Ticker

6/recent/ticker-posts

Wuraren Rubuta Manyan Bakake

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

525.  Duk harafin da za a zana a rubutu,

 In har dai ana buƙata ya karantu,

 Ba zancen a kama furcin sabbatu,

 Matuƙar dai ana buƙatar ya karantu,

  Sai a bi ƙa’idar rubutun Hausawa.

 

526.  Manya da ‘yan ƙanana duk a bi tsarinsu,

 Duk bagiren da ke buƙatar a saka su,

 An tanadi inda yak kamata a sanya su,

 Shi ne ƙa’idar rubutu ka kula su,

  Kar a yi yamutse abin zai kwaɓewa.

 

527. Shi babban baƙi muhallinsa a keɓe,

 An masa tanadin wurinsa yana keɓe,

 Ba ya zuwa wurin ƙananan ya la~aɓe,

 In ko ya je kusan rubutun zai kwaɓe,

Matuƙar ba wurinsa ba ne ba ya tsayawa.

 

528. Ba a saka shi ko’ina barkace watse,

 Babu batun a gan shi ya yo kutse,

 Ba ya zama cikin ƙanan ko an matse,

 Kuma doka gare shi ta hana kutse,

  Bi ni a sannu ga su nan zan nunawa.

 

529. Harafi lamba Wan ga jimla a kula shi,

 In dai har ƙida ake buƙata a yi to shi,

 Za a saka, ya zo a farko na rubuta shi,

 Ba a buƙatar a sanya ɗan karamin shi

  Dole ya zamto babba ne za a sakawa.

530. Shi harafi babba in har ya taho,

 Ko ya zamo baƙi walau wasali oho,

 Ko ko tagwan baƙi fa duk an yo ho,

 Ron, a rubuta babba kar a yi ko oho,

Dole ya zamto babba gun mai zanawa.

 

531.  Sai ka kiyaye duk rubutun waƙar nan,

 Tun farkon rubuta sunan waƙar nan,

 Kai saka babukan da ka ga kitabun nan,

 Babu guda wanda mun ka ƙyale sannan,

  Farkon sheɗara da shi muka farawa.

 

532. Ayar tambaya idan an ka saka ta,

 Ƙarshe za a ganta a jimlar ta,

 Sai ku sani akwai buƙatar amsar ta,

 Bayan ta biyo a ƙarshen jimlar ta,

  Harafi babba zai biyo gun zanawa.

 

533.  Wane ne ya ce? Ku ba ni dalilinku?,

Maikwari ne, Abu-Ubaida muna shakku,

Mun daɗa sheɗara ga waƙar har ukku,

Tahmisi mukai ga waƙar ba shakku

  Wa ya kashe wuta? Alu bai kunnawa.

 

534. Don me kun ka bar shi har yai maku ɓarna?

 Ga shi gaban ku ya tsaya ƙarna-ƙarna,

 Ya sa ƙaramin baƙi muhallin don ɓarna,

 Marmaza shafe shi, kar ya zam an yo ~arna,

Kun yi kure abin ga ya wuce ƙyalewa.

 

535.  Don wa an ka ba ku? Shin wa yas sa ku?

 Maikwari ne ya sa ku? Ko ra’ayin kanku?

 Shin wai dai ina Abu-Ubaida ya iske ku?

 Shin kun san da Bunza ya yaba aikinku?

  Kowace tambaya alama aka sa wa.

 

536. In kuma an saka ta ta cika shi ke nan,

 In aka sa ta can a ƙarshen jimlar nan,

 In ka gan ta ta taho a muhallin nan,

 In ma’anar tambayar ka ta cika sannan

  Harafi babba zai biyo bisa tsarawa.

 

537. Motsin rai idan ta zo sai a kula ta,

 Sai a kula da inda doka ta aje ta,

 Kar a saka ta inda babu muhallinta,

 Can bagiren da an ka tanada za a saka ta,

  Duk dokarsu ɗai ka zan mai ganewa.

 

538.  Wayyo! ‘Yan wala-wala sun washe shi,

 Sun washe kuɗin shi babu ko sisi gun shi,

 Sun bar shi tsula yana zufa har bisa goshi,

 Kaico! Wanga ɗa akwai tausai gun shi,

  Sun cuce shi sun hana masa ganewa.

 

539. Masu hali na yaudara nai masu kaico!

 Kaiconku! Mayaudara, gare ku na ce kaico!

