Muhimmancin Ingantaccen Shugabanci A Ƙasar Hausa A Wannan Zamani: Darussan da Suka Kamata a Koya Daga Usul Al-Siyasa

    An Gabatar Da Wannan Takarda a Babban Taron Ƙara wa Juna Ilimi Na Shekara-Shekara Wanda Gidan Sarautar Dallazawa ke Gudanarwa Ƙarƙashin Inuwar Reshen Matasa na Zuri’ar Malam Ummarun Dallaje, a Babban Ɗakin Taro na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina, a Ranar 02 ga Watan Oktoba, 2022

    Muhimmancin Ingantaccen Shugabanci A Ƙasar Hausa A Wannan Zamani: Darussan da Suka Kamata a Koya Daga Usul Al-Siyasa

    Daga

    Bashir Aliyu Sallau, Ph. D.
    (Sarkin Askar Yariman Katsina)
    Farfesan Nazarin Al’adun Hausawa
    Sashen Koyar da Hausa
    Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dutsin-ma
    Jihar Katsina-Tarayyar Nijeriya

    Gabatarwa

    Ɗalibai da manazarta da masana tarihin Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo sun bayyana cewa, akwai manyan dalilai uku ko huɗu da suka haifar da wannan jihadi, waɗanda suka haɗa da farkar da al’ummar Musulmi bauta wa Allah Shi kaɗai ba tare da haɗa Shi da wani ba. ‘Yanto talakawa Fulani da Hausawa daga mulkin mallakar sarakunan ƙasar Hausa. Magance matsalar cin hanci da rashawa da ƙwace da al’ummar ƙasar Hausa suke fuskanta daga sarakuna da wakilansu. Sannan kuma da magance matsalar cin mutunci da tozartawa da aikin dole da al’ummar ƙasar Hausa suke fuskanta a wancan lokaci. Dangane da haka, an gudanar da nazarce-nazarce da rubuce-rubuce a kan waɗannan dalilai da yadda aka gudanar da jihadin da kafuwar Daular Musulunci ta Sakkwato, wadda ta mamaye dukkan ƙasar Hausa da wasu maƙwabtanta. Sakamakon samun nasarar kafa wannan daula, shugabannin wannan jihadi sun ba da tutoci ga wasu mabiyansu waɗanda aka yi wannan yaƙi na jihadi da su, don su tafi masarautunsu a sassan ƙasar Hausa da maƙwabta domin su yaƙe su don kafa mulki na adalci da yin biyayya ga koyarwar Alƙur’ani da Sunnar Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi. Daga cikin waɗannan mabiya, akwai Malam Ummarun Dallaje da Malam Ummarun Dumyawa da Malam Na’Alhaji waɗanda suka je Sakkwato don karɓo tutar aiwatar da jihadi a ƙasar Katsina. Daga ƙarshe saboda wasu dalilai, Malam Ummarun Dallaje ne ya sami nasarar zama Sarkin Katsina. Kafin ya baro Sakkwato, sai Malam Ummarun Dallaje ya roƙi Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rubuta ma shi wata maƙala wadda za ta taimaka ma shi gudanar da mulki bisa adalci da koyarwar Alƙur’ani Maigirma da kuma sunnar Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi. Sarkin Musulmi ya amince da bukatar Malam Ummarun Dallaje kan rubuta masa maƙala wadda ya sanya wa sunan Usul al-siyasa, ma’ana, matakan gudanar da ingantaccen shugabanci na adalci. Wannan maƙala ta ƙunshi ayoyin Alƙur’ani Maigirma, da ingantattun hidisan Annabi da fahimtar malamai kan yadda za a gudanar da ingantaccen shugabanci ga al’umma. Dangane da haka, maƙasudin wannan takarda shi ne, ta dubi yadda shugabanci yake a ƙasar Hausa tun asali kafin shugowar wasu baƙi musamman Turawan Mulkin Mallaka waɗanda suka karɓe mulkin ƙasar Hausa daga sarakuna suka kawo mulkin da ya haifar da tsarin siyasar zamani irin ta Turawa. Daga nan ta yi waiwaye don nazarin maƙalar Usul al-siyasa dangane da ire-iren abubuwan da suka ƙunshi ingantaccen shugabanci, wato shugabanci wanda zai ba kowa haƙƙinsa tare da kare mutuncinsa da lafiyarsa da dukiyarsa da ta iyalansa, musamman yadda aka fito da su cikin wannan maƙala, don a tunatar da shugabannin wannan zamani da waɗanda ake shugabanta ire-iren darussan da suka kamata su yi koyi da su don gudanar da ingantaccen shugabanci a ƙasar Hausa a wannan zamani da Turawa suka kawo tsarin siyasa irin ta ƙasashensu.

    An ɗauki ƙasar Hausa a wannan nazari saboda kasancewarta ƙasar da tun kafin shigowar Turawan Mulkin Mallaka take da ingantaccen tsari na shugabanci da zamantakewa da addini da hanyoyin tattalin arziki fiye da sauran sassan da aka haɗa aka yi Tarayyar Nijeriya ta yau. Matuƙar an sami ingantaccen shugabanci a ƙasar Hausa a wannan zamani zai zama abin koyi ga sauran sassan da suke maƙwabtaka ta kusa ko ta nesa da ƙasar Hausa a Tarayyar Nijeriya.

    Waiwaye kan Ƙasar Hausa Kafin Shigowar Musulunci da Jihadin Shehu Ɗanfodiyo

    Masana da manazarta da ɗalibai kan tarihi da al’adu da zamantakewar Hausawa irin su (Alhassan, 1981:1) da Ibrahim, (1982:1) da (Birnin-Tudu, 2002:11-12) sun yi cikakkun bayanai a kan farfajiyar ƙasar Hausa, mutanenta da yanaye-yanayen ƙasar. A taƙaice, a yau, a iya cewa, ƙasar Hausa tana shimfiɗe a shiyyar Sudan ta tsakiya. A tsari na gargajiya ta haɗa da ƙasashen sarakunan Katsina da Kano da Daura da Zazzau (idan aka ɗebe kudancin Zazzau) da Sakkwato da Gusau da Anka da Kabin Argungu da Gwandu da Birnin Kabi da Gwandu da Gumel da Haɗejiya a Nijeriya ta Arewa, da kuma Ƙwanni da Maraɗi da Tassawa da ƙasar Arawa a Dogon-Dutsi a Kudancin Jamhuriyar Nijar da kuma wasu Arawa a Kangiwa ta Jihar Kabi a Arewacin Nijeriya da sauransu.

    A da can kafin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da shigowar Turawan Mulkin Mallaka, ƙasar Hausa rarrabe take, don kuwa kowane sarki yana cin gashin kansa, babu wata dangantaka tsakaninsu sai ta zumunci da kasuwanci da fatauci ko yaƙe-yaƙe don ƙarin mallakar ƙasa ko kamen bayi. Sakamakon jihadi ne ya haɗa ƙasar Hausa wuri ɗaya ƙarƙashin ikon Sarkin Musulmi a Sakkwato. Zuwan Turawa kuma da kafuwar mulkin mallaka a ƙarshen ƙarni na sha tara (Ƙ19) da farkon ƙarni na ashirin (Ƙ20) ne ya sa aka raba wasu al’ummomi na wannan ƙasa da ‘yan’uwansu. Misali, ƙasar Katsina wadda a da can Maraɗi take cikinta, an raba su, Katsina ta zama cikin yankin da Turawan Ingilishi suke mulki, ita kuma Maraɗi ta koma yankin da Turawan Faranshi suke mulki. Akwai wurare da dama waɗanda irin wannan sauyi ya shafa a sassa daban-daban na ƙasar Hausa (Sallau, 2010: 28).

    Shugabanci a Tsakanin Hausawa Kafin da Bayan Shigowar Musulunci

    Shugabanci yana nufin yi wa al’umma jagora a halin zamantakewarsu na yau da kullum. A nan duk wanda aka ba ragamar tafiyar da mulkin al’umma, nauyi ya hau kansa na tsare lafiyarsu da dukiyarsu da mutuncinsu. Su kuma waɗanda ake shugabanta haƙƙinsu ne su ba wanda yake shugabancinsu haɗin kai da bin ummurnin sa ta hanyar bin doka da oda don ya sami sauƙin tafiyar da mulkinsu cikin kwanciyar hankali.

    Kafin shigowar wasu baƙi ƙasar Hausa shugabanci yana farawa daga gida, a kowane gida wanda yake ƙunshe da mutanen da suka kai biyu ko waɗanda suka wuce haka, akwai maigida wanda nauyin dukkan mutanen wannan gida yana kansa. Shi ne yake shugabancin harkokin rayuwar yau da kullum na mutanen da suke wannan gida. A saboda haka dukkan mutanen wannan gida waɗanda suka haɗa da matansa da ‘ya’yansa da ƙannensa da jikokinsa da barorinsa duk da matansu da ‘yan cin arziki suna bin ummurninsa. Haka kuma, shi ne yake ɗaukar nauyin yi masu dukkan abubuwan da suka shafi sutura da abinci da tsaro da kare mutuncinsu. Idan ire-iren waɗannan gidaje suka yi yawa, sai su kafa unguwa. Daga cikin masu waɗannan gidaje, sai a sami wani mai kwarjini da iya tafiyar da harkokin al’ummarsa a ba shi muƙamin mai’unguwa. Mutanen wannan unguwa ne suke zaɓar sa su kai shi ga magaji ko dagacinsu ko maigari wanda shi ne zai amince da shi. Daga nan nauyin tafiyar da harkokin mulkin al’ummar wannan unguwa ya hau kansa. Shi ne kuma zai riƙa wakiltarsu a duk wasu harkoki da kuma yin sasanci a tsakanin talakawan wannan unguwa. Haka kuma, shi zai riƙa tattara kuɗin harajin mutanen wannan unguwa don kai wa magaji ko dagacinsu (Usman, 1972:176).

    Samuwar unguwanni da yawa ke sa a sami magaji ko dagaci ko maigari wanda shi yake shugabantar masu unguwanni. Dukkan abubuwan da ke faruwa a waɗannan unguwanni sai an sanar da shi. Haka kuma, duk wani sasanci da ya gagari mai’unguwa, sai a kai wa magaji ko dagaci ko maigari don ya sasanta. Magaji ko dagaci ko maigari ne yake wakiltar al’ummominsa waɗanda suke zaune a unguwanni a wasu al’amuran da suka shafi waɗannan unguwanni, kuma shi masu unguwanni suke kai wa kuɗin harajin unguwanninsu don ya kai wa uban-ƙasa ko hakimi.

