Ticker

6/recent/ticker-posts

Zarce (...)

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

488. Zarce masu yin sa su ne gogaggu,

 Kuma su sun wuce a ce masu jemagu,

 Ilimi ag garesu sosai sun gogu,

 Sun zama malamai, ga ilmi sun tsawgu,

  Masana mazhabar rubutun Hausawa.

 

489. Ba a saka shi sai wurin adana zance,

 Sai a saka shi, don alamar mu ta zarce,

 Sannan ma akwai shi har ma a magance,

 Amma dai a nan da aikinsa rubuce,

  Daidai gun gaɓa a bar ka da idawa.

490. Sarki goma... sai a bar ka a ƙyale nan,

 In ka karanta tambaya biɗo amsar nan,

 Kuma sai wadda za ta dace da wurin nan,

 A zato na da Hausa ka san tsarin nan,

  Amsa zamunansa goma ga Hausawa.

 

491. In aka sa shi mai karatu ya kiyaye,

 Dole ya nemo tasa amsa kai waye,

 Kuma ai dai ana buƙatar ko waye,

 Ya kula don rubuta amsa ba ɓoye,

  Shi aka son ya ƙarasa don ganewa.

 

492. Saɓaninsu gun karan-ɗori lura,

 Aikinsu daban tsaya nan saurara,

 Zarce ba ya ɗora kalmomi sara,

 Bai kuma tara zuntukanmu ya ɗoɗɗora,

Ba ya biɗar wurin da za a yi nunkawa.

 

493. Ba ya zuwa a tsakkiya sai dai ƙarshe,

 Can aka sa shi za ka hango shi a tarshe,

 Bai da kama da tarinmu na kwashe,

 Ɗan layi ake  gaban kalmar ƙarshe,

  Jimlar ta ƙire a neme ka cikawa.

 

494. Ba a saka shi sau guda don a kula shi,

 Dole a ɗiɗɗiga shi nan ga muhallin shi,

 Haka ne zai fi kyau ga doka a kula shi,

 Kar a yi ɗan guda hakan na kwaɓe shi,

  Sau uku ko aji biyar ba a hanawa.

 

495. An ce kog ga raƙumi, shi ga..... to ida,

 An so wanda zai isar da jawabin da,

 Yai lura da yadda zai sa ga takarda,

 Kar ya yi ɗan guda, ya ƙara gaba sada,

Zarce ne guda biyar to shiga ƙyargawa.

 

496. Masu bugun ƙasa, a jinsi na mutane,

 Mu nan Hausa yanzu boka Arne ne,

 Shi muka ba irin cikon jimlar gane,

 Yau ƙarya ƙasa take in ji... su wane,

Mai duba da yag ga yau za shi macewa.

 

497. Zarce ukku an ka sa nan ga rubutu,

 Ba laifi a sa su don masu karatu,

 Su sani ba turaddadin ko ɓaɓatu,

 Ko da fiye ma abin nan ya kyautu,

Ko haka an ka yi shi duk ba a hanawa.

 

498. Labari na zuciya tambi.. abokai,

 Wansu su zana fuska kuma ba kai,

 An kuma tsara duk abin an bi matakai,

 Doka ce ta ayyana kar ka bi son kai,

  Ko biyu an ka sa abin bai sauyawa.

 

499. Zarce ba a yin sa sau ɗaya ko ƙaƙa,

 Kul kul kar a sa guda don sauƙaƙa,

 In ka sanya ɗan guda ka kitsa tufƙa,

 An saɓa wa ƙaida an saka sarƙa,

  In aka yi shi sau guda sai sokewa.

Post a Comment

0 Comments