sai ta tuntuɓi likita.

Don haka, idan abin da ake tambaya a nan ba ɗaya daga cikin abin da na ambata ba ne, to sai a kusanci wasu masana a makarantu ko masallatai ko kuma likitoci a asibiti.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

𝐅𝐀��𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments