Jamilu Shuaibu Usman
Ɗalibin Digiri na Biyu,
Fannin Harshen Hausa
Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar
Bayero, Kano
Imel:
jamilshuaib659@gmail.com
08020538613
Tsakure
Manufar wannan binciken shi ne, domin, a gano kalmomin saye da masu magungunan Islamic kyamis ke amfani da su wajen tallata maganinsu. tare da duba karɓuwar kalmomin sayen a gun masu sayen magungunan. Saboda, kiraye-kiraye da malaman addini suka yi. A cikin binciken an gano, Ire-iren saye da suke amfani da su, da ma'anarsu a gun masu tallan da masu kallon tallan. An zaɓi amfani da hanyar bi-sharhi (Qualitative research) a sigar bi-bayani (descriptive) don kawo sayen da ma'anarsu, domin taskace su ga ma'abota ilimi don nazarta. An kalli bidiyoyin masu tallan magungunan da hira da masu tallan magungunan guda (20). Domin, tantance ma'anonin kalmomin sayen da suke amfani da su wajen talla.
An gano
kalmomi da suke amfani da su da ma'anarsu, kamar saye a sunayen nau'o'in cutuka
da magunguna da sunayen sassan jikin ɗan adam. Muhimmancin samuwar irin kalmomin sayen nan a fagen
kasuwanci na magungunan gargajiya da ake tallansu a shafin tiktok na dayawa,
domin suna isar da saƙo cikin hikima da kinaya
da suka dace da al' adar Hausawa da addinin musulunci da zamantakewar al'umma,
domin kiyaye tarbiyyar matasan wannan zamani, da ke ta'ammali da kafofin sada
zumunta na zamani ciki har da na tiktok.
An ɗora wannan bincike a kan
ra'i na zantuka da ƙalailaicewa (Critical
Discourse Analysis) wanda ya nuna ana nazarin harshe da ma'anar da kalmomin
ke ɗauke da su wanda al'umma ta aminta da su. Suke kuma amfani da
su.
Haƙiƙa, kiraye-kirayen malaman
addini da suka sha yi, an samu nasara. Domin, samuwar irin kalmomin saye a
fagen tallata magunguna islamik na da matukar muhimmanci, don kare tarbiyya da
kunya da Bahushe ya gada iyaye da kakanni. Ga shi kuma za su dace da kauce wa
yasasshen zance wanda ya saɓa wa addinin islama.
1.0
Gabatarwa
A yau,
kafofin sada zumunta na zamani sun taka muhimmiyar rawa a rayuwar ɗan Adam, musamman ta
hanyar kafafen sada zumunta irin su Tiktok da Fesbuk da Instagiram. A Najeriya,
Tiktok ya zama wata hanya ta yaɗa saƙo cikin sauƙi da sauri. Ɗaya daga cikin rukunin masu amfani da wannan kafa akwai masu
tallata magungunan gargajiya da suke kiran kansu Islamik Kyamis. Su ma sun
samar da kalmomin saye, wato kalmomin da aka ƙirƙira ko aka samar da ma’anarsu da nufin sakaya ma'anar abu don ya
dace da kunya ta Bahaushe. Wasu daga cikin kalmomin na asali ne daga Hausa,
wasu daga Larabci, wasu kuma daga Ingilishi.
Kalmomin
saye dama can akwai su a cikin tsarin zamantakewar Bahaushe. Akwai masana da
dama da suka yi bincike a kansa. Sai dai hannuna mai nazari bai kai, kan wanda
ya yi a kan masu maganin gargajiya da suke talla a tiktok ba. Sai hakan ya ja
hankalin mai nazari wajen gudanar da wannan nazarin.