 Mtsw! Ƙyale su ai gare ka wala gacco,

 Duk mai yaudara ku ce nai masa kaico!

  Ba su haye tudun siraɗi ga wucewa.

 

540. Can ga faɗar haba! Da to! Mai dogewa,

 Koko ka ce iye! Da ƙarfi don ƙosawa,

 Kai! Kai! Kai! Kana da niyya ta kwatsewa,

 Ko kalima da za ta sosa rai don tausawa,

  Motsin rai akai ka zan mai ganewa.

 

541. In ka ce Alu! Da niyyar ka kwatse shi,

 Ko ka hanai faɗin abin da ka damun shi,

 Kar ya fito ya furta zance son ran shi,

 Sai ka kwatsai gudun kar ya faɗe shi,

Kar ya shige wuyar da bai iya zagewa.

 

542. Duk kalmar da rai ka motsin furtawa,

 Ko da faɗinta kaj ji rai na sosawa,

 Matuƙar dai da razana gun furtawa,

 Ko a ji tausai ana batun a yi kokawa,

  Ayar za a sa wurin don nunawa.

 

543. In aka sa ta ko’ina sai a kiyaye,

 Ko ka ji an ce da kai Alu! Zo nan ɓoye,

 Masu karatu ku lura kanku yana waye,

 In ta biyo cikin rubutu a kiyaye,

  Harafi babba zai biyo ba sauyawa.

 

544. Lura da kyau idan ka ce: wayyo! Baba,

 Ko ko ka ce: na boni! Ana yi mani zamba,

 Matuƙar ka yi fargaba da ‘yar murya babba,

 In dai har ga ranka, ka ji tsawa babba,

Ko gwai! Manu manya-manyan ka biyowa.

 

545. Aya babba ɗan ɗigo ke nuna ta,

Za ka ga an ɗiga shi ƙarshen jimla ta,

 Shi zai zo cikin rubutu a kwatanta,

 Daura inda an ka yo na muhallinta,

  In aka yi ta nan bayani ka tuƙewa.

 

546. Ba ta zuwa ko’ina fa ko an yi dabaru,

 Sai bagire nata inda jimla tat taru,

 Ga ma’ana ta fito da saƙo an ƙaru,

Ba a saka ta sai bayani ya tsaru,

  Jimla ta yi cif-da-cif babu ragawa.

 

547. Ta zama kamila bayani ya gamsu,

 Ga ma’anarta ta fito a fili an gamsu,

 Jimla ta cike ci-cif ba masu musu,

 Ta kammala duk lafuzzan sun tarsu,

  Kowaj ji shi take zai iya ganewa.

 

548. To a wurin ake biɗar aya babba,

 A dasa don ta nuna ka hutawa babba,

 Ai da isar ka za ta yi mak ka maraba,

 Da ɗigo babba, don ka san a tsaya ba

  Mai yin bita nan yake numfasawa.

 

549. Ba a shiga ruwa idan ba a koya ba,

 In ko ka shiga akwai wahala babba,

 Sa lura zan awon tunani ka yi duba,

 Kar ka shiga idan ba ka iya iyo ba,

Kwas shiga bai iya ba ko ba ya fitowa.

 

550. Tsorci Ubangiji guda Sarki babba,

 Wannan da ya ce a zan girmama babba,

 Ya yi umurni garemu yarammu da babba,

 In mun yi kure mu lura mu yo tuba,

Da nadama ga kuskure zan ka kulawa.

 

551. Kob bi Nabiyu ba ya yin kuka gobe,

 Mai alƙawarin da ba ya kyauta ya yi zobe,

 Na yi tsaye a gun Nabiyu ko za a yi dambe,

 Nai fatar fita ga ƙangi can gobe,

  Ranar bincike hisabi da tsayawa.

552. Je ka gaya wa Manu na ba da umurni,

 Ya jira kar ya doki yaro ya yi rauni,

 Ya tsaya tsab! Ya dakata zan yi umurni,

 Ce masa Manu Baba ya ba da umurni,

Ka da a hukunta yara sai sun ƙi tsayawa.

 

553. Suna kowane iri za a rubuta,

 In dai har ana buƙatar a karanta,

 Kar a yi son kai wurin idan za a rubuta,

 Sai a bi tsarin da yaf fi sannan a kwatanta

  Harafi babba za a sa gun farawa.

