Tarihin Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato

    Ahmadu Ibrahim Bello, Sardaunan Sokoto wanda aka yi wa lakabi da Sir Ahmadu Bello , dan Najeriya ne mai ra’ayin mazan jiya wanda ya mulkin Arewacin Najeriya ta hanyar samun ‘yancin kai a shekarar 1960 kuma ya zama Firimiya ta farko kuma tilo daga 1954 har zuwa kisan gillar da aka yi masa a shekarar 1966 , inda ya mamaye harkokin kasa sama da shekaru goma.

    Salsalarsa

    Kakansa shi ne sarkin Musulmi Bello, wanda na daya daga cikin wadanda suka kafa daular Sokoto, kuma dane ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo.

    Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ɗan ƙabilar Fulani ne, kuma shi jika ne a wajen Shehu Mujadaddadi. Sunan mahaifinsa Ibrahim Bello. Da kansa ya ce, “Mahaifina ɗan Abubakar ne, da aka fi sani da Atiku na Raɓah, wanda shi ne sarkin Musulmi na bakwai. Ya yi mulkinsa na tsawon shekaru huɗu (4) daga 1873. Mahaifinsa kuma shi ne Sultan Bello ɗan Shehu Usman Ɗanfodiye Mujadaddadi. Bello, wanda ya gaji jagoranci Musulunci a bayan rasuwar mahaifinsa kakan-kakana ne”. (Ahmadu, 1961).

    Saboda haka kenan, Sir Ahmadu Bello ɗan Ibrahim ne, shi kuma Ibrahim ɗan Abubakar Atiku na Raɓah, shi kuma ɗan Sultan Bello shi kuma ɗan Mujadaddadi Shehu Usman. Dan haka tsakaninsa da Shehu mujadaddadi rawani ko hula uku ce kacal. Wato mutane uku ne a tsakaninsa da Shehu mujadaddadi.

    Ibrahim Bello wanda shi ne mahaifin Sir Ahmadu Bello ya kasance mutum ne jarumi wanda saboda jarumtakarsa wani shahararren mawaƙi na lokacinsa mai suna Zamnu ya yi masa kirari da Mai ƙafon karo a bayan da ya gwabza da Turawan mulkin mallaka iya ƙarfinsa. Sunan mahaifiyar Sir Ahmadu Bello Maimunatu wanda aka fi sani da Mamu (Paden, 1986).

    An haifi marigayi Sir Ahmadu Bello a garin Rabah dake cikin lardin Sakkwato a Ranar 12 Ga Watan Yuni shekara ta 1910, kuma dan sarauta ne jinin shehu dan Fodio, wanda ya kafa daular fulani. Da yake shekara 16 da haihuwa bayan ya sami iliminsa na makarantar lardi ta Sakkwato, sai wuce zuwa kwalejin horon malamai ta katsi
    Tarihin Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato
    Mai rubutawa 
    Mujitaba Mainasara Gwandu
    mujitabamainasara@gmail.com
    09162624242
    Ɗalibin nazarin harsunan Nigeria a Jami'ar Usman Dan fodiyo dake nam sakkwato.
       Rana '01-10-2023

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.