Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
599. Shi ƙaramin baƙi daɗai bai rikitarwa,
Domin kodayaushe
shi ne aka sawa,
Da yawa mai
kurenmu shi yaka zanawa,
Ba ya rikitar da
mai rubutun Hausawa,
In aka zo ga ƙa’ida gun zanawa.
600. Duk a wurin da ba baƙi babba ake ba,
Ko ka sa shi ka ga
ba zai riba ba,
Don ba ka so sa shi
inda yad dace ba,
Ba shi zuwa wurin
da nashi ba ne ba,
Ƙaramin za a sa wurin
don dacewa.
601. Kowane aikatau baƙi ƙarami zai zo,
Matuƙar dai cikin rubutu ne
yaz zo,
Amma in ya zo a
farko zo-zo-zo,
Za a rubuta babba,
don farko yaz zo,
Yanka yanke-yanke
ko yayyankewa.
602. Can ga sifa da ‘yan ƙanana ake zane,
Su ma dai kamar
hukunci aiki ne,
Ƙarami za a sa shi
babba yana zaune,
Can bagirensa ko a
farko yin zane,
Dogo ko baƙi, fari mai haskawa.
603. Haka doka ta ce wakilan sunaye,
Sai a rubuta ‘yan ƙanana kai waye,
Kar a sake sanya
manya dogaye,
Na baƙi ko wasal a kowane
halaye,
Duk harufa ƙanana za a rubutawa.
604. Tamkar ya
buwaya, ta shiga ɗakinta,
Ko kuma ni ka ba shi, shi ke aurenta,
Sannan wa zai biya sadakin kanwata?
An ce ku zo batun neman mata,
To sun gayyace ku kun kasa fitowa.
605. Matuƙar ya fito ga sunan mabuwayi,
Za a saka shi
babba, don samun sauyi,
Ba a rubuta ƙanƙanin harafi, bai yi,
Tsari ne na ƙa’idar rubutu a yi
koyi,
Babba ake saka shi don wanwancewa.
606. Bayan neni ko’ina ɗan yaro ne,
Sa ƙaramin baƙi, wakilin ko wa ne,
Ba a saka shi
babba, mun san laifi ne,
Ƙarami ko da yaushe in
dai harafi ne,
Bai rigima da
babba can gun zanawa.
607. In waƙafi ya zo a bayansa a sa shi,
Ai nazarin iri na
kalmar kan sa shi,
Domin babba na da
gurbinsa na sa shi
In dai ba wurin
haraf babba ba sa shi,
Ko da mai ruwa a
nan babu rabewa.
608. Haka bayan baka alamar buɗewa,
Sa ƙarami ka bar batun duk
ruɗewa,
Sai ka bi yadda ƙa’ida ke tsarawa,
Har ma can a dab
da ƙarshen zanawa,
Da rufewa ƙanana duk za a sakawa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.