Ticker

6/recent/ticker-posts

'Yar Damisa (Kashi na 1)

Labarin ya faro a cikin Gidan Alhaji Damisa. Uwargidansa Hajia Jummala na zaune a cikin babban daki, sai Alhaji Damisa ya shigo sanye da babbariga da hula, rike da carbi a hannunsa na dama yana ja a hankali ya samu waje kusa da matarsa ya zauna, ya kammala wuridin da addu'a. Hajia ta juya kofin da ke kife a kan tebur.

Hajia Jummala:

Malam barka da asuba

Alhaji Damisa:

Yauwa, kin tashi lafiya, yaya ciwon kan riaki?

Hajja Jummala:

Da sauki, dama rashin barci ne. Alhamdulillah (ta zuba masa ruwan shayi mai zafi) Ko in sa maka madara?

Alhaji Damisa:

Zuba dan kadan da sukari kwaya biyu (ya mayar da carbinsa cikin aljihu)

Hajia Jummala:

(Ta sa madara da suga ta motsa da cokali, ta mika masa) Ga-shi

Alhaji Damisa:

(Ya karbi kofin ya kurbi kadan) Mmhm, kai ba dai iya shayi ba (ya kalle ta yana murmushi)

Hajia Jummala:

Allah ne abin yabo. Ina fatan ba shayi kawai na iya ba? (cikin fara'a)

Alhaji Damisa:

Haba da ban kara aure ba? (Suka bushe da dariya)

Hajia Jummala:

Malam ke nan, har ka sani dariya (Bayan dan lokaci kankani) Malam batun 'yar nan Lauratu, Sakamon jarawarta na sakandare bai yi kyau ba. Takardu uku kawai ta samu cin kiredit, biyu kuma ta sha da kyar sauran kuwa ba magana. Ba haka na zaci za ta kasance mata ba.

1>>>
'Yar Damisa - Gabatarwa

From the Archive of:

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +2348067062960

©2023 Tijjani M. M.


Post a Comment

0 Comments