 

554. Adamu Nuhu Annabawan Allah ne,

 Sa Yusuf da Yaƙuba duka dangi ne,

 Musa da Haruna tare suke zaune,

 Isah mun sani badaɗen Allah ne,

Ahmadu namu an na ƙarshen aikowa.

 

555. Manu da Mande Sani sunan manya ne,

 Shi Ummaru Ɗa yana rubutun waƙa ne,

 Shi ma Ali Bunza ya ƙware a wajen zane,

 Har ya sa mu yanzu mun kwana a zaune,

Buba Hassan da Ango sunan Hausawa.

 

556. Ladidi da Nanuwa Rakiya na nan,

 Sa muna Abu na ga ta yi daka ran nan,

 Ke kuma Binta kwashe kayanki wurin nan,

 Suna biyu Fati, A’isha mai sunan nan,

  Indo, Inno, ƙara lura da kulawa.

 

557. Sunan kowane mutum za ka rubuta,

 Ko Musa, Habibu, don za a karanta,

 Mudi, Babuga aminin Ɗantata,

 Ƙarami bai zuwa a farko a rubuta,

  Harafi babba za a fara rubutawa.

 

558. Haka sunan garuruwa sannan Bunza,

 Maikwari naf fi so a sa kafin Bunza,

 Misau Bauchi ce a Zamfara Ɗanbaza

Can Sakkwato akwai gari ana ce masa Bazza,

  Zariya ko Kano Madinar Hausawa.

 

559. Haka suna na harsuna duk a kiyaye,

 Sa lura ɗan’uwa ya zan kan ka a waye

 In za ka rubuta harsuna sa Buzaye,

 Kar ka rubuta ‘b’ haka wai buzaye,

  Harafi babba za a sa dinga kulawa.

 

560. Larabci da Hausa, Yarbanci lura,

 Fillanci Yola yai yawa in muka lura,

 Barbarci, Karekari, Babur, Cera,

 Harshen Igbo je jiha ta Anambara,

  Turanci ka sa shi harshen Turawa.

 

561. Sunaye na masu harshe haka zai zo,

 Sunan harshe da masu shi su yi zo-zo-zo,

 Farko babba ko’ina in har zai zo,

 A misalin da zai biyo duk haka zai zo,

  Hausawa da su da gungun Yarbawa.

 

562. Haka littattafai ga sunansu a lura,

 Ai azama a bar tuwo da miyar bara,

 Dokar ta gwado muhallin tun bara,

 Ƙarami bai zuwa wurin babba ku lura,

  Harafi babba can ga farkon farawa.

563. Ƙamus, Askari Risala ga rubuta,

 Ko Literature kake buƙata ka rubuta,

 Ko Culture haɗa da Language a rubuta,

 In har aka tashi za a zance a rubuta,

  Harafi babba an ka fara rubutawa.

 

564. Darusa kowane iri za a rubuta,

 Sai dokar da tai umurnin a katabta,

 Sai a rubuta babba sannan a maganta,

 Sai ƙaramin baki ka bi nai a rubuta,

  Harafi babba za a fara gabatarwa.

 

565. Nahawu da Manɗaƙi ka sa Adabi na nan,

 Kwai Shara’a sai ka sa ta Al’ada na nan,

 Lissafi da Biology, Philosophy, na nan,

 Kiwon Lafiya, Kimiyya duka sannan,

  Tarihi da Engilish ga rubutawa.

 

566. Sunan Rabbana da siffarSa dukkansu,

 Farkon kowane baƙi ga rubuta su,

 Babban an ka so a sa ga tsarin dokarsu,

 Don sauƙi ya samu sai a karanta su,

Da wakilinsu manya-manya ake sawa.

 

567. Arrahamani, Arrahimu Mujibun ne,

 Alfattahu, Alkarimu, Karimi ne,

 Arrazzaƙu, Albasiru, Alimun ne,

 Alƙahharu, Al’Azizun, Mabuwayi ne

  Allah Ya buwayi bayinSa iyawa.

 

568. Allah bai da dole can ga ayyukkanSa,

 Sannan kuma babu wanda zai iya tursasa,

 Shi ga abin da za a ce wai dolenSa,

 Sai yai niyya abin da yas so don son Sa,

  Al’adarsa bai faɗa babu cikawa.

 

569. Duk harafin da zai wakilci Ilahinmu,

 Dole a sa babba ƙa’ida ta rubutunmu,

 Doka ce ta tsara dukkan tsarinmu,

 Ba rubuta ƙanƙanin harafi ilmu,

Zai zama babba ba musu gun Hausawa.