    Garuruwan magaddai ko dagatai ko masu gararuruwa da yawa suke samar da ƙasar uban-ƙasa ko hakimi wanda shi yake shugabancin dukkan garuruwan magaddai ko dagatai masu garuruwa da suke ƙarƙashinsa. Dukkan abubuwan da ke faruwa a garuruwan magaddai ko dagatai ko masu garuruwa sai an sanar da uban ƙasa ko hakimi, kuma shi yake wakiltarsu a wasu ma’amalolin da suka shafi wannan ƙasa tasu. Idan magaddai ko dagatai ko masu garuruwa suka gaza wajen yin sasanci a tsakanin talakawansu, sai su miƙa maganar ga uban-ƙasa ko hakimi wanda zai yi iyakar ƙoƙarinsa ya yi sasanci. Bayan magaddai ko dagatai ko masu garuruwa sun kammala tattara kuɗin harajin ƙasashensu, sai su kawo wa uban-ƙasa ko hakimi, daga nan sai ya kai wa sarki. Waɗannan ƙasashe na iyayen ƙasa ko hakimai ne suke taruwa su kafa ƙasar sarki wanda shi ne wuƙa da nama a duk harkokin da ke faruwa a wannan masarauta. Dukkan mutanen da suke zaune a wannan ƙasa na ƙarƙashin ikonsa, kuma iyayen ƙasa ko hakimai na sanar da shi dukkan abubuwan da ke faruwa a ƙasashensu. Idan iyayen ƙasa ko hakimai sun gaza wajen yin sasanci tsakanin talakawansu, sai su kai maganar ga sarki, wanda ta hanyar shawartar ‘yan majalisarsa zai yanke hukunci na ƙarshe ko da daɗi ko ba daɗi. Wanda hukunci bai yi wa daɗi ba, dole ya yi haƙuri (wannan dalilin ne ya sa ake yi wa sarakunan gargajiya na ƙasar Hausa laƙabi da sunan wuƙar-yanka). Idan iyayen ƙasa ko hakimai suka kammala tattara kuɗin haraji na ƙasashensu, sai su kai wa sarki, wanda zai sa a saka su cikin Baitulmali don gudanar da harkokin mulki na wannan masarauta (Usman, 1972:176).

    A kowace masarauta akwai ‘yan majalisar wannan sarki, su ne suke taimaka wa wannan sarki da shawarwarin aiwatar da mulkin wannan ƙasa cikin nasara da adalci. Waɗannan ‘yan majalisa sun haɗa da waziri wanda shi ne babban mai taimaka wa sarki, kuma a mafi yawancin lokaci shi yake wakiltarsa a lokacin da ya yi wata tafiya wajen masarautarsa. Bayansa akwai alƙali da magatakarda da ma’aji ko ajiya da sarkin fada da shamaki da shantali da galadima da sarkin gida da sauransu da dama.

    Bayan waɗannan sarautu, akwai waɗanda ake ba masu yin sana’o’in gargajiya. Kowace sana’a tana da wanda ake ba jagorancin masu yin wannan sana’a don ya yi jagoranci da sasanci a tsakanin masu yin wannan sana’a da kuma tafiyar da sana’ar bisa ingantaccen tsari. Ire-iren waɗannan sarautu sun haɗa da sarkin noma ga manoma da sarkin maƙera ga maƙera da sarkin aska ga wanzamai da sarkin makaɗa ga makaɗa da sanƙira ko sarkin roƙo ga maroƙa da sarkin fawa ga mahauta da sauransu da dama (Adamu, 1978:5).

    Dukkan waɗannan sarautu da aka yi bayani a kansu tun daga mai unguwa zuwa ga sarki da ‘yan majalisarsa da masu riƙe da sarautun gargajiya, an tsara su ne bisa tafarkin gado. Watau idan wanda yake riƙe da sarauta ya rasu ko aka tuɓe shi, a mafi yawancin lokaci ana zaɓar wani daga cikin ‘ya’yansa don ya gaje shi.

    Shigowar Addinin Musulunci Ƙasar Hausa

    An gudanar da bincike masu yawa dangane da addinin Musulunci wanda shi ne addinin da Allah Maɗaukakin Sarki Ya aiko ta hannun Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, don ya shiryar da al’ummar duniya zuwa ga hanya madaidaiciya a cikin shekara 610 Miladiyya. Addinin Musulunci ne ya biyo bayan addinin Kirista wanda Allah Maɗaukakin Sarki ya aiko ta hannun Annabi Isa, Allah ya yarda da shi. A tsakanin waɗannan addinai akwai kimanin shekaru ɗari shida Annabi Muhammadu ne ya joganci al’ummar musulmi a Madina (Ibrahim, 1982:63).

    Wajen tafiyar da wannan al’umma ba a nuna ƙabilanci ko fifiko tsakanin jama’ar da suke cikinta. Abin da ta sa gaba shi ne haɗin kai da son juna da nuna ‘yan’uwantaka a tsakanin Musulmi. Babban tsarin mulkin wannan al’umma shi ne shari’ar addinin Musulunci. Kafin Annabi ya ƙaura, ya bar wa al’ummar Musulmi Alƙur’ani Maigirma da kuma Hadisai don su yi masu jagora dangane da addininsu (Ibrahim, 1982:63).  

    Duk da cewar addinin Musulunci ya daɗe da shigowa ƙasashen Afrika ta Yamma, bai shigo ƙasar Hausa da wuri ba. Wannan kuwa ya faru ne saboda a wancan lokaci babu wasu manyan kasuwanni da kuma kyawawan hanyoyin safara waɗanda suka haɗe ƙasar Hausa da sauran sassan ƙasashen Afrika ta Yamma. A saboda haka yana da matuƙar wuya a ce ga takamaiman lokacin da addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa. A sakamakon samuwar hanyoyin ciniki da suka ratsa ta cikin hamadar Sahara sun taimaka wajen shigowar addinin Musulunci cikin ƙasar Hausa. Ta waɗannan hanyoyi ne ‘yan kasuwa suka fara shigowa ƙasar Hausa don yin kasuwanci da kuma yaɗa addinin Musulunci. Haka kuma, ta waɗannan hanyoyi ne ƙabilun Afrika ta Yamma waɗanda suka fara karɓar addinin Musulunci kamar Mandingo da Wangarawa da Fulani suke bi suna zuwa Makka domin yin aikin Hajji. Saboda haka, ana tsammanin addinin Musulunci ya fara karɓuwa sosai a ƙasar Hausa cikin ƙarni na goma sha huɗu. An bayyana Katsina ita ce ƙasar da ta fara karɓar addinin Musulunci a cikin ƙasashen Hausa. Wannan kuwa ya faru ne saboda hanyar fatake wadda ta taso daga Tambutu, sai ta fara zuwa Katsina sannan ta isa Kano. Haka kuma, an bayyana cewa, a wajen tsakiyar ƙarni na goma sha biyu, Katsina na da babbar kasuwa wadda fatake da daman gaske waɗanda suka haɗa da Larabawa da Azbinawa da Wangarawa suke haɗuwa don yin cinikayya (Ibrahim, 1982:74-75).

    An ce addinin Musulunci ya shigo ƙasar Katsina a lokacin Sarkin Katsina Muhammadu Korau wanda ya yi mulki a shekarun 720-754 Bayan Hijira daidai da 1320-1353 Miladiyya. Haka kuma, sarakunan da suka biyo bayansa duk Musulmi ne, waɗanda suka haɗa da Sarkin Katsina Ibrahim Sara da Sarkin Katsina Ali Murabus. Dukkan waɗannan sarakuna sun taimaka wajen yaɗa addinin Musulunci a ƙasar Katsina. Bayan waɗannan sarakuna, wani sarki da ya ƙara taimakawa wajen haɓakar addinin Musulunci a ƙasar Katsina shi ne Sarkin Katsina Maja wanda ya yi sarauta a cikin shekarun 900-927 Bayan Hijira daidai da 1494-1520 Miladiyya. A lokacin mulkin wannan sarki, ya yi ƙoƙarin ganin ya mayar da addinin Musulunci ya zama na kowa-da-kowa a duk ƙasar Katsina. Ya sa an gina Masallatai, ya kuma umurci talakawa da su riƙa yin salloli biyar na kowane yini a cikinsu. A lokacin mulkinsa ne mashahuran malamai da yawa suka ziyarci Katsina, cikinsu har da Shehu Abdulkarim Al-Maghili.

    Ana tsammanin addinin Musulunci ya shiga ƙasar Kano a zamanin mulkin Sarkin Kano Aliyu Yaji, wanda ya yi mulki a cikin shekarun 750-787 Bayan Hijira daidai da 1349-1385 Miladiyya. Wata ƙungiyar Wangarawa wadda ta ƙunshi kimanin mutane arba’in su ne suka kawo addinin Musulunci Kano a ƙarƙashin shugabansu Abdurrahman Zaiti. Waɗannan mutane sun bar ƙasarsu da niyyar zuwa Makka don yin aikin Hajji. A lokacin da suka shigo Kano sun yi kira ga Sarkin Kano da ya shiga addinin Musulunci, cikin yardar Allah, wannan sarki ya karɓi addinin. Daga nan sai suka umurce shi da ya sare tsamiyar tsafinsu ta Madabo ya gina Masallaci a wurin. Sarki ya yarda ya aikata abubuwan nan da aka umurce shi ya yi. Bayan da sarki ya amshi addinin Musulunci, sai ya umurci dukkan talakawansa da su amshi addinin, wasu suka karɓa wasu kuma suka ƙi, waɗanda suka ƙi sai sarkin ya yaƙe su.

    An bayyana cewa, addinin Musulunci ya ƙara haɓaka sosai a Kano zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa wanda ya yi mulki a shekarun 858-905 Bayan Hijira daidai da 1463-1499 Miladiyya. A lokacin mulkinsa ne wasu Shaihunan Malamai suka shigo ƙasar Hausa don jaddada addinin Musulunci. Daga cikinsu akwai Shaihu Muhammadu Ibn Abdulkarim al-Maghili. Wannan malami ya zo Kano da litattafan addinin Musulunci masu yawa. A saboda iliminsa ne ya sa Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya roƙe shi da ya riƙa zama a fada don ya taimake shi yin shari’a. Shi kuma, sai ya ummurci sarki da ya gina masallacin juma’a, wanda sarki ya amince ya gina. Kafin Al-Maghili ya bar Kano, sai da ya rubuta wa Sarki Muhammadu Rumfa litattafan hukunce-hukuncen addinin Musulunci waɗanda za su taimaka masa wajen tafiyar da mulki kamar yadda shari’ar addinin Musulunci ta tsara. Waɗannan litattafai su ne kamar haka:

    (i)     Tajulmulk Fi Ma Ya Jibu Alal Muluki (Kambin Sarauta a Kan Abin da ya Wajaba a Kan Sarauta).

    (ii)  Majmu’at al-Maghili Fi Shu’unin al-Imarati (Talifin al-Maghili a cikin Sha’anunuwan Sarauta)

    (iii)   Ma Yajuz Ala al-Hukkumi fi Raɗ’i Nasi an al-Haram (Abin da ya Halatta Kan Masu Hukunci Don Tsawatar da Mai Rabkana Kan Cin Haram).

    Bayan Al-Maghili, wani malami mai suna Shaihu Abdulrahman al-Suyuɗi mutumin Masar ya ziyarci Kano a lokacin mulkin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa. Wannan malami ya sadu da Shaihu al-Maghili a Katsina. A Kano Shaihu al-Suyuɗi tare da wasu malamai da suka zo Kano sun rubuta shahararren littafin tafsirin Alƙur’ani Maigirma wanda ake kira Tafsirin Jalalaini. Ana amfani da wannan littafi don yin wa’azi a lokacin watan azumi a duk faɗin ƙasar Hausa har a wannan zamani (Ibrahim, 1982:81).