A cikin
wannan bincike, an tattara faifayen bidiyo ashirin (20) na masu tallan
magungunan Islamik Kyamis a Tiktok, inda aka zaƙulo
kalmomin saye da suke amfani da su wajen tallace-tallacen nasu tare da
tattaunawa da wasu daga masu tallan maganin da masu kallon tallace-tallacen. An
gano cewa daga cikin irin waɗannan kalmomi, akwai waɗanda ke da ma’ana a Hausa, sannan akwai waɗanda aka jirkita tsarin
furuci ko aka sauya ma’anarsu. Wannan dalili ne ya sa masu sana’ar magungunan
Islamic Kyamis, suke amfani da harshen Hausa wajen tallata kayansu, domin isar
da saƙo cikin sauƙi. Haƙiƙa, kalmomin saye suna taimakawa wajen kauce wa amfani da
kalmomin batsa, wanda kan iya shafar tarbiyyar matasa da yara da ke kallon waɗannan
tallace-tallace.Wannan nazarin, ya mayar da hankali ne kan Ire-iren saye na
masu tallan magani a tiktok, musamman saye na sassan jikin ɗan adam da cutuka da
magungunansu.
1.1.
Manufar Bincike
Manufar
wannan bincike ita ce, domin taskace kalmomin saye da masu tallace-tallace
magungunan gargajiya na Hausa da ke kiran kansu na Islamik Kyamis ke yi a
shafin sadarwa na tiktok. Suna amfani da Ire-iren kalmomin sayen ne, domin
sakaya ma'anar cuta ko sassan jikin ɗan'adam, da kauce wa yin batsa da yasassun zantuka. Saboda,
akwai yara masu ƙananan shekaru da ke
bibiyar tallace-tallacensu a shafin sadarwar na Tiktok. Wannan na daga cikin
irin ɗabi'ar
da Bahaushe ke da ita dama can, na amfani da saye a kan al'amuran
zamantakewarsa na rayuwa.
1.2
Dalilin Bincike
Dalilin
wannan bincike na da nasaba da yadda Hausawa masu amfani da shafin tiktok ke
samar da kalmomin saye, domin cinikayya ko kasuwanci da sauran al'amuran
rayuwa. Bibiyar irin waɗannan kalmomin da taskace su, domin manazarta da ɗaliban ilimi su fahimci
irin saye da harshen Hausa ke samarwa a fannin kasuwanci da sada zumunta a
shafin sada zumunta na tiktok, na da matiƙar alfanu. A cikin
nazarin, an ware nau'o'in da sayen da wannan nazari ya fi karkata a kai. Su ne,
na masu tallan magungunan gargajiya da suke kiran kansu na Islamik Kyamis a
tiktok.
1.3
Ra'in Bincike
An ɗora wannan binciken a kan
ra'in Zantuka da ƙalailaicewa (Critical
Discourse Analysis) Wannan ra'i wanda ya samar da shi, shi ne Fairclough,
(1995) inda Dirjk, (2008) Ya sake goyi bayan ra'in. Ra'i ne da yake nazarin
harshen da al'umma ke amfani da shi, da nazartar zamantakewarsu. Ra'in na
kallon al’umma ce ke tsara yadda ake amfani da harshensu. Haka kuma, harshe
yana tasiri wajen tsara mu’amala tsakanin rukunin mutane na wannan al'umma da
lura da akidu da halayensu, wanda suke amfani da harshensu a yanayin da ya dace
da su.
Ra'in
zantuka da ƙalailaicewa(Critical Discourse Analysis). Na nuna wasu rukuni
ko ƙungiyoyi ne ke da ikon fayyace irin harshen da ya dace da
ma’anoni da ƙa’idojin da za su iya bi, idan za a yi magana a wannan rukunin
al'ummar. (CDA) Ya fayyace harshe na ɗauke da ɓoyayyun ma'anoni da wasu daga cikin al'ummar da ke magana da
wannan harshen ne kawai ke iya fahimtarsu da amfani da su a tsakaninsu bisa
imani da suke da shi a kan wani addini da suka aminta da shi, waɗanda kan bayyana kamar
al’ada ce ko abin da aka saba da shi. Ra'in Zantuka da Ƙalailaicewa, ra'i ne da ke cewa ma’ana ta dogara da mahallin da
ake ciki. Ba za a iya fahimtar zance gabaɗaya ba, sai an yi la’akari da yanayin da al’ada da addini da
zamantakewar al’umma. Kuma Ra'in zantuka da ƙalailaicewa
(Critical Discourse Analysis). Na kallon harshe na iya ƙarfafa aƙidun da ke mafiya rinjaye
a tsakanin al’umma.To ashe ke nan, wannan bincike ya dace da wannan ra'in,
domin dukkansu suna kallon yadda rukunin wata al'umma ke da tasiri na samar da
kalmomi da za su iya amfani da su, domin ƙarfafa
al'adu ko addini ko kasuwanci a tsakaninsu.