 

570. Ga rubutun zube sakin layi na nan,

 Bayan kammalar bayani duka sannan,

 A sako ‘yar taƙar rubutu duka sannan,

 Harafin duk da zai biyo bayansa nan

  Farkonai baƙinsa babba yake zowa.

 

571. Haka sunan dukan ƙasashe a yi babba,

 Farkon sunan a zan rubuta shi da babba,

 Ita Nijeriya ƙasa ce kuma babba,

 Sai Kamarun da Chadi, Saudi ƙasa babba,

  Nijar, Ghana, China, birnin Sinawa.

 

572. Sunaye na unguwanni haka za su,

 Harafi babba za a sa a rubuta su,

 Samaru, Sabon Gari a sake rubuta su,

 Arkilla, Bello way duk mun san su,

  Tamkar Kanwuri da babba aka sa wa.

 

573. Laƙabi kowane iri sa mishi babba,

 Harafin farko zan rubuta shi da babba,

 In ƙarami ya zo wurin an yo kwaɓa,

 Duba nan ƙasan ga don kar ka yi kwaɓa,

  Cigari, Citumu, Namaiwa ga tsarawa.

 

Sauyawar Babban Baƙi Zuwa Ƙarami

 

574. Nahawun Hausa na da doka ga rubutu,

 In an bi ta sai rubutun ya karantu,

 In kuma an dagula da shirme a rubutu,

 Ba shi karantuwa ga wanda yay yi rubutu,

  Masana sun aminta ba ta sauyawa.

 

575. Sun ce can wurin rubutun sunaye,

 Nan aka sa ƙanana kan ku yana waye,

 Kar ku rubuta babba nan gun sunaye,

 Sa ƙarami gaban gaɓar Ɗan ka kiyaye,

  Ga wata ƙa’idar da za a kiyayewa.

 

576. Suna in ya zo riɓinji ga rubutu,

 Sai a rubuta yadda doka ta amintu,

 Sa muna ‘yan ƙanana don masu karatu,

 Su kuma manya-manya farko na rubutu,

  Ba asalinsa za a bi ba ga zanawa.

 

577. Farkon nan ake buƙatar a kiyaye,

 Zan saka manya-manya kar ka yi tawaye,

 In ka saka ‘yan ƙanana ka yo tawaye,

 Gun dokar da tay yi horon a kiyaye,

  Don babban baƙi a nan za shi fitowa.

 

578. Ɗanbala, Ɗanhasan, da Ɗangambo dukan su,

 Sa Ɗanladi, Ɗantanin haɗa duka jerin su,

Ɗanhauwa’u, Ɗan’amina, ga Tasalla a cikin su,

 Sa muna Ɗan’amarya duk gun tsarin su,

  Ga Ɗandatti, Ɗan’alu gun tsarawa.

 

579. Ɗanmairogo kana ga Ɗanmairiga,

 Ɗan aka so a sa ta babba, kana a sa mairiga,

 Ko mairogo duk ƙanana harafi hanga,

 Tabello, ko Tamalam, Ɗanmanga,

Ga Na’abu, Tabawa can ga ƙiyastawa.

 

580. Ka ga a nan wurin ga an samu riɓinji,

 In yunwa tai yawa ana ji har hanji,

 Dole a sake tsari idan za a yi canji,

 Na muhallin wurin rubuta riɓinji,

Tun farkonsu sun ka zo da dibiltarwa.

 

581. Ka ga a nan Bala Hassan had da su Gambo,

 Sa Ladi, Tanin, Amarya, ba gyambo,

 Hauwa’u, Amina, ran Salla sai ƙwambo,

 Sai tafiya guda-guda suna famar ƙwambo

  Datti da Ali duk ƙanana ake sa wa.

 

582. Abu da Bawa duk baƙi ba mai babba,

 Haka Bello da Manga duk ba mai babba,

 Mairogo, Mairiga duk ƙanana suke duba,

 Ba harafin da na rubuta shi a babba,

  Don farkonsu babba yaf fara tahowa.

 

583. Harafi babba kun ga nan ya gurfana,

 Ya zam ƙarami gudun rubtun a yi ɓarna,

 Doka ta hana shi babba sai dai da ƙanana

 Dole ya zo gun manya-manya ya gurfana,

  Ya zama tsito an hana masa miƙewa.