    Tun daga wancan lokaci har zuwa wannan zamani a kullum addinin Musulunci sai ƙara samun karɓuwa da ɗaukaka da bunƙasa yake yi a ko’ina cikin ƙasar Hausa. An bayyana cewa, daga garuruwan Katsina da Kano ne addinin Musulunci ya bazu zuwa sauran ƙasashen Hausa waɗanda ba sa kan hanyoyin da fatake ke bi irin su Gobir da Zamfara da Zazzau. Ana sa ran cewa addinin Musulunci ya isa Zazzau a cikin ƙarni na goma sha biyar (Osae, 1968:80).

    Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo

    Idan ana maganar shigowar addinin Musulunci, yaɗa shi da bunƙasarsa a ƙasar Hausa dole a duba jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. An gudanar da wannan jihadi ne daga shekarar 1804 zuwa 1809 Miladiyya. Kamar yadda aka bayyana a bayanan da suka gabata cikin wannan nazari, addinin mutanen ƙasar Hausa na farko shi ne addinin gargajiya na bautar iskoki da tsafe-tsafe da camfe-camfe. A dalilin shigowar addinin Musulunci an rushe wannan hanyar bauta, don kuwa daga cikin shika-shikan addinin Musulunci akwai kaɗaita Allah Maɗaukakin Sarki. Ma’ana ba a bauta wa kowa sai Allah wanda ba Shi da abokin tarayya. Duk da kasancewar sarakunan ƙasar Hausa sun karɓi addinin Musulunci su da talakawansu, sai suka riƙa haɗa bautar addinin Musulunci da yin tsafe-tsafe da camfe-camfe, kuma suna shawartar malaman tsibbu da ‘yan bori wajen yin wasu harkokin yau da kullum. Waɗannan al’adu da sarakunan ƙasar Hausa da talakawansu ke aiwatarwa, ya sa malaman addinin Musulunci waɗanda suke son ganin ana aiwatar da addinin Musulunci kamar yadda shari’a ta tsara, suka fara yin wa’azi ga mutanen ƙasar Hausa don tsarkake addinin. Haka kuma, a jawo waɗanda suka yi ridda da waɗanda ba su ma shiga addinin ba don su shiga.

    Daga cikin ire-iren waɗannan malamai wanda ya fi fice a kan wannan harka shi ne Shehu Usmanu Ɗanfodiyo wanda ya fito daga cikin zuri’ar Toronkawa-Fulani. A farkon ƙarni na goma sha takwas mahaifansa sun zauna a Ƙwanni, daga baya sai suka yi ƙaura suka koma Maratta inda aka haife shi a shekara ta 1168 Bayan Hijira daidai da 1754 Miladiyya.

    Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya fara karatun addini a wurin mahaifiyarsa Hauwa’u da mahaifinsa Muhammadu Fodiyo. Bayansu ya yi karatu a wurin wasu malamai kamar Muhammadu Sambo ɗan Abdullahi da Malam Abdurrahman ɗan Hammada da Malam Bunuduwa Bakabe da Alhaji Muhammadu bn. Raj da kuma Malam Shehu ɗan Muhammadu ɗan Hashimu na Zamfara. Daga cikin malamansa, Malam Jibril bn. Umar na Ahir (Agadez) ya fi yin tasiri kan himmar Shehu ta son kawo gyaran rayuwar al’umma ta yadda za ta dace da tafarkin addinin Musulunci (Yahaya, 1988:49-50).

    Sakamakon matsalolin da aka samu tsakanin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da sarakunan Gobirawa sun yi sanadiyyar ɓarkewar yaƙi tsakani rundunar Shehu da Sarkin Gobir Yunfa a shekara ta 1804.

    A wannan yaƙi dakarun Musulmi a ƙarƙashin shugabancin Shehu sun yi nasara a kan mayaƙan Sarkin Gobir Yunfa, aka kashe shi, Musulmi suka cinye masarautar Gobirawa da take a Birnin Alƙalawa. Ragowar Gobirawa suka tsorata suka gudu suka yi wajen arewa. Wannan ne ya sa abokan wasan su suke yi masu kirari da cewa “a mazaya a maida iri gida”.

    Wannan nasara da Musulmi ƙarƙashin Shehu suka samu a kan mayaƙan Gobirawa ta taimaka ƙwarai wajen faɗuwar sauran biranen ƙasar Hausa da kewaye. Kafin cikar shekara ta 1224 Bayan Hijira daidai da 1809 dukkan garuruwan ƙasar Hausa sun fita daga hannun sarakunan Haɓe. Daga nan sai Shehu ya zaɓi Malamai waɗanda suka san ilimin addinin Musulunci, kuma mafi yawancinsu Fulani ne daga cikin jama’arsa ya ba su sarautar waɗannan garuruwa, cikinsu akwai Malam Ummarun Dallaje wanda aka ba tutar aiwatar da jihadi a ƙasar Katsina. Shehu ya ɗauki wannan mataki ne don ya sami sauƙin tafiyar da manufarsa ta jaddada addinin Musulunci. Akwai garuruwa waɗanda ba sa cikin garuruwan ƙasar Hausa kuma ba na Hausawa ba, amma suna cikin garuruwan da aka ci da yaƙi, kuma suka zama cikin Daular Usmaniyya wadda aka kafa bayan yaƙi.

    Dukkan waɗannan malamai da aka ba sarautar garuruwan ƙasar Hausa da na maƙwabta, Shehu ya ba su tutoci don su gudanar da yaƙin jihadi a waɗannan ƙasashe da aka ba su. Kafin su tafi sai da ya yi masu gargaɗi idan sun kafa mulki su yi jagorancin jama’arsu cikin hasken Musulunci da nuna adalci. Wannan shi ne lokaci na farko da ƙasashen Hausa suka haɗu a inuwar daula ɗaya wadda ake kira da sunan “Daular Usmaniyya”, kuma Sarkin Musulmi shi ne shugaban dukkan sarakunan da suke ƙarƙashin daular. Kowane daga cikin waɗannan sarakuna, Sarkin Musulmi ne yake naɗa shi, amma duk da haka a kowane gari akwai masu zaɓen sarki waɗanda da ma can akwai su, don kuwa kafuwar wannan sabuwar daula bai sauya su ba. Dukkan wanda suka zaɓa, sai a kai wa Sarkin Musulmi, idan ya aminta da shi, sai ya naɗa shi.

    Bayan kammala yaƙin jihadi saboda rashin sha’awarsa da yin mulki, sai Shehu Usmanu ya koma Sifawa da zama, ya ci gaba da yin wa’azinsa da koyarwa da rubuce-rubuce, ya kuma riƙa yin kira ga Musulmi da su riƙa kula da addininsu, a daina zalunci da cin rashawa da sauran miyagun halaye. Masu neman ilimi daga ko’ina cikin wannan daula suka riƙa zuwa wurinsa don yin fatawa da ɗaukar karatu da kuma neman tubarraki (Yahaya, 1988:51).

    Su kuma garuruwan da aka ci da yaƙi watau waɗanda aka kafa Daular Usmaniyya, sai ya raba su biyu. Kashi na farko wanda yake a ɓangaren gabas da ya ƙunshi dukkan garuruwan da ake kira “Hausa Bakwai” ya shugabantar da ɗansa Muhammadu Bello don ya jagorance su, aka naɗa masa sarautar Sarkin Musulmi. Bayan naɗa shi, sai ya zo cikin ƙasar Gobir ya gina sabuwar masarautarsa a inda Sakkwato take a yanzu a cikin shekara ta 1327 Bayan Hijira daidai da 1809 Miladiyya. Wannan ya nuna ke nan garin Sakkwato ba ya cikin tsofaffin garuruwan ƙasar Hausa. A ɗaya ɓangaren kuma, watau daga yamma wanda ya ƙunshi dukkan garuruwan da ake kira “Banza Bakwai” ya danƙa su hannun ƙanensa Abdullahi Ɗanfodiyo, shi kuma aka naɗa masa sarautar Sarkin Gwandu, sai ya yi tasa masarautar a Birnin Kabi cikin ƙasar Argungu (Ibrahim, 1982:95).

    Shugabanci a Ƙasar Hausa Lokacin Mulkin Mallaka

    Sakamakon shigowar baƙi ƙasar Hausa musamman Turawa da suka kawo mulkin mallaka sun shigowa da wani sabon tsarin mulki wanda suka riƙa shugabantar al’ummar Hausawa ta hanyar sarakuna da sauran shugabanninsu, wanda da turancin ingilishi suka kira Indirect Rule. A taƙaice a mulke ku a fakaice. Gwamna Lugga ne ya tsara wannan mulki, ta hanyar barin sarakunan gargajiya ikon tafiyar da mulkin ƙasashensu kamar yadda suke yi kafin zuwan Turawa, amma shi ke ba su umurnin abubuwan da za su yi a madadin Gwamnatin Ingila, saɓanin kafin shigowarsu lokacin da sarakuna su ke mulkin ƙasashensu ba tare da sa idon wani ba. Kamar yadda sarakunan gargajiya suke da mataimaka wajen tafiyar da mulkin ƙasashensu waɗanda suka haɗa da hakimai da dagatai da masu unguwanni kafin shigowar Turawan mulkin mallaka, haka shi ma Gwamna Lugga sai ya sa Razdan-Razdan su riƙa taimaka masa a larduna da ya ƙirƙiro. Akwai larduna da yawa da Turawa suka ƙirƙiro a ƙasar Hausa waɗanda suka haɗa da Lardin Kano da Lardin Zazzau da Lardin Sakkwato da Lardin Katsina da dai sauransu. A wancan lokaci kowane lardi yana da matsayi irin na jihohi a wannan zamani. Kowane lardi na da nasa Razdan wanda yake kula da shi. An karkasa waɗannan larduna zuwa gundumomi, kuma kowace gunduma tana da nata D. O District Officer mai kula da ita. Su kuma gundumomi a wancan zamani suna da matsayi kamar na ƙananan hukumomi a wannan zamani. A nan an sami mulki iri biyu a duk faɗin tsohuwar Daular Usmaniyya da rana tsaka, ga dai mulkin gargajiya na sarakuna, sannan kuma ga mulkin mallaka na Turawa a ƙarƙashin tutar Ingila wanda Gwamna Lugga da Razdan-Razdan da D. O-D. O suke aiwatarwa. Wannan mulki ne ya kawo ƙarshen cikakken mulkin sarakunan ƙasar Hausa ga al’ummominsu.

    Babban ƙalubalen da ke gaban Gwamna Lugga shi ne ya sami ‘yan ƙasa waɗanda za su riƙa taimaka masa wajen tafiyar da mulki a ofisoshi kamar yadda ake yi a Ingila. Waɗannan mutane ba za su samu ba, dole sai an kafa makarantun da za su horar da su. Wannan ne ya sa shi ɗaukar matakin da ya kai ga kafa makarantar Ɗan Hausa a Nasarawa Kano, wadda ta zama makarantar Gwamnati ta farko a duk faɗin ƙasar Hausa, aka kuma ba wani Bature mai suna Sir Hans Ɓischer shugabancin ta a shekara ta 1909. Saboda yadda yake jin Hausa ake yi masa laƙabi da Ɗan Hausa. Sannan kuma a shekara ta 1921 aka kafa Kwalejin Katsina wadda ta yaye mafi yawancin ‘yan bokon Arewa na farko waɗanda suka haɗa da Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Abubakar Tafawa Ɓalewa da Malam Aminu Kano da Shehu Shagari da sauransu.