1.4.
Ma'anar Harshe
Chomsky,
(2006). Ya bayyana harshe da cewa shi ne madubin zuciya da yake bayyana tunanin
da yake cikin zuciyar ɗan adam. A ra'ayin Bagari, (1986). "Harshe hanyar sadarwa
ce, da ake amfani da shi, wajen sadarwa ta hanyoyi biyu. Wato ko dai a furta
magana da baki mutum ya ji da kunnensa ya fahimta ko kuma a rubuta" CNHN,
(2006). An ba da ma'anar harshe da: "Hanyar magana tsakanin al'umma
iri ɗaya"
Adamu,
(2025). Ya yi bayani cewa"Harshen Hausa a yau, yana baza kafasiti
(Capacity) a kafofin sada zumunta na zamani a tsakanin matasa tun da su ne suka
fiye amfani da shafin" Abdallah, (2025). Ya ƙara da cewa da yawa-yawan kalmomin da ake amfani da su a
soshiyal midiya na batsa ne, Ko na ɓatanci ne ko na iskanci ne! Saboda haka, sai suka zama kamar
zaurance ne, wato kalma ce za a yi amfani da ita, ga muhallinta an santa, amma
kuma an canza mata wannan muhallin an kai ta wani muhalli na daban, wanda yake
fitar da wata ma'ana ta daban da aka santa. Wanda sai waɗanda suka san wannan
ma'anar za su gane ta. Kamar yanzu, wata kalma da ake amfani da ita a soshiyal
midiya wato kafaciti (capacity) yana baza kafaciti. Me kafaciti yake nufi?
Kafaciti tana nufin isa ko cikowa ko daidaito da abun da za ka ɗauka. Ko a ce daidai ruwa
daidai tsaki abin da kafaciti take nufi ke nan. To amma yanzu, an juya ma'anar
kalmar ko zamananci ne? Sai a ce yarinyar nan tana da kafaciti, wato yarinyar
nan tana da kyau ko tana da wani aji ko wani abu. Ashe ke nan, kalmar kafaciti
da aka santa da daidai ruwa daidai tsaki an canja ta ta zamo wani abu. Ya ƙara da cewa masu amfani da soshiyal midiya ne ke ingiza samar da
irin wannan kalmomin. Kamar misalin kalmar marke, batsa ce. Kamar zarmalulu ita
ma batsa ce. Amma yanzu an fara amfani da ita a matsayin kalmar yau da
kullum".
A
takaice, harshe hanya ce ta isar da saƙon da ke cikin rai zuwa
ga mai sauraro ko mai karantawa da nufin isar da shi saƙon cikin sauƙi.
1.4. 1.
Amfanin Shafin Sada Zumunta na Tiktok
Kaye,
V, da Chen, X. da Zeng, J. (2022) sun ayyana manhajar tiktok ta fuskar
kasuwanci da tattalin arziki da cewa " Ya zama wata kasuwar intanet inda
ake tallata kaya da kasuwanci da kuma samar da kuɗaɗe ga masu kirkira (content creators).