 

584. Haka doka ta ce ga tsarin nahawunmu,

 Ba laifi mu bi ta, kare mutuncinmu,

 In muka saɓa ta mu ɓata rubutunmu,

 Ma’ana za ta barkace ga masu karatunmu,

  Gun suna kaɗai abin ke bijirowa.

 

585. In ba nan ba ko’ina babba ya sauka,

 Ko a ina ake da gurbin shi ya sauka,

 Yay yi kane-kane ya zam ba ya da tamka,

 Ya bi tsarin doka, ya koma ya sha toka,

  Ƙarami bai hawansa don bai morewa.

 

586. Tilas godiya a nan gun Ɗangambo,

 Ali na Bunza godiyarsa ga Ɗangambo,

 Mu ma mun yi godiya gun Ɗangambo,

 Mun gode wa Bunza yaron Ɗangambo,

  Babban malaminmu gogan koyarwa.

 

Muhimmanci Kiyaye Babban Baƙi da Ƙarami

587. Kyawon jewaɗi a samo amfani,

 Kar a yi shawagin da ba ya da amfani,

 Ko a yi yawo kama da na shanshani,

 Bai dace ba jewaɗi ya zan ba amfani,

  Don mai jewaɗin ya zan bai taɓewa,

 

588. Sa babban baƙi akwai shi da amfani,

 Gurbi nai da an ka tanada mai amfani,

 Kai shi a can saka shi don ba ruɗani,

 Zana shi ɓaro-ɓaro cikin rubutu ba muni,

  Ga wuraren da an ka ce ba saɓawa.

 

589. In aka baddala su za a ga ruɗarwa,

 In sun barkace ka san suna rikitarwa,

 In an baddala shi mai karatu na ruɗewa

 Rubutunka ya barkace ya zan ba shawa,

  Sai ma’ana ta ƙalgame ba ta fitowa.

590. Ka ce Abu ta ƙi tuƙa tuwo sosai,

 Ga shi a yanzu ba ta toya muna ƙosai,

 Laifinta gare mu ya girmama sosai,

 Shin wai Abu ce a tarshe kamar mosai?

Ga abu sai ka ce hurar ga ta Rundawa.

 

591. Sarkin Isa ya kira taro babba,

 Duk an taru yara-yaranmu da babba

 Kowa ya taho da riga tai babba,

 Dud duka ‘yan gari guda muke ba sabba,

  Ya isa fada ganguna na cashewa.

 

592. Tanko Ba’askaren mutum ba ya da tsoro,

 Ya yo ɗamara yana buƙatar fasa taro,

 Jami’an tsaronmu sun  bayyana tsoro,

 Sun lura Tanko zarumi ba ya da tsoro,

  Ya tanko bakarsa ba mai gittawa.

 

593. Kalmomin da an ka jirge ga rubutu,

 Su za ai nazari ga tsarin na rubutu,

 A zo bayaninsu don kawai masu karatu,

 Duk kalmomin da an ka jirge ga rubutu,

‘Yan Jimmai da Jimma ne babu rabewa,

 

594. Bambancinsu ɗai guda da baƙi babba,

 Shi ke nuna ɗa guda kuma na baba,

 Bambanci uba da ɗa girmama baba,

 Ko da gani ka sani da bambanci babba,

Ɗaya ƙaramin baƙi ya mamaye farawa.

 

 

595. Abu, da Isa, Tanko sunaye ne su,

 In an zo aji na suna a saka su,

 Kar a yi wasa a harha]a su a dangin su,

 Sunaye na mutum, gari, duka tsarin su,

  Wasali ko baƙin su manya aka sa wa.

 

596. Abu, da isa, da tanko ba suna ne ba,

 Ba a saka su inda duk bai  dace ba,

 Don ba a zana harrufansu da manya ba,

 In dai ƙaramin haraf ya zo ba saɓa ba,

  Tun farkon gaɓarsu nan aka ganewa.

 

597. In ba don shigan baƙaƙe manya ba,

 Ko doka da laffuzan maudu’i ba,

 Ba za ka ƙididdige  ka ce ka gane ba,

 Ba lallai ne a gane tsarin bagiren ba,

  Wa zai rarrabe can ga karantawa?

 

598. Saura je ka tambi malam ya gaya ma,

 Ya gaya ma ya ƙara haske ya faɗa ma,

 Ya samu misalai kamar ɗari sai ya faɗa ma,

 Sa himma haɗa da ƙwazo bari hamma,

  Kar fa ka daƙile ka zam mai ruɗewa.

Post a Comment

0 Comments