    Samuwar waɗannan ‘yan boko ne a arewa da kuma kudanci ya taimaka wajen tursasawa Turawan Mulkin Mallaka saka ‘yan ƙasa wajen tafiyar da mulkin ƙasa. Waɗannan dalilai ne suka sa Turawa sake fasalin yadda za a gudanar da mulkin ƙasar da a yau ake kira Nijeriya, ta hanyar gudanar da tarukan fasalin tsarin mulki wanda aka fara gudanarwa a shekara ta 1922.

    Tsarin Mulkin Sir Hugh Clifford na Shekara ta 1922

    Bayan haɗe kudanci da arewacin Nijeriya a shekara ta 1914 da kuma samuwar ‘yan ƙasa waɗanda suka sami ilimin zamani a makarantun da Turawa suka kafa a sassa daban-daban na Nijeriya da kuma wasu da suka sami damar zuwa Ingila irin su Dr. Akinwade Saɓage, sun fahimci cewa duk da kasancewar an sami ‘yan ƙasa waɗanda za su iya wakiltar al’ummominsu wajen tafiyar da mulkin ƙasa, amma Turawan Ingila sun mamaye kome dangane da harkokin da suka shafi mulki da tattalin arzikin da ake samu a wannan ƙasa. Waɗannan dalilai ne suka sanya wasu daga cikinsu suka ga ya dace a saka ‘yan ƙasa wajen tafiyar da mulkin Nijeriya. Duk da kasancewar Gwamna Lugga bai saurare su, ba su yi ƙasa a guiwa ba, don sun ci gaba da wannan fafitika wadda har ta kai su Ingila don ganin haƙar su ta cimma ruwa. Wannan gwagwarmaya ce ta sa, gwamnan da ya gaji Gwamna Lugga, wato Sir Hugh Clifford shirya taron tsarin mulki a shekara ta 1922. A wannan sabon tsarin mulki an sauya tsarin da Gwamna Lugga ya bi wajen tafiyar da mulkin ƙasar Nijeriya, don kuwa tsarin mulkin ya ƙirƙiro hanyar zaɓen wakillai don wakiltar sassan da suka fito. Haka kuma, ya ƙara wayar da kan ‘yan ƙasa shiga harkokin siyasa da gwagwarmayar kishin ƙasa. A wannan sabon tsarin mulki Arewacin Nijeriya bai sami wakilci ba, don kuwa Gwamna ne ke aiwatar da kome a madadinsu. Haka kuma, Gwamna shi yake tsara duk wasu dokoki da suka shafi Nijeriya.

    Muhimman abubuwan da wannan tsarin mulki ya kawo su ne;

    ü  Ya buɗe ƙofar kafa jam’iyyun siyasa.

    ü  Ya ba da dama ga ‘yan ƙasa su shiga cikin harkokin siyasa.

    ü  Ya ba da damar kafuwar kamfanonin jaridu ‘yan ƙasa irin su,

    Lagos Daily News da Daily Times Nigeria Plc. a shekara ta 1925.

    ü  Ya ba da damar zaɓar wakilai.

    ü  Samuwar tsarin zaɓaɓɓun wakilai ya ƙara bunƙasa fahimtar siyasa da kishin ƙasa.

    Illolin wannan tsarin mulki sun haɗa da;

    v  ‘Yan ƙasa ba sa cikin majalisar zartarwa.

    v  Turawa ne suka mamaye majalisar zartarwa.

    v  Ba da shawara kaɗai ke aikin zaɓaɓɓun wakilai.

    v  An ba Gwamna cikakken ikon zartar da kome.

    v  Arewacin Nijeriya ba ya da wakilci a majalisa. Haka kuma, duk da kasancewar ƙasar Hausa na da ingantaccen daɗaɗɗen tsarin sarautar gargajiya wanda ake gudanarwa lokaci mai tsawo da ya gabata, ba a saka sarakunan gargajiya na ƙasar Hausa cikin wannan tsarin mulki ba.

    Tsarin Mulkin Sir Arthur Richards na Shekara ta 1946

    Kasancewar ‘yan ƙasa sun fahimci ire-iren illolin da suke tattare da tsarin mulkin Clifford, sai suka ƙara zafafa kururuwa kan bukatunsu yadda za a yi wa wannan tsarin mulki gyara ta yadda za a sami daidaito. Wannan al’amari ya faru daga shekara ta 1935 zuwa 1943 lokacin mulkin Sir Bernard Bourdillon, wanda ya gaji Clifford. Matakin farko da ya fara ɗauka shi ne,  a shekara ta 1939 ya karkasa Nijeriya zuwa manyan shiyoyi uku, wato shiyyar kudu wadda ta ƙunshi ƙasashen Yarabawa da shiyyar arewa wadda ta ƙunshi tsohuwar daular Usamaniyya da ƙananan ƙabilun da suke maƙwabtaka da ida, sai kuma shiyyar gabas wadda ta ƙunshi ƙasashen Ibo da maƙwabtansu na kudu-maso-kudu.

    Arthur Richards ne ya gaji Sir Bernard Bourdillon a matsayin Gwamna, daga nan ne a shekara ta 1946, ya kawo tsarin mulkin da ya maye gurbin na Clifford wanda ya ƙunshi tsare-tsare kamar haka;

    ü  Haɗe dukkan Nijeriya ƙarƙashin majalisar mulki ɗaya.

    ü  Kowane yanki yana da majalisarsa.

    ü  A Arewacin Nijeriya an samar da majalisa iri biyu, Majalisar Sarakuna da Majalisar Wakilai, amma a Yammaci da Gabacin Nijeriya kuma suna da majalisa ɗaya ta wakilai kawai.

    ü   An ba da damar da zaɓaɓɓun wakilai za su taimaka wa Gwamna tafiyar da mulki.

    ü  Zaɓaɓɓun ‘yan majalisar dokoki na shiyyoyi su ne za su zaɓi sauran wakilan majalisa.

    Muhimman abubuwa da wannan tsarin mulki ya ƙunsa;

    v  A karo na farko aka sami haɗaɗɗiyar majalisa wadda ta haɗe dukkan ‘yan majalisa na kudu da na arewa a majalisa ɗaya ta Nijeriya.

    v  ‘Yan ƙasa sun sami babbar damar da ta taimaka masu shiga majalisar tarayya ta ƙasa.

    v  Mafi yawancin masu wasu bukatu na musamman da sassan ƙasa sun shiga wajen zartar da mulkin ƙasa.

    v  Tsarin mulkin ya fahimci ire-iren bambance-bambancen al’ummomin Nijeriya.

    v  Haka kuma, a hankali aka shigar da salon mulkin ‘yan ƙasa ta hanyar sarakunansu cikin wannan tsarin mulki (Indirect Rule).

    Shi ma wannan tsarin mulki yana tattare da nasa illolin waɗanda suka haɗa da;

    ·         Majalusun shiyyoyi ba su da wani cikakken iko sai dai ba da shawara ko tuntuɓa. A taƙaice na je-ka-na-yi-ka ne.

    ·         Shigar da wakilai waɗanda ba zaɓaɓɓu ba yaudara ce kawai, don kuwa mafi yawancinsu sarakuna ko masu riƙe da muƙaman gargajiya ko kuma waɗanda gwamnati ta zaɓa.

    ·         An tilasta tsarin mulkin ga al’umma don ba zaɓin su ba ne. Wannan ya bayyana babu demokraɗiyya a cikinsa.

    ·         Ba da damar tsayawa a zaɓe ko gudanar da zaɓe ya tsaya ne a Lagos da Calabar kawai.

    ·         Sakamakon ƙirƙiro shiyoyi a Nijeriya ya haifar da bambance-bambance da rarrabuwar kanu da matsaloli tsakanin ‘yan Nijeriya, inda kowa yake ikirarin shiyyar da ya fito.

     

     

    Tsarin Mulkin John Macpherson na Shekara ta 1951

    Shi ma wannan tsarin mulki ya gamu da soke-soke saboda matsalolin da suke ƙunshe cikinsa. Waɗannan dalilai ne suka yi dalilin samun tsarin mulkin John Macpherson a shekara ta 1951 don magance waɗannan matsaloli. A watan Maris na shekara ta 1949, Gwamna Macpherson ya kafa wani babban kwamiti na ‘yan majalisar wakilai waɗanda za su ba da shawara yadda za a kauce wa dukkan wani kuskure a sabon tsarin mulkin da za a gabatar. Waɗanda aka zaɓa suka amince da ɗaukar nauyin da aka ɗora masu, amma sun ba da shawarar yana da matuƙar muhimmanci a zagaya lungu da saƙo na ƙauyuka da birane don tattaunawa da samun shawarwari daga al’ummomi da dama.

    Muhimman abubuwan da wannan sabon tsarin mulki ya fito da su sun haɗa da;

    ü  An kafa majalisar dokoki da majalisar zartarwa ta ƙasa wadda za ta riƙa gudanar da aikace-aikace.

    ü  Kowace shiyya tana da majalisar dokoki da majalisar zartarwa.

    ü  Majalisar Wakilai ta Tarayya tana da babban ɗakin taro ɗaya, kuma Gwamna shi ne shugabanta tare da manyan mambobi shida, da kuma zaɓaɓɓun wakilai ɗari da talatin da shida (136) waɗanda aka zaɓo daga majalusun shiyyoyi.

    ü  A ɓangaren zartarwa wato majalisar ministoci akwai Gwamna wanda shi ne shugabanta, sannan kuma akwai cikakkun ministoci goma sha biyu (12) da kuma shida (6) waɗanda ba cikakku ba. Kowace shiyya na zaɓo ministoci huɗu waɗanda suka ba da jimlar goma sha biyu (12).

    Muhimman abubuwan da wannan tsarin mulki ya kawo sun haɗa da;

    Ø  An sami daidato tsakanin wakilan da suka haɗa majalisar wakilai ta ƙasa yadda kowace shiyya ta sami adadin ‘yan majalisun da za su wakilce ta.

    Ø  A karon farko tun kafuwar Nijeriya an sami tsarin mulkin da ya bayar da damar samun ministoci ‘yan ƙasa a tarayya da shiyyoyi.

    Ø   A lokacin rubuta tsarin mulkin an nemi shawarwari daga al’ummomi daban-daban daga ƙauyuka da birane.

    Ø  Tsarin mulkin ya shimfiɗa wata ingantacciyar turba wadda ta kafa mulkin tarayya na gaskiya da gaskiya a tarayya da shiyyoyi.

    Ø  Tsarin mulkin ya samar da babbar majalisa ta ƙasa wadda aka sanya wa sunan Majalisar Wakilai.

    Bayan waɗannan muhimman abubuwa shi ma wannan tsarin mulki yana tattare da wasu illoli da matsalaloli kamar haka;

    v  Tsarin mulkin ya gaza matuƙar gaya wajen samar da ingantaccen shugabanci a gwamnatin tarayya.

    v  Ministoci ‘yan ƙasa ba su da cikakken iko a kan ma’aikatun da suke shugabanta.

    v  Tsarin mulkin ya taimaka sosai wajen zaɓen wakilai waɗanda ba su cancanta ba a tarayya da shiyyoyi.

    v  Wannan tsarin mulki ya cigaba da ba Gwamna ikon zartar da kome, ko an yarda ko ba a yarda ba. A taƙaice yana iya hawa kujerar-na-ƙi a kan kowace irin shawara da aka kawo masa.

