Ticker

6/recent/ticker-posts

Baka Biyu ( )

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

500. A rubutu ana alamci ya alamtu,

Masana sun kiyaye doka ta rubutu,

 Sun kuma gargaɗe mu, mu masu karatu,

 Sun yi kira gare mu sun so mu fahimtu,

Sun ka aza ta gunmu domin koyarwa.

 

501. Lura da kyau dai baka idan za a saka ta,

 Tai siga kamar bakar nan ta farauta,

 Wadda ake gani ga hannun mafarauta,

 Ita wannan baka idan za ka saka ta,

  Zance zai zamo tsakanta ga tsarawa.

 

502. Ba a saka ta don ƙawa ko burgewa,

 Kuma ba kwalliya ake ba ga zanawa,

 Ya zama wajibi a sa ta ga tsarawa,

 Ita ke ƙara bayyana mana ganewa,

  Hujjar sa ta ɗan bayanin sadarwa.

 

503. In ka je Kano akwai sallahu (saƙo),

 Can Zamfara ko bara shi ne (roƙo),

 Shi Bakabe yana da na masƙi wai (maiƙo),

 Har yau dai muna da kawo wai (miƙo)

Yadda Basakkwacen mutum zai ganewa.

 

504. Can a ƙasar Kano akaifa (farce) ce,

 Haka farce wajenmu ko ai (yatsa) ce,

 Shi yatsa jihar Kabinmu ai  farce ce,

 Shi kuma farcen wajen su akaifa ce,

Wasu ko Sakkwatonmu ƙumba suka cewa.

 

505. Waliddai (iyaye) a kyautata masu tilas ne,

 Sanya baka a nan ku gane doka ne,

 Larabci da Hausa ne duk mun gane,

 Yin ɗa’a gare su ai ko tilas ne,

Domin tsallake uƙubar (azabar) ƙonewa.

 

506. Je ka gaya wa baba (Mudi) mun sadu,

 Mun haɗu can (kasuwa) ni da Sa’idu,

 Ya kuma ce a gai da ‘yar Manu da Audu,

 Dangin nan a san da gurinsu su sadu,

Matata (Halima) mun ƙara haɗewa.

 

507. Shi ƙwaro (baubawa) haƙiƙa wauta ka kashe shi,

Don ba ya da Hausa (Azanci) bami yake ji shi,

 Koyaushe ka gan shi bai da dabara shi,

 Kuma ya dambale, da aiki a cire shi,

Ko an sha kwatse (hana) shi bai iya hangowa.

 

508. Tica (malami) ba a son yana halin assha,

 Ban kuma son ace da shi wane yana sha,

 In kuma ya yi ya kasance sha-sha-sha,

 An fi da son ya ƙaurace wa wurin assha!

  Haddai in da ɗalibai ke gittawa.

 

509. Kalmomin da mun ka sa a baka kenan,

 Lura da su ka ƙara kwance bayanin nan,

 Doka ce ta yin baka ga rubutun nan

 Su ke ta ƙara haskake kalmomin nan,

  Ƙari ne wajen bayanin ganewa.

 

510. Ba don su ba da abin sai kirdado,

 A karanta a sa ke bi gardo-gardo,

 Ba a gane ba, ba bari sai ɗai kirdado,

 Ba kwanon jido ruwa an sayi kwando

  Ma’anoninsu ɗalibi bai ganewa.

 

511. Sa su cikin baka a nan zai nuna ma,

 Ƙari kan batun da an ka rubuta ma,

 Dalla-dalla su warware har su daɗa ma,

 Sai ka fahimce su don ka gane ko da ma,

  Shi ne fassarar su don tantancewa.

Post a Comment

0 Comments