Omar,
B. da Dequan, W. (2020) Sun kalli manhajar Tiktok ta fuskar ilimi da irin
ma'anar da suka ba shi da cewa masana ilimi suna ganin" TikTok ya zama
wata hanya da ake amfani da ita wajen ilimin zamani, musamman wajen jan
hankalin ɗalibai ta hanyar bidiyoyi gajeru. Ana amfani da shi wajen koyar
da harsuna da kimiyya da ma al’adu. "
Ashe ke
nan, shafin sada zumunta na Tiktok na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki kamar yadda masanan nan suka kawo a matsayin
(content creator) Haka kuma, ya taimaka wa masu ilmantarwa damar samar da
gajerun faifayen bidiyo don koyar da rawa ko azancin magana ko samar da sabbin
kalmomi a tsakanin matasa da tallan magunguna da sauran kayan buƙatu na ɗan adam. Lalle, kafar sadarwa ta Tiktok ta zama sha kudum ta
fuskar alfanunta ga matasa na duniya ma ba Hausawa zalla ba.
1.5.
Mene ne Saye?
Azare
da Almajir, (2024)"Saye hanya ce da ake amfani da wasu kalmomi a maye
gurbin waɗanda
ake ganin suna ɗauke da maganganu na batsa ko waɗanda za su iya haifar da matsala, domin daidaita tasirin magana
ko kauce wa jin kunya." Shi da Sheng (2011) Haka kuma, saye hanya ce da
ake musanya wata magana ko furuci da ake ganin za ta iya haifar da ɓatanci ko wani abu na
rashin jin daɗi. Al'umma daban daban na amfani da saye wajen rage kaifin
magana mai nauyi zuwa mai sauƙi da ƙarancin ɓatanci ga mai sauraro. A taƙaice, Saye wata hanya ce
da ake amfani da ita wajen musanya wani bayani na ɓatanci ko cin zarafi ko
batsa zuwa waɗanda ake ganin ba sa ɗauke da hakan. Za a iya samun wannan sauyin a kalma ko a yankin
jumla ko jumla gabaɗayanta. Ana amfani da saye ne don kauce wa jin kunyar kai ko
sanya wani jin kunya. Wasu masana na ganin cewa akwai yanayin da ake amfani da
saye wajen amfani da harshe don cimma wata manufa" Azare. Y. M. da
Almajir, T. S. (2024). Saye salo ne da masu magungunan gargajiya wanda suke
kiran kansu da na Islamic kyamis ke amfani da shi wajen tallata magunguna
kala-kala a shafukan sada zumunta na zamani musamman tiktok, don jan hankalin
abokan kasuwancinsu da rage wa wasu kalmomin nauyin tasirin da za a iya ji garangatsau!
1.5.1.
Ire-iren Saye
Azare
da Almajir (2024) sun kawo ire-iren saye guda huɗu a cikin littafinsu. Amma, za a yi bayaninsu. Sai dai guda biyu
ne, suka fi alaƙantuwa ta kai tsaye da nazarin da ake yi.
« Saye na Mutuwa : A al'umma da dama mutuwa aba ce da ake fargaba
da jin tsoro da kuma rashin jin daɗin ta. Wannan ne ya sa akwai kalmomin saye da ake amfani da su
wajen bayyana mutuwa. Al'ummar Hausawa su ma suna da nasu kalmomin saye da suke
amfani da su wajen bayyana mutuwa: Misali.
· Komawa ga Allah.
· Rasuwa.
· Riga mu gidan gaskiya.
· Rasa rai.
« Saye na kunya: Saye na kunya na nufin ƙin faɗar wani abu ko wani jinsi ko wani adadi ko hali ko yanayi da
inkiyarsa ta asali(Lawal, 2019) Kunya na ɗaya daga cikin abubuwan da suke haifar da samuwar saye a
tsakanin al'ummar Hausawa. A tsarin zamantakewar Hausawa akwai kunya tsakanin
miji da mata da kunyar ɗan fari wanda shi ne ke haifar da samuwar saye ta hanyar ƙin kiran suna a maye gurbinsa da wani abu. Misali:
· Shi.
· Ita.
· Ɗan nan.
· 'Yar nan.
· Ɗan fari.
· ' Yar fari.
