𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Kafin na fara
Al'adata, nakan lura da zubar jini/ruwa mai launin kalar kasa (brown discharge)
Kuma Yana kaiwa tsawon kwanaki biyar, Bayan nan kuma sai jinin Al'ada ya biyo.
Jinin Al'adar yana daukar tsawon kwanaki takwas bayan kwanaki biyar na farko.
Nakan yi Sallah cikin kwanaki biyar ɗin
amma sai nake shakkun yin azumi da sallah cikin wa'ennan kwanaki biyar ɗin na farko ko a'a? Don
Allah ka bani shawara, Allah ya saka da alkhairi.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan cikin
kwanaki biyar ɗin da
kike ganin ruwa mai launin kasa (brownish discharge) ba haɗe yake da kwanakin da
kike ganin jini hailar ki ba, toh ba ya ɗaukar
hukuncin jinin Al'ada, don haka zaki yi sallah cikin wa'ennan kwanakin biyar da
azumi.
Amma kuma zaki
jaddada alwala ga ko wani sallah idan zaki yi. Saboda ya na ɗaukar hukunci ne daidai
da na fitsari, amma ba na Al'ada ba.
Kenan hakan baya nufin cewa bazaki iya yin sallah ba ko
azumi, amma zaki rika yin alwala duk sanda kika tashi yin sallah, har sai
lokacin da wannan ruwan ya yanke, kamar yadda hukuncin jinin istihaadah (jinin
cuta/non-menstrual bleeding) yake ɗauka.
Amma idan
wa'ennan kwanaki biyar ɗin
haɗe suke (bima'ana
babu wani tazaran lokaci a tsakani) da kwanaki takwas da kike yin al'ada, toh
hukuncin wannan ruwa mai launin kasa-kasa (brownish discharge) ɗin, daidai yake da na
jinin al'ada, don haka bazaki yi sallah ba ko azumi cikin wa'ennan kwanakin.
Haka zalika, a
karshen Al'adar ki, fitar ruwa mai launin kasa (brownish), ko me fatsi-fatsi
(yellowish discharge), baya ɗaukar
hukuncin jinin Al'ada, amma ya na zuwa ne karkashin hukuncin istihaadah (jinin
cuta), don haka zaki rika yin tsarki ki jaddada alwala akan ko wani sallah idan
zaki yi.
Sannan zaki yi
sallah da azumi da kuma rayuwar aure da mai gida. Dalili kuwa shi ne hadithin
Ummu Atiyyah:
كنا لا نعد الكدرة
والصفرة بعد الطهر شيئا " أخرجه البخاري في صحيحه وأبو
داود وهذا لفظه).
Ki duba:
Majmoo’ Fataawa na Shaykh Ibn Baaz, 10/207
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.