Ticker

6/recent/ticker-posts

Barkwanci Shida Daga Taskar www.amsoshi.com

Barkwanci
Malam ka ji tsoron soyayya da mace mai wanka da soson buhu a lokacin sanyi.

Barkwanci
Audu: "Kada ka sake zuwa wurin ƙanuwata zance!" 

Idi: "Da wannan lambar ka buɗe Opay?"

Audu: "E, ya daɗe ma. Saƙon da na turo a sama kuma typing error ne."

Barkwanci
Ina za mu zauna lafiya, Anas kaɗai ya yi wa 'yammata 10 alƙawarin aure a ƙarshen December?? 💔😅

Barkwanci

Ango ya ce wa amarya a rayuwa babu abin da yake burge shi kamar abinci mai ƙamshi.
Zainabu ta zuba turaren wuta cikin miyar kuɓewa. 🥳🥳

Barkwanci
Lamarin ƙasar nan sai a hankali. Yanzun nan ake ba ni labarin wani ɗan ajinmu a sakandare ya zama boka. 🏃‍♂️😅

Barkwanci
Ki riƙa buɗe status a-kai-a-kai, kada a yi bikin mijinki ba ki sani ba🥱🥱


Post a Comment

0 Comments