    Dalilai da dama sun taimaka wajen rushewar wannan tsarin mulki, waɗanda suka haɗa da:

    a.Rikicin Gabacin Nijeriya na shekara ta 1953

    b.      Ƙudurin neman ‘yancin kai da Anthony Enahoro ya gabatar a shekara ta 1953.

    c. Ƙudirin ƙin amincewa da neman ‘yancin kai da ‘Yan’arewa suka gabatar wanda ya kawo rarrabuwar kanu.

    d.     Ƙoƙarin Arewacin Nijeriya na fita daga Tarayyar Nijeriya.

    e.Rikicin Kano a shekara ta 1953.

    Tsarin Mulkin Oliɓer Lytteton na Shekara ta 1953/54

    Sakamakon waɗannan matsaloli ne ‘yan ƙasa suka ci gaba da bayyana ƙorafe-ƙorafen su don a ƙara gyara al’amura yadda ‘yan ƙasa za su ƙara samun wakilci wajen tafiyar da mulkin ƙasa. Dalilin haka ya sa aka gudanar da taron tsarin mulki a London a shekara ta 1953 da kuma a Lagos a shekara 1954, sakamakonsu aka samar da tsarin mulkin Oliɓer Lytteton. A waɗannan taruka ‘yan arewa irin su, Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Malam Abubakar Tafawa Ɓalewa da sauransu sun sami damar halarta.

    Abubuwan da wannan tsarin mulki ya ƙunsa sun haɗa:

    Ø  An ƙara ba shiyyoyi ƙarin ‘yanci.

    Ø  Zama a shiyya ikon ‘yan shiyyar ne.

    Ø  An samar da Gwamnoni ga shiyyoyi, a Tarayya kuma aka samar da Gwamna Janar.

    Ø  Arewaci da Yammacin Nijeriya suna da Majalisu biyu, amma Gabacin Nijeriya suna da Majalisa ɗaya.

    Muhimman abubuwan da wannan tsarin mulki ya kawo sun haɗa:

    ü  Daga ƙarshe an kafa Gwamnatin Tarayya.

    ü  An gabatar da tsarin gudanar da zaɓe na gaba-ɗaya.

    ü  Ministoci suna da ikon zartarwa a ma’aikatansu.

    ü  Shugabannin Shiyyoyi wato Firemiya sun karɓi ikon gudanar da mulkin shiyyoyinsu.

    ü  Wannan tsarin mulki ya share hanyar samun ƙarin cigaba.

    ü  An ƙirƙiro ofishin Kakakin Majalisa.

    Illolin da suke tattare da wannan tsarin mulki sun haɗa da:

    v  Babu ofishin Firaminista a Gwamnatin Tarayya.

    v  Tsarin mulkin ya gaza wajen samar da Majalisa ta biyu a Tarayya.

    v  Har yanzu Gwamna Janar yana da ƙarfin ikon hawan kujerar-na-ƙi.

    v  Tsoron taushe ƙananan ƙabilu ya jawo ce-ce-ku-ce wajen neman ƙara shiyyoyi.

    v  Ministocin Gwamnatin Tarayya na yin biyayya ga shugabannin shiyyoyi.

    Shugabanci a Ƙasar Hausa Bayan Samun ‘Yanci Kai

    Daga cikin shirye-shiryen da Turawa suka yi na ba da mulkin kai ga al’ummomin Nijeriya shi ne, gabatar da tsarin mulki wanda zai zama jagora ga waɗanda za su zama shugabanni ‘yan ƙasa a sabuwar Nijeriya wadda za a ba ‘yancin mulkin kansu da kansu. Wannan dalili ne ya sa aka kafa kwamiti wanda zai rubuta wa Nijeriya tsarin mulkin samun ‘yancin kai a shekara ta 1960.

    Tsarin Mulkin Samun ‘Yancin Kai na Shekara ta 1960

    Tsarin mulkin samun ‘yanci na shekara ta 1960, ya samu ne sakamakon tsarin mulkin Oliɓer Lytteton na shekara ta 1953 da kuma tarukan da aka gudanar a London da Lagos a shekara 1954 da kuma na 1957/58, waɗanda suka ba da damar Nijeriya ta sami ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba, 1960.

    Wannan tsarin mulki ya ƙunshi abubuwa kamar haka:

    Ø  Sarauniyar Ingila ita ce shugabar ƙasa kuma Gwamna Janar shi yake wakiltarta.

    Ø  An rarraba yadda za a gudanar da mulki tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatocin Shiyyoyi.

    Ø  Hanyoyin da za a bi wajen yi wa tsarin mulkin gyara suna cikin tsarin mulkin.

    Ø  Manufofin kare haƙƙin ɗan’adam suna cikin tsarin mulkin.

    Ø  Hukumar Shari’a ta ƙasa ita ke da haƙƙin ɗaukar Babban Alƙalin Kotu ta ƙasa.

    Muhimman abubuwan da suke cikin wannan tsarin mulki sun haɗa da:

    ü  Wannan tsarin mulki na samun ‘yancin kai ya samar da majalisu biyu a tarayya, waɗanda suka haɗa da Majalisar Dattawa da Majalisai Wakilai ta Tarayya, sannan kuma a shiyyoyi akwai Majalisar Sarakuna da Majalisar Wakilai.

    ü  Tsarin mulkin ya ba da damar kula da dukiyar al’umma inda Ministan Kuɗi dole ya ba da sakamakon binciken da Darektan Binciken Kuɗi na Ƙasa ya bayar ga Majalisa.

    ü  Sakamakon samun ‘yancin kai ‘yan Nijeriya masu yawa sun sami guraben ayyuka waɗanda Turawan Ingila suka bari.

    ü  Samun ‘yancin kai ya ba Nijeriya damar ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da ƙasashe da dama.

    Shi ma wannan tsarin mulki yana tattare da wasu matsaloli waɗanda suka haɗa da:

    v  Ɗaya daga cikin matsalolin da wannan tsarin mulki ya ƙunsa sun haɗa da, har yanzu Sarauniyar Ingila ita ce shugabar ƙasa ta Je-ka-na-yi-ka.

    v  Kotun ƙoli ta ƙasa ba ita ce ƙarshen shari’a ba, don kuwa kwamitin Alƙalan Biritaniya su ke da ikon yanke hukuncin ƙarshe na dukkan wata shari’a da aka yi a Nijeriya.

    v  Tsarin mulkin yana da rauni don kuwa Gwamnatin shiyyoyi ce take zaɓo ‘Yan Majalisar Dattawa ba al’umma ne suke zaɓo su ba. Wannan ne ya sa suka zama ‘yan amshin Shata, sai abin da aka ba su umurni suke yi.

    v  Haka kuma, tsarin mulkin bai ba da hanyoyin da za a bi ba wajen ƙirƙiro sabbin shiyyoyi a Nijeriya. Wannan rashin hangen nesa ya kawo babbar matsala lokacin da aka so ƙirƙiro shiyyar Yamma ta Tsakiya.

     

    Tsarin Mulkin Jamhuriyar Nijeriya na Shekara 1963

    Mulkin Jamhuriya na nufin mulkin ‘yantacciyar ƙasa wadda zaɓaɓɓen shugaba yake shugabanta bisa wani ƙayyadajjen wa’adi. Saɓanin mulkin sarakunan gargajiya wanda ɗa kan gaji mahaifinsa, a irin wannan mulki ana zaɓar wanda zai gaji wanda adadin mulkinsa ya ƙare ko aka tuɓe shi ko ya rasu. Gwamnati ce wadda jama’a suke zaɓarta don ta wakilce su wajen tafiyar da mulkin ƙasa.

    Shugaban gwamnati ko Firaminista da Shugabannin Gwamnatocin Shiyyoyi suka zauna a Mayu na shekara ta 1963 suka zauna don tattauna abubuwan da suka shafi tsarin mulki. A wannan zama waɗannan shugabanni na Nijeriya suka tattauna tare da yanke hukuncin a gayyaci dukkan jam’iyyu a Lagos don tattauna muhimman sauye-sauye a tsarin mulkin Nijeriya. Dukkan waɗannan jam’iyyu sun haɗu a Lagos a watan Yuli na shekara 1963, inda suka aminta Nijeriya ta zama Jamhuriya, sannan kuma shugaban ƙasa ya zama shi yake da ƙarfin faɗa-a-ji na Gwamna Janar wanda yake cikin tsarin mulkin samun ‘yancin kai.

     Wannan tsarin mulki ya fito da abubuwa waɗanda suka haɗa:

    Ø  Tsarin mulkin ya ba da damar zaɓar shugaban ƙasa wanda ba wakilin Sarauniyar Ingila ba ne.

    Ø  An ba Majalisa damar ta yi gyara ga tsarin mulkin.

    Ø  An ba da hanyar da za a ƙirƙiro sababbin jihohi.

    Ø  Majalisa ta haɗa da Shugaban Ƙasa da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa.

    Ø  Kotun Ƙoli ta ƙasa ta zama kotun ƙarshe ta ƙasa.

    Muhimman abubuwan da suke cikin wannan tsarin mulki sun haɗa da:

    ü  Zaɓaɓɓen Shugaban ƙasa ya maye gurbin Sarauniyar Ingila wadda ita ce Shugabar Ƙasa a tsarin mulkin samun ‘yancin kai na shekara ta 1960.

    ü  Wannan tsarin mulki ‘yan ƙasa ne suka zauna suka tsara shi.

    ü  Kotun Ƙoli ta ƙasa ta zama kotun ƙarshe a shari’ar Nijeriya, inda ta maye gurbin Kwamitin Masana Shari’a na ƙasar Biritaniya.

    ü  An tabbatar da haƙƙoƙin ‘yan ƙasa cikin tsarin mulkin.

    ü  Tsarin mulkin ya ba ‘yan Nijeriya damar shawarta abin da zai zama makomarsu.

    Shi ma wannan tsarin mulki yana tattare da wasu matsaloli waɗanda suka haɗa da:

    v  Majalisar Dokoki ta ƙasa ce take zaɓen shugaban ƙasa wadda wakilanta ba su da yawa, maimakon dukkan ‘yan ƙasa su zaɓe shi.

    v  Sashen Majalisar Dokoki da Majalisar Zartarwa ne kaɗai suke gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

    v  Tsarin Mulkin ya ba zaɓaɓɓun ‘yan siyasa damar yin abubuwan da suka ga dama na biyan bukatunsu, fiye da yi wa al’ummar da suke wakilta ayyuka.

    v  Tsarin Mulkin ya ba ‘yan Majalisa iko mai ƙarfi.

    v  Firaminista na sauraren ‘yan Majalisa fiye da mutanen da suka zaɓe shi.