· Maigida/Malam (miji)
· Uwargida/mai ɗakina/mai ɗakin gabas. (mata)
Akwai
kunya ta faɗin
sunan jinin haila da mata suke yi wata-wata. Ana saye wannan jinin da kalmomi
irin su al'ada ko fashin salla ko baƙo da sauransu. Haka kuma,
idan mace ta tsallake wata ba ta ga baƙonta ba, wannan na nuna
cewa ta samu ciki. Amma saboda kunya ta Bahaushe yana sakaye kalmar yin ciki ya
yi amfani da kalmomi kamar :
· Ɓatan wata (ma'ana ba ta ga baƙonta
ba)
· Juna biyu.
Idan ta
haihu, shi ma ana saye ana cewa:
· Ta sauka.
· An samu kai.
« Saye na halittar jiki: Akwai wasu ɓangarori na jiki da
Bahaushe kan saye sunansu na asali saboda nauyin faɗarsu a baki kai tsaye,
inda ake ɓoye su da kalmomi kamar: matanci ma'anarta farjin mace da ƙirji ana nufin nonuwan da ke ƙirjin
mace da maƙarfafa na nufin azzakari na namiji da mazaunai na nufin ɗuwawu da sauransu.
« Saye na addini: Kalmomi ne da ake saye su saboda girmamawa da
tsoron Allah (S. W. T) da kuma martaba addini. Misalin irin wannan saye sun haɗa da wafati na da ma'anar
mutuwa da riga mu gidan gaskiya na da ma'anar mutuwa ita ma da marigayi na da
ma'anar namiji wanda ya mutu, idan kuwa mace ce sai a ce marigayya da sauransu.
Kamar
yadda muka ga ma'anar saye da Ire-irensa, za a fahimci, saye hanya ce da
Bahaushe kan yi amfani da wasu kalmomi ko gajeruwar jumla domin ɓoye girman abu don kauce
wa jin kunya da sakin zance don mutunta kai da mai sauraron saƙonsa ko karanta saƙonsa.
A cikin
wannan nazarin saye na kalmomin masu magungunan gargajiya na Hausa wanda suke
kiran kansu da na Islamik kyamis aka duba. Kamar: Saye na halittar jiki da saye
na sunayen cutuka da magungunansu.
1.6. Saye na Masu Tallan
Magungunan Gargajiya da ke kiran kansu da na Islamik kyamis a Tiktok
Saye na
masu magungunan gargajiya da ke kiran kansu na islamik kyamis da ke
tallace-tallace a tiktok, a wannan nazari an kasa su gida biyu ne. Na halittar
jiki da ma'anarsu sai na cutuka da ma'anoninsu.
1.6.1.
Ire-iren saye na halittar jiki da ma'anarsu:
A
wannan jadawalin an kawo wasu daga cikin kalmomin da masu tallan magunguna na
gargajiya suke amfani da su a shafin sada zumunta na tiktok da suke da saye na
halittar jikin ɗan'adam da ma'anoninsu.
|
Saye
na Halittar Jiki. |
Ma'anarsa |
|
Zarmalulu |
Azzakari. |
|
Gaba |
Farjin
mace ko na namiji |
|
Ƙulaƙulai |
Nonon ƙirjin mace |
|
Inzali. |
Fitar
maniyyi. |
|
Kusanta. |
Saduwar
aure tsakanin ma'aurata. |
|
Mu'amala |
Saduwar
aure tsakanin ma'aurata. |
|
Kawowa |
fitar
maniyyi daga jikin mutum. |
|
Halitta |
Al'
aurar Namiji ko mace. |
1.6.2. Saye na Cutuka da
magungunansu:
A wannan jadawalin kuwa,
saye ne da masu tallan magungunan gargajiya da ke talla a shafin sada zumunta
na tiktok, da ke amfani da su a kan wasu cutuka da magungunansu da kuma
ma'anoninsu.
|
Saye na Cutuka da
magunguna. |
Ma'anarsu. |
|
Saurin biyan buƙata |
Saurin fitar da
maniyyi. Nau'in cutar basir ce ko sanyi ga namiji. |
|
Ƙanƙancewar gaba |
Azzakarin namiji ya
zamo ƙarami saboda cutar sanyi ko basir ko Istimna'i. |
|
Turaren gaba |
Nau'in haɗin magani ne da ke
matse farjin mace. |
|
Ƙetara |
Ciwan sanyi kowane iri.
