𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum, na kasance ina jinin al'ada kwana shida 6, to amma innayi kwana huɗu 4 sai ya ɗauke, Rana ta biyar zan
wuni har dare bakomai, sai Rana ta shida zai dawo da asuba,
To Mallam
ranar da baizoba Zanyi wanka ne in cigaba da sallah ne ko zan dakata ?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
An tambayi Sheikh
muhammad bin swalih al'uthaimeen-(rh) irin wannan tambaya, sai ya ce: Abinda ya
fi bayyana shi ne wannan tsarki da take gani kokuma bushewan farji wanda yake
zuwa mata acikin kwanakin hailanta, shima hailane ba tsarkiba. Saboda haka za
ta cigaba da barin duk abinda mai haila za ta bari.
Wasu daga
cikin malamai suka ce: Wanda take ganin yau jini gobe babu jini. To jinin,
jinin hailane. Rashin jinin kuma tsarkine. Matukar bai wuce kwana sha biyarba
(15days). Wannan shi ne fahimtan mafi yawa daga cikin malaman mazhaban
hanabila.
Sai dai bisa
ga wannan bayanai guda biyu zance tsaka-tsaki shi ne: Awayannan kwanaki idan
jinin ya yanke sai taga alaman tsarkinta, (wato taga wannan farin ruwa) lokacin
tsaya wan jinin, to wajibine ta yi wanka ta yi sallah. Idan jinjn ya dawo sai
ta bar yin sallan. Idan kuma bataga alaman tsarkiba, to za ta zauna ciki wannan
halin harsai taga alaman tsarki. Wannan shi ne abinda shekhul islam ibnu
taimiyyah ya tafi akai.
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.