Ticker

6/recent/ticker-posts

Karan Ɗori (-)

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

474. Doka ce ta gwama kalma biyu tare,

 Wani sa’in sukan fi biyu ga su a jere,

 In aka sa shi an haɗe su suna cure,

 Don haka za a zo da shi tsakiya tsare,

  Don su haɗe wuri guda ba a rabawa.

 

475. In aka sa shi babu sauran kirdado,

 Ba sauran a zo a yo muna gadodo,

 Ma’ana ta fito, karanta muna Lado,

 Sharaɗi ya cike a harshenmu na gado,

  Kalma ta zamo guda ga hukuntawa.

 

476. Wani ɗan lokaci yakan shiga sunaye,

 Sai a kula shi in ya zo daɗa kai waye,

 Ɗan layi yake zuwa tsakiya jaye,

 Doka ta aminta sa su a jeranye,

  Su biyu ko fiye da su za a haɗewa.

 

477. In aka zo faɗar sa domin nunkawa,

 Sunayen gaba ɗaya ga rubutawa,

 Za ka saka su, sai alamar ɗorawa,

 Ka ga gari-gari a gun mai furtawa,

  Dubi gida-gida misalin ganewa.

 

478. In ga sifa ya zo idan aka nunka ta,

 Ita ma za a sa shi in za a rubuta,

 Shi zai warware ma kowa ya karanta,

 Shi ke nuna za a nunka ga faɗinta,

  Za a yi ɗan karan tsakani na rabewa.

 

479. Ɗauki misali ga masu yin kiwon dabba,

 In har za ka zaɓi dabba don riba,

Za ka rubuta dogo-dogon nan babba,

 Ko kuma mai baƙi-baƙin nan na duba,

  Ya ɗara wake-wake ƙoshin turkewa.

 

580. Har a bayanau akwai ta nan ta wanzu,

 Dubi misali da za a bayar tun yanzu

 Wanki sannu-sannu, amma sun darzu,

Zabura yanzu-yanzu don ya fita ɗazu,

  Sai ka yi sauri-sauri don ba a sakewa.

 

481. Ka ga fa ɗanya-ɗanya ce wannan gwanda,

Sa mana wada-wada gun kalmar wada,

 Haka ma sanda-sanda gun kalmar sanda,

 In ka kula halin karan-ɗori sada,[1]

Dat tsaka zai shiga ga dokar nunkawa.

 

482. Wasar doki-doki sai gun ‘yan yara,

 Haka nan lambe-lambe su ne na lura,

 Ko wargi na ɓoyo-ɓoyo in sun tara,

 Wasar langa-langa ma ta zama sara,

  Sai a yi goyo-goyo domin sheƙawa.

 

483. Duk kalmar da mun ka nunka ka kiyaye,

 Mun mata ‘yar alama haka gindaye,

 Nan tsaka mun ka zo da dokar kai waye,

 Kowace kalma gabanta ɗan layi jaye,

  Za mu sako karan da zai zo ɗorawa.

 

484. Ɗan layin da an ka zana tsakiyarsu,

 Ai shi ne ya ɗora kalmar jimlarsu,

 Sun ka zamo guda ga tsarin aikinsu,

 Wato dai ya nuna aikin nunkasu,

  To shi ne kara ga dokar ɗorawa.

 

485. Ƙiuyar sa shi kuskure ne munana,

 Dole a sa shi in ana neman ma’ana,

 Ai ƙin sa shi ya zamo yankan ƙauna,

 Ga karatunsa nan ake faman ɓarna,

  Jimla za ta yamutse ba ganewa.

 

486. Lura da su dukan misalan ka fahimtu,

 Don kar ka ɓata hankalin masu karatu,

 In aka sa shi sai ya zam ya daidaitu,

Kalma duk da an ka katse ga rubutu,

  Kan a cika ta to kara za a sakawa.

 

487. Matuƙar dai ka fara kalma ƙarshe ja,

 Ɗan layi ka sauka sannan ka cika ja,

 Shi ka nuna isuwar kalmar ba ja,

Ga misali ka ce fararen daj jaja-.

Ye sun hana babbaƙun budare lelawa.[1] Kalmar “sada” tana nufin “koyaushe.” Wannan kalma an fi amfani da ita a yankin Sakkwato da Kebbi.

Post a Comment

0 Comments