Kamar sanyin ƙashi. |
|
Bushewa |
ɗaukewar sha'awa ko rashin ni'ima ga mace. |
|
Saurin inzali. Kinin
saurin kawowa ne. |
Saurin fitar da maniyyi
saboda cutar sanyi da basir ga namiji. |
|
Fitar baya. |
Nau'in ciwan basir mai
fitar da jini da zazzago da duburar mara lafiya. |
|
Fulasko/Sinamaki |
nau'in sinadari ne da
ke wanke ƙwaƙwalwar mutum da hanyoyin jijiya na jikin mutum. |
|
Rashin kuzari |
Rashin miƙewar al'aurar namiji yayin mu'amalar aure. |
|
Noƙewar gaba |
Rashin miƙewar al'aurar ɗa namiji. |
|
Istimna'i |
Cuta ce wannan da ake
kamuwa da ita, ta hanyar Wasa da gaba ko amfani da wani abu don kawar da
sha'awa kamar 'yar tsana ko wani abu mai jijjiga da sauransu. |
Kammalawa
Harshen
Hausa ya samu gagarumin cigaba a kafafen sada zumunta na zamani fiye da sauran
tsarekunsa na cikin gida Nijeriya kamar: Yarabanci da inyamuranci da sauransu.
Saboda yawan amfani da ake yi da shi wajen sada zumunta da kasuwanci da sauran
al'amuran yau da gobe a tsakani matasa da sauran al'umma. Hakan ta sa, ya samu
saye a fannin kasuwanci na magungunan gargajiya da ake tallansu a shafin
tiktok. Wannan takarda ta yi duba da irin saye na kalmomin da masu magungunan
gargajiya suke amfani da su. Saye na masu magungunan gargajiya na da matuƙar amfani da muhimmanci, domin kinaya ce da Bahaushe yake yi wa
wasu kalmomi, don kauce wa amfani da kalmomin batsa da ke buƙatar sakayawa ko kunya domin mutunta kai. Sannan, da kiyaye
tarbiyyar matasa da ke amfani da shafin sada zumunta na tiktok da kuma kiyaye
al'ada da umarnin da addinin islama ya yi, na a faɗi alkairi ko a yi shiru.
Manazarta
Adamu,
A. U. (2025). Hira da sashen Hausa na DW [interview].
Facebook. https://www.facebook.com/share/v/1AwLRAzBp2/
Azare,
Y. M da Almajir, S. T. (Eds). (2024). Littafin Karatu Don Nazarin Ilmin
Ma'ana a Hausa. Jami'ar Bayero Kano.
Bagari,
D. M. (1986). Bayanin Hausa: Jagora ga mai Koyan Ilimin Harshe.
Rabat, Moroc: Impremeries: El'Ma'arif Aljadida.
Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya. (2006). Ƙamusun Hausa na Jami'ar
Bayero Kano. Ahmadu Bello University, Press.
Chomsky,
N. (2006). Language and Mind. (3rd ed.). Cambridge University
Press.
Fairclough,
N. (1995). Critical Dscourse Analysis: The critical study of
language. London: Longman.
Kaye,
D. B. V., Chen, X., & Zeng, J. (2022). TikTok: Creativity and
culture in short video. polity Press.
Lawal,
N. (2019). Sayen Kunya a Tsarin Zaman Hausawa. Algaita, Vol 12 No
2.Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero, Kano.
Omar, B., & Dequan,
W. (2020). Watch, share or create: The influence of personality traits and user
motivations on TikTok mobile video usage. International Journal of Interactive
Mobile Technologies, 14(4), 121–137.
Shi, Y. da Sheng, J.
(2011). The Role of Metonymy in the Formation of Euphemism in Chinese and
English. Journal of Sustainable Development, 8(5)
Van Dijk, T. A. (2008). Discourse and power. New York: Palgrave Macmillan
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.