    Shigowar Sojoji Cikin Mulkin Nijeriya

    Shigowar sojoji cikin mulki na nufin sojoji su fito daga bariki su karɓe mulki daga farar-hula ta hanyar amfani da ƙarfi ko bindiga. Sojoji sun fara yin juyin mulki a Nijeriya a shekara ta 1966. Dalilan da suka haifar da wannan juyin mulki sun haɗa da:

    Ø  Jam’iyyun Siyasa ba a gina su a turbar ƙasa ba, kowace shiyya na goyon bayan wata jam’iyyar siyasa. Domin kuwa Jam’iyyar NCNC tana da magoya baya daga ƙasar Ibo, AG tana da magoya baya daga ƙasashen Yarabawa, sai kuma NPC wadda take da magoya baya daga Arewacin Nijeriya.

    Ø  Almubazzaranci da dukiyar al’umma.

    Ø  Rashin fahimta da ce-ce-ku-ce tsakanin manyan ƙabilun Nijeriya.

    Ø  An siyasantar da aikin soja, inda wajen ƙara wa soja girma, ba a la’akari da ƙwazonsa ko cancantarsa. Ana mayar da hankali wajen wa yake da shi a gwamnati.

    Ø  Nuna son kai ko ƙabilanci wajen ɗauka aiki ko ƙarin girman ma’aikata.

    Ø  Da sauransu.

     Wannan juyin mulki ne ya kawo Janar Johnson Aguiyi-Ironsi bisa mulki a matsayin Shugaban Ƙasa na farko na mulkin soja a Nijeriya a shekara ta 1966.

    Bayan wata shida da hawansa kujerar mulki, saboda wasu matsaloli da suke tattare da shugabancinsa, musamman fifita ‘yan ƙabilar Ibo saman sauran ƙabilun Nijeriya, da kuma kashe mafi yawancin ‘yan siyasar Arewacin Nijeriya irin su Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Shiyyar Arewa da Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa Firaministan Nijeriya da wasu ‘yan siyasar Shiyyar Yamma, irin su Akintola, ya sa wasu sojoji suka yi masa juyin mulki inda suka ɗora Laftana Kanar Yakubu Gowon a matsayin shugaban mulkin soja na biyu a Nijeriya. Domin ya magance matsalar da za ta sake sanya wasu sojoji yin juyin mulki, sai Yakubu Gowon ya kafa Majalisar Ƙoli ta Mulkin Soja wadda ita ke da nauyin aiwatar da dukkan wasu aikace-aikace da dokokin Nijeriya. Wannan juyin mulki bai yi ‘yan ƙabilar Ibo daɗi ba, don kuwa a shekara ta 1967 zuwa 1971, Nijeriya ta yi yaƙin basasa da ‘yan ƙabilar Ibo ƙarƙashin jagoranci Odumegu Ojuku, wanda aka kashe mutane masu yawa daga sojoji da fararen hula masu biyayya ga Nijeriya da kuma sojoji da farar hula ‘yan-a-ware na Biafra. A ranar 27 ga watan Mayu, 1967, kafin fara yaƙin basasa, gwamnatin Gowon ta ƙirƙiro jihohi goma sha biyu waɗanda suke maye gurbin manyan shiyyoyin da Sir Bernard Bourdillon ya ƙirƙiro a shekara ta 1939.

    Duk da haka, shi ma Yakubu Gowon bai tsira ba, don kuwa wasu sojoji sun yi masa juyin mulki suka ɗora Janar Murtala Muhammad ya zama shugaban ƙasa a shekara ta 1975. A mulkinsa na ɗan ƙanƙanin lokaci, Janar Murtala ya kawo wasu sauye-sauye da ƙudurce-ƙudurce masu ma’ana waɗanda suka taimaka wa al’ummar Nijeriya, ciki har da mayar da mulki ga farar hula. Shi ma Janar Murtala bai tsira ba don kuwa a shekara ta 1976 wasu sojoji ƙarƙashin wani Kanar mai suna Bukar Suka Dimka suka shirya masa juyin mulki, inda suka kashe shi a Lagos, amma ba su sami nasarar karɓar mulki ba. Mataimakinsa Janar Olusegun Obasanjo ya gaje shi kan kujerar shugaban ƙasa tare da Janar Shehu Musa ‘yar’aduwa a matsayin mataimakinsa. Janar Obasanjo na hawa mulki ya sa aka kama waɗanda suka shirya juyin mulki aka yanke masu hukunci kisa da bindiga.

    Janar Obasanjo ya ci gaba da aiwatar da ayyukan da Janar Murtala ya fara waɗanda daga cikin su akwai sake tsara yadda za a tafi da ƙananan hukumomi wanda aka kafa kwamiti a shekara ta 1976. Dalilai da dama suka sanya aka sake tsarin ƙananan hukumomi, ciki har da kasancewar, su ne hukumomin da suke kusa da al’umma, don kuwa tsarin ƙananan hukumomin da Turawan Ingila suka kawo ba ya biyan bukatun al’umma. Dangane da haka, abubuwan da wannan tsari ya kawo sun haɗa da:

    Ø  Sabon tsarin ya kawo ƙaruwar yawan ƙananan hukumomi a duk faɗin ƙasar ta amfani da yawan al’ummomin da suke wuraren da aka ƙirƙiro ƙananan hukumomin.

    Ø  A karon farko Gwamnatin Tarayya Nijeriya ta ɗauki nauyin tafiyar da ƙananan hukumomi, inda ake ba kowace ƙaramar hukuma kasafin kuɗin da za a riƙa tafiyar da ayyuka.

    Ø  Ƙananan hukumomi sun zama ɓangare na uku na gwamnati idan aka haɗa da Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin jiha.

    Ø  Akwai demokraɗiyya wajen tafiyar da ƙananan hukumomi, don kuwa ana zaɓar waɗanda za su gudanar da mulki.

    Ø  Sabon tsarin ya kawo zaɓar shugaban ƙaramar hukuma da zaɓaɓɓun kansiloli da kuma naɗaɗɗun kansiloli masu duba ayyuka.

    Ø  Sarakunan gargajiya ba a ba su wani muhimmin aiki ba a wannan tsari, sai dai aka bar su a matsayin waɗanda za su tabbatar da bin doka da oda a masarautunsu. Sannan kuma aka ɗauke su a matsayin iyayen ƙasa, kuma masu adana al’adu da muradu da tarihin al’ummominsu

    Haka kuma, wannan gwamnati ta Murtala da Obasanjo ta kafa wani kwamiti na tsarin mulkin mayar da mulki ga farar hula na shekara ta 1979. Bayan da sojoji suka yi juyin mulki a shekara ta 1966, sai suka ajiye tsarin mulkin shekara ta 1963 a gefe. Gwamnatin Ironsi ta kafa kwamiti ƙarƙashin F. R. A. Williams don su sake tsara wani sabon tsarin mulki, amma ba su kai ga kammala aikinsu ba aka yi wa Ironsi juyin mulki.

    Tsarin Mulkin Jamhuriyar Nijeriya na Shekara ta 1979

    Yakubu Gowon wanda ya gaji Ironsi, ya sake kafa wani kwamiti wanda suka zauna a Aburi ta ƙasar Ghana, inda suka tsara wani sabon tsarin mulki wanda ba a aiwatar da shi. Gwamnatin Murtala da Obasanjo ce ta sake kafa wani kwamiti mai mambobi 49 ƙarƙashi jagorancin F. R. A. Williams a shekara ta 1975 don sake rubuta wani tsarin mulki.

    An kammala rubuta wannan sabon tsarin mulki a shekara ta 1976 inda aka ba mambobin sake tsarin mulki su 230 ƙarƙashin jagorancin babban alƙali Udo Udoma don gyara tsarin mulki. Sun kammala wannan aiki a shekara ta 1978. Majalisar Ƙoli ta Mulkin Soja ce ta sake bitar sa ta amince da wannan sabon tsarin mulki ta mayar da shi doka wadda za a fara amfani da ita a ranar 1 ga watan Oktoba na 1979.

    Abubuwan da wannan tsarin mulki ya ƙunsa sun haɗa da:

    Ø  Ya ba da damar zaɓar shugaba mai cikakken iko.

    Ø  Ya samar da majalisu biyu a Tarayya: Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Tarayya, amma jihohi suna da majalisar wakilai ɗaya-ɗaya.

    Ø  Ya ba da damar hanyoyin da za a riƙa samun kuɗaɗen shiga ta hanyar haraji.

    Ø  Tsarin mulkin ya tabbatar da zaman ƙananan hukumomi a matsayin ɓangare na uku na gwamnati.

    Ø  Ya zayyana ire-iren ayyukan da ƙananan hukumomi za su riƙa gudanarwa.

    Ø  An kafa hukuma mai bin diddiƙin abubuwan da ma’aikata suka mallaka da hanyar da suka sami abin da suka mallaka.

    Ø  Tsarin mulkin ya ba da ingantattun ƙudurori da yadda za a aiwatar da su wajen aikace-aikacen gwamnatocin jihohi.

    Wannan tsarin mulki yana ƙunshe da abubuwa masu kyau waɗanda suka haɗa da:

    ü  Tsarin mulkin ya ba da damar kafa jam’iyyun siyasa.

    ü  Ƙananan hukumomi sun zama ɓangare na uku na gwamnati.

    ü  An yi ƙoƙarin daɗe duk wata hanya ta cuwa-cuwa.

    ü  An kawo manufar raba mulki don sanin wuraren da matsala ta faru.

    ü  A lokacin gaggawa majalisun dokoki na jihohi na da izinin ba da damar gudanar da aiki.

    ü  Shugaban ƙasa yana da cikakken ikon aiwatar da ayyukan gwamnati.

    ü  Tsarin mulkin ya yi ƙoƙarin daƙile cin-hanci-da-rashawa ta hanyar kafa hukuma mai bin diddiƙin abubuwan da ma’aikata suka mallaka da hanyar da suka sami abin da suka mallaka.

    Shi ma wannan tsarin mulki kamar sauran waɗanda suka gabace shi yana tattare da wasu matsaloli kamar haka:

    v  Tsarin mulkin ya ba shugaban ƙasa iko wanda ya wuce kima.

    v  An siyasantar da sashen shari’a.

    v  Tsarin mulkin yana da matuƙar tsada wajen tafiyar da shugabanci irin na siyasa.

    v  Tsarin ba kowa damar ya gudanar da aikinsa, ‘yan siyasa sun yi masa mummunar fahimta.

    v  Tsarin raba dukiyar ƙasa wadda aka ba haɗakar majalisun tarayya ba a yin shi yadda ya dace, don kuwa aiki ne na ƙwararru ba ‘yan majalisa ba.

    v  Damar tsige zaɓaɓɓe da aka ba majalisu ba a tsara ta yadda ya dace ba.

    Bayan an gudanar da zaɓe a shekara ta 1979 an kuma kafa gwamnatin farar hula ƙarƙashin Alhaji Shehu Aliyu Shagari, sun shekara huɗu suna mulki aka sake zaɓe a shekara ta 1983. A watan Disamba na shekara ta 1983 sojoji suka yi masu juyin mulki aka ba Manjo Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa. Lokacin mulkinsa Janar Buhari ya kawo sauye-sauye masu yawa waɗanda suka taimaka wa talaka. Yaƙi da rashin ɗa’a da tarbiyya da cin-hanci-da –rashawa sun sami karɓuwa wajen al’ummar Nijeriya, kuma sun taimaka wajen farfaɗo da tarbiyya da zamantakewa da bunƙasar tattalin arziki. Shi ma a shekara ta 1985, wasu sojoji daga cikin gwamnatinsa suka yi masa juyin mulki aka ba Janar Ibrahim Badamasi Babangida shugabanci. Janar Babangida ya yi ƙoƙarin mayar da mulki ga farar hula, amma saboda wasu bukatu nasa haƙa ba ta cimma ruwa ba. An gudanar da zaɓe tsakanin M. K. O. Abiola da Alhaji Bashir Tofa, inda alƙalumma zaɓe waɗanda aka samu ta bayan fage sun bayyana Abiola ya ci zaɓen amma Gwamnatin Babangida ta soke zaɓen. Wannan dalili ne ya kawo matsaloli da kafuwar ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam irin su NADECO a sassa daban-daban na Tarayyar Nijeriya musamman ƙasashen Yarabawa waɗanda suke ganin an tauye masu haƙƙinsu. Da abubuwa suka ƙi-ci suka ƙi-cinyewa, sai Babangida ya yada ƙwalon mangoro ya huta da ƙuda, inda ya amince a kafa gwamnatin haɗin-kan-ƙasa ƙarƙashin jagorancin wani Bayarabe mai suna Arnest Shonekan don a sanyaya zuciyar Yarabawa. Shi ma Shenekan bai daɗe yana gudanar da mulki ba ya sauka Janar Sani Abacha ya amshi mulkin. Lokacin mulkin Abacha an yi ƙoƙarin komawa mulkin farar hula inda aka fahimci yana son tuɓe kakin soja ya koma farar hula don a zaɓe shi shugaban ƙasa, amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba don kuwa Allah ya amshi rayuwarsa a ranar 8 ga watan Yuni shekara ta 1998. Bayan rasuwarsa an naɗa Janar Abdulsalam Abubakar a matsayin wanda zai gaji Janar Abacha. Da hawansa kujerar mulki abin da ya fara yi shi ne rushe dukkan jam’iyyun siyasa da Janar Abacha ya kafa da dukkan wasu hukumomi waɗanda aka ɗora wa nauyin miƙa mulki ga farar hula.

    Tsarin Mulkin Jamhuriyar Nijeriya na Shekara ta 1999

    A watan Disamba na shekara ta 1998 gwamnatin Janar Abdulsalam Abubakar ta kafa kwamitin ba da shawara kan yadda za a sake tsarin mulki ƙarƙashin Mai Shari’a Niki Tobi. Wannan kwamiti ya ba gwamnati shawara ta ɗauki tsarin mulki na shekara ta 1979 a yi masa gyare-gyare, amma gwamnatin Janar Abdulsalam ba ta amince ba, sai ta ɗauki tsarin mulki na shekara ta 1995 wanda Janar Abacha ya sa aka rubuta, ta yi ma shi gyare-gyare ta tabbatar da shi a matsayin karɓaɓɓen tsarin mulki a ranar 29 ga watan Mayu, shekara ta 1999.

    Abubuwan da wannan tsarin mulki ya ƙunsa sun haɗa da:

    Ø  Tsarin mulkin ya ƙara jaddada tsarin shugaban ƙasa mai cikakken iko.

    Ø  Tsarin mulkin ya ƙara jadadda raba iko tsakanin Gwamnatin Tarayya da Jihohi da Ƙananan Hukumomi.

    Ø  Tsarin mulkin ya tabbatar da jihohi 36 ba ragi ba ƙari.

    Ø  An ƙara tabbatar da Ƙananan Hukumomi a matsayin ɓangare na uku ga gwamnati.

    Ø  Tsarin mulkin ya ba tabbatar da jimilla ƙananan hukumomi 768 a Nijeriya da kuma 6 a Birnin Tarayya Abuja waɗanda suka ba da jimlar ƙananan hukumomi 774.

    Ø  A zaɓi shugabannin ƙananan hukumomi.

    Ø  An ba ‘yan jarida wani muhimmin matsayi da damar faɗin albarkacin bakinsu dangane da yadda gwamnati take aiwatar da ayyukanta ga al’umma.

    Muhimman abubuwa da wannan tsarin mulki ya ƙunsa sun haɗa da:

    ü  Tsarin mulkin ya kawo kafuwar Jamhuriya ta Huɗu da kuma tsarin shugaba mai cikakken iko.

    ü  Tsarin mulkin ya ƙayyade shekaru da matakin Ilimi ga dukkan wanda zai tsaya takara don a zaɓe shi a kowane muƙami.

    ü  Tsarin mulkin ya buɗe ƙofa wadda ta ba da damar shiga tare da bunƙasa harkokin siyasa daga tushe.

    ü  Tsarin mulkin ya ba da damar miƙa mulki da sojoji zuwa farar hula cikin kwanciyar hankali.

    Shi ma wannan tsarin mulkin yana da nasa matsaloli waɗanda suka haɗa da:

    v  Sojoji sun tilasta tsarin mulki ga farar hula.

    v  Tsarin mulkin yana da tsauri yadda zai yi wuya a yi sauye-sauye cikinsa.

    v  An gudanar da tsarin mulkin cikin gaggawa yadda aka tafka manyan kura-karai a cikinsa.

    v  An tsara shi yadda zai tafi daidai da muradun Abacha.

    v  Tsarin mulkin ya tauye ɓangare shari’a saɓanin bukatun da suke cikin tsari irin Jamhuriya.

    v  Tsarin mulkin ya fifita ilimi boko fiye da ilimin addini yadda ya ƙayyade ilimin boko ga dukkan mai bukatar takara.

    Bayan kafa jam’iyyun siyasa an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 27 ga watan Fabrairu na shekara ta 1999. Sakamakon zaɓe ya bayyana tsohon shugaban mulkin soja Janar Olusegun Obasanjo ya ci zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP tare da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, inda ya kayar da abokin hamayyarsa Chief Olu Falae da Alhaji Umaru Shinkafi na jam’iyyar AD-APP. Gwamnatin Janar Obasanjo da Atiku ta yi mulki na tsawon shekaru huɗu a wa’adi na farko (1999-2003).

    A wa’adi na biyu wanda aka gudanar da zaɓe a ranar 19 ga watan Afrilu, shekara ta 2003, Obasanjo da Atiku sun sake yin takara a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP, inda suka sami nasara a kan Janar Muhammadu Buhari da Chuba Okadigbo ƙarƙashin Jam’iyyar ANPP. Sakamakon irin yadda Buhari ya gudanar da mulki a lokacin yana soja ya sa mafi yawancin al’ummar Arewacin Nijeriya suka goya masa baya. Masu sa ido kan yadda aka gudanar da zaɓen na cikin gida da waje sun bayyana an yi maguɗi da ƙarin ƙuri’un bogi da ƙwatar akwati a wannan zaɓe. Waɗannan dalilai ne suka sa Janar Buhari da Jam’iyyarsa ta ANPP suka kai ƙara Kotu. Daga ƙarshe Kotu ta tabbatar da nasarar Obasanjo da Atiku.

    Lokacin da Janar Obasanjo ya fahimci wa’adin mulkinsa na biyu ya zo ƙarshe, sai ya so ƙara tsawaita mulkinsa zuwa wasu shekaru huɗu ta hanyar yi wa tsarin mulki gyara, amma bai sami nasara ba, don kuwa daga cikin gwamnatinsa da wajen ta aka yi wa wannan ƙuduri nasa ƙafar-ungulu yadda bai cimma burinsa ba. Dole ya yi haƙuri jam’iyyarsa ta PDP ta tsayar da Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Umaru Musa Yar’adua ya yi mata takarar shugaban ƙasa a zaɓen da aka gudanar a ranar 21 ga watan Afirilu shekara ta 2007 tare da Dr. Goodluck Ebele Jonathan a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, inda ya sami nasara a kan Janar Muhammadu Buhari da Edwin Ume Ezeoke na Jam’iyyar ANPP da kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar wanda ya fita daga Jam’iyyar PDP ya shiga wata Jam’iyya mai suna ACN. Bayan gudanar da zaɓe da sanar da sakamakon zaɓe da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa bayyana cewa Alhaji Umaru Musa Yar’adua ne ya lashe zaɓen, shi kansa Umaru Musa Yar’adua daga baya ya bayyana cewa, zaɓen na tattare da manyan matsaloli waɗanda gwamnatinsa za ta gyara a zaɓuka masu zuwa. Gwamnatin Malam Umaru Musa Yar’adua ta yi ƙoƙari na a zo gani wajen gyara al’amuran da suka shafi shugabanci a Nijeriya, amma Allah bai ba shi ikon ganin an gyara abubuwa ba. Allah Ya karɓi rayuwar Malam Umaru Musa Yar’adua a ranar 5 ga watan Mayu shekara ta 2010, inda aka rantsar da mataimakinsa Goodluck Ebele Jonathan a matsayin sabon shugaban ƙasa wanda zai ƙarasa mulkin marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar’adua, sannan aka ɗauko gwamnan jihar Kaduna Malam Namadi Sambo aka ba shi mataimakin shugaban ƙasa.

    A zaɓen shekara ta 2011 an sami taƙaddama a Jam’iyyar PDP kan wanda ya kamata ya zama shugaban ƙasa, wasu na cewa wanda yake kan kujerar ya yi takara wasu kuma na cewa damar ta Arewacin Nijeriya ce, tun da Kudancin Nijeriya sun yi mulki na shekara takwas, an zaɓi ɗan Arewa bai cika shekara huɗu ta farko ba ya rasu, kamata ya yi a zaɓi wani ɗan Arewa don ya iyar da mulkin. Daga ƙarshe dai aka sasanta aka bar wa Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya yi takara. Da farko an tsayar da ranar 9 ga watan Afirilu, 2011, amma saboda wasu matsaloli hukumar zaɓe ta sauya ranar zaɓen zuwa 16 ga watan Afrilu, 2011. An gudanar da zaɓe inda shugaba mai ci Goodluck Jonathan da mataimakinsa Malam Namadi Sambo na Jam’iyyar PDP suka sami nasara a kan Janar Muhammadu Buhari da mataimakinsa Pastor Tunde Bakare na jam’iyyar CPC da kuma Malam Nuhu Ribadu da mataimakiyarsa Fola Adeola. Ana sanar da sakamakon zaɓe sai rikici da ƙone-ƙone suka ɓarke a Arewacin Nijeriya saboda ana zargin yi wa Janar Buhari maguɗin zaɓe, amma duk da haka masu sa idanu kan yadda aka gudanar da zaɓen na cikin gida da waje sun bayyana an gudanar da ingantaccen zaɓe a Kudancin Nijeriya inda Jam’iyyar CPC take zargin an yi mata maguɗin zaɓe. Sakamakon wannan zaɓe an yi asarar dukiya da rayuka a sassa daban-daban na Tarayyar Nijeriya.

    Zaɓen shekara ta 2015 an yi takara tsakanin shugaba mai ci Dr. Goodluck Jonathan da mataimakinsa Malam Namadi Sambo a Jam’iyyar PDP da kuma Janar Muhammadu Buhari da mataimakinsa Professor Yemi Osubanjo na jam’iyyar APC. Tun lokacin da Buhari ya fara takarar zaɓe a shekara ta 2007 zuwa 2015 farin jininsa sai ƙaruwa yake, musamman da ya yi haɗin gwiwa da wasu manyan jam’iyoyi a zaɓen 2015. Wannan kuwa ya faru ne saboda mutane sun yanke hukunci babu wanda zai iya ceto Nijeriya daga halin da take ciki sai Buhari. Saɓanin sauran zaɓuɓɓuka da suka gabata, zaɓen 2015 an gudanar da shi a ranakun 28 da 29 ga watan Maris na shekara ta 2015. Hukumar zaɓe ta ƙasa ta bayyana Janar Muhammadu Buhari da mataimakinsa Professor Yemi Osibanjo ne suka sami nasara a zaɓen, inda suka kayar da shugaban ƙasa mai ci Dr. Goodluck Ebele Johathan da mataimakinsa Malam Namadi Sambo na jam’iyyar PDP. Shugaban ƙasa mai ci ya amince an kayar da shi, inda ya kira Janar Muhammadu Buhari ta waya ya taya shi murna kuma ya sanar da duniya ya amince an kayar da shi a zaɓen. Da shi shugaba Dr. Goodluck Ebele Jonathan da mataimakinsa Malam Namadi Sambo sun miƙa mulki ga waɗanda aka zaɓa Janar Muhammadu Buhari da Professor Yemi Osinbajo a ranar 29 ga watan Mayu, 2015.

     A zaɓen shekara ta 1999 an yi takara tsakanin shugaba mai ci Janar Buhari Muhammadu Buhari da mataimakinsa a ƙarƙashin jam’iyyar APC da kuma Alhaji Atiku Abubakar (tsohon mataimakin shugaban ƙasa Obasanjo) da mai rufa masa baya Peter Obi ƙarƙashin jam’iyyar PDP. An shirya gudanar da wannan zaɓe a ranar 16 ga watan Fabrairu, 2019, amma saboda wasu matsaloli hukumar zaɓe ta ƙasa ta sauya ranar zuwa 23 ga watan Fabrairu, 2019. Saboda wasu matsaloli da aka fuskanta a lokacin gudanar da zaɓena a wasu sassa na Tarayyar Nijeriya zaɓen ya kai har ranar 24 da watan Fabrairu, 2019. Bayan an kammala tattara sakamakon zaɓe, hukumar zaɓe ta ƙasa ta bayyana shugaba mai ci Janar Muhammadu Buhari da mataimakinsa Professor Yemi Osinbajo na jam’iyyar APC matsayin waɗanda suka sami nasara a kan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar da mai biye masa baya Peter Obi na jam’iyyar PDP. An bayyana cewa, an kashe kuɗi masu ɗimbin yawa wajen gudanar da wannan zaɓe fiye da duk wani zaɓe da aka gudanar tun daga shekara ta 1999, inda aka ƙiyasta kashe kimanin Naira Biliyan Sittin da Tara.

    A wannan wata na Oktoba na shekara ta 2022 saura watanni biyar suka rage a sake gudanar da wani zaɓen a watan Fabrairu na shekara ta 2023. Jam’iyyun siyasa sun tsayar da waɗanda za su yi masu takara a madafun iko daban-daban a zaɓen 2023. Jam’iyyar APC wadda take riƙe da mulki a wannan ƙasa ta tsayar da tsohon gwamnan Jihar Lagos Alhaji Bola Ahmed Tinubu da Senator Kashim Shattima a matsayin waɗanda za su yi mata takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa. Ita kuma PDP ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar da gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin waɗanda za su yi mata takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa. Al’amarin bai tsaya nan ba, don kuwa sabuwar jam’iyya mai suna NNPP da tsohon gwamnan jihar Kano ya kafa ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa, ita kuma jam’iyyar LP ta tsayar da Peter Obi da Dr Datti Ahmed a matsayin waɗanda za su yi mata takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa. Abin da ya rage mu roƙi Allah Ya kai mu lokacin lafiya kuma ya yi muna zaɓi da mafi alheri.

    Waiwaye Adon Tafiya: Shugabanci a Ƙasar Hausa a Wannan Zamani Ina Mafita?

    Kamar yadda bayanai suka gabata, an yi bayanai dangane da shugabanci a ƙasar Hausa da ma Tarayyar Nijeriya gaba ɗaya tun tsarin shugabanci na gargajiya aka zo lokacin addinin Musulunci da shigowar Turawa ƙasar Hausa da kafuwar mulkin mallaka a Tarayyar Nijeriya da kuma bayan samun ‘yancin kai har zuwa wannan zamani na mulkin siyasa ta demokraɗiya wadda Turawa suka kawo a wannan ƙasa. Idan muka nazarci yadda aka gudanar da waɗannan shugabanci musamman shigowar Turawa da irin yadda suka mallake al’ummomin da a yau suke zaune ƙasar da ake cewa Nijeriya, za a ga sun kawo wasu sauye-sauye waɗanda ta wata fuska sun kawo cigaba, amma ta wata fuska tawaya suka kawo wa wasu al’ummomi musamman Hausawa a wannan zamani. Lokacin da Turawa suka shigo ƙasar Hausa sun tarar da Hausawa suna da ingantaccen tsarin da suke tafiyar da harkokinsu waɗanda suka shafi shugabanci da addini da zamantakewa da hanyoyin bunƙasa tattalin arziki da sauransu. Sakamakon shigowarsu ya taimaka matuƙar gaske wajen ruguza waɗannan muhimman fannonin rayuwa na Hausawa musamman abubuwan da suka danganci shugabanci da zamantakewa da tattalin arziki. Idan muka ɗauki shugabanci, kafin shigowar Turawa ƙasar Hausa a dunƙule take ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, kuma dukkan sarakunan da suke sauran garuruwan ƙasar Hausa na yin biyayya gare shi. Shigowar Turawa ta sa suka ruguza wannan tsari, inda dukkan sarakunan ƙasar Hausa suka koma ƙarƙashin Razdan-Razdan har zuwa lokacin da suka mayar da mulki ga ‘yan ƙasa a shekara ta 1960. Samun ‘yancin kai bai kawo wani sauyi ba wajen mayar wa sarakuna darajarsu ba, sai ma a shekara ta 1976 lokacin mulkin Obasanjo aka ƙara rage masu daraja sakamakon sabon tsarin ƙananan hukumomi. Duk da kasancewar tun daga lokacin da aka sami ‘yancin kai har zuwa wannan zamani gwamnatoci a matakai daban-daban suna bayyana kawo sauye-sauye da tsare-tsare da ƙudurce-ƙudurce waɗanda za su kawo haske wajen ingantuwar shugabanci a ƙasar Hausa da sauran sassan Tarayyar Nijeriya, amma a kullum al’amarin sai ƙara ɓaci yake yi. A taƙaice a iya cewa, sakamakon siyasar zamani da Turawa suka kawo ƙasar Hausa da sauran sassan Nijeriya a kullum shugabanci da yadda ake tafiyar da shi ƙara taɓarɓarewa yake. Babu abin da yake a gaban shugabanni sai hanyar da za su bi su ci zaɓe ko ta wane hali. Ana amfani da kuɗi fiye da ƙima wajen sayen masu jefa ƙuri’a, ana ƙwace ƙuri’ar zaɓe da tsiye, ana wulakanta mutane tare da kashe wasu don a ci zaɓe. Waɗannan dalilai ne suka sa a yanzu dukkan shugaban da ya gama mulkinsa idan wani ya hau sai a riƙa cewa, “ƙara jiya da yau”.

    Ta fuskar zamantakewa kullum al’amarin sai ƙara ɓaci yake yi yadda al’ummar ƙasar Hausa ba su zaune lafiya. Shugabanni sun ƙi ɗaukar matakin da ya dace wajen maganin marasa kishin ƙasa da ɓarayi da ‘yan fashi da makami da ‘yan ta’adda da masu sace mutane don a ba su kuɗin fansa da ma’aikatan gwamnati masu satar dukiyoyin mutane a ofisoshi don amfanin kansu da na iyalansu. Wannan al’amari ya haifar wa ƙasar Hausa da wasu sassa na Tarayyar Nijeriya munanan abubuwa waɗanda suka taimaka ruguza tattalin arzikin wannan ƙasa, yadda a yau akwai al’ummomi a sassa daban-daban na wannan ƙasa da aka kora daga gidajensu, suka koma wasu wurare inda babu abinci babu sutura babu abubuwan yi, babu zaman lafiya, farashin kayan masarufi da za a riƙa amfani da su yau da kullum suna tashin gwabron zabo. Waɗannan dalilai sun sa wasu mutane sun mutu saboda yunwa ko azaba ko fargaba.

    Malamai da almajirai da sauran al’umma ba su gajiya ba wajen faɗakar da al’umma ta hanyar wa’azi dangane da illolin waɗannan abubuwa. Wannan tsanani ya sa malamai suke ta yin kira ga al’umma a koma ga Allah, a tuba a roƙe shi a kuma sauya halaye daga munana zuwa kyawawa don Allah Ya kawo muna sauƙi.

    Dangane da haka ne ya sa na ga ya dace in ba da tawa gudummuwa wajen kawo sauƙin halin da ƙasar Hausa take ciki. Gudummuwa ta ita ce, matuƙar ana son a sami ingantaccen shugabanci a ƙasar Hausa a wannan zamani yana da matuƙar muhimmanci a waiwaya baya don nazarin maƙalar Usul Al-Siyasa dangane da yadda ta fito da manufofin da suka kamata shugabanni da waɗanda ake shugabanta za su bi don samun ingantacciyar al’umma. Koyi da waɗannan dasussa za su taimaka wa shugabanni a sami ingantaccen shugabanci a ƙasar Hausa a wannan zamani.

    Maƙalar Usul Al-Siyasa da Ire-Iren Darussan da Suka Kamata a yi Koyi da su

    Kamar yadda aka bayyana a gabatarwa, maƙasudin wannan takarda shi ne, ta yi nazarin maƙalar Usul Al-Siyasa dangane da ire-iren darussan da suka kamata shugabanin wannan zamani da sauran al’ummar da ake shugabanta suka kamata su yi koyi da su yadda za a sami ingantacciyar al’umma a ƙasar Hausa a wannan zamani. Dangane da haka, yana da matuƙar muhimmanci kafin mu shiga cikin wannan nazari mu san wane ne Malam Ummarun Dallaje? Wace irin dangantaka take tsakaninsa da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da ɗansa Sarkin Musulmi Muhammadu Bello?

    Shi Malam Ummarun Dallaje ya fito daga zuru’ar Fulani Dallazawa waɗanda mabambanta ra’ayoyin masana suka gaza wajen tsayar da matsaya ɗaya kan asalin wurin da suka fito. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon rashin samun wani ingantaccen rubutu da ya adana tarihin mafi yawancin al’ummomin Afirika ba wai Dallazawa ko Fulani ba. Dangane da haka, wasu masana irin su Ɗankoussou, (1970: 134-5) da Dr. Yusuf Bala Usman, (1972:190-191), suna da ra’ayin cewa, Dallazawa sun shigo ƙasar Katsina daga gabacin ƙasar Hausa, inda suka kafa ƙauyen Dallaje ta ƙasar Bindawa. Dr. Bala Usman ya ƙara da bayyana cewa, a nan ne Abdulmumini ɗan Muhammadu Goshi mahaifin Malam Ummarun Dallaje ya zauna a farkon ƙarni na goma sha takