Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne Wasan Kwaikwayo?

Wasan kwaikwayo na Hausa, fage ne da ya taɓo dukkan harkokin da suka shafi rayuwar ɗan’Adam ta yau da kullum, domin yana bayyana wa mai kallo ko mai sauraro ko karatu, hanyoyin rayuwar jama’a ta fuskar sana’o’insu. Masana adabin Hausa da suka yi nazari akan wasan kwaikwayo sun yi ƙoƙari sun fito da ma’anar wasan kwaikwayo.

Ɗangambo (1984) ya ce “Wasa ne da ake ginashi don kwaikwayon wani labari ko wata matsala ta rayuwar da ake son nusarwa ga jama’a cikin sifar yaƙini ko kuma a rubutashi”. Yahaya, (1978) ya bayyana wasan kwaikwayo da cewa; “Wasan kwaikwayon na nuni ne da aikata wani abu musamman a dandali domin yasa nishaɗi ga masu kallo ko ya raunanar masu da zuciya”.

Danna nan domin samun cikakkiyar takardar.

www.amsoshi.com


Post a Comment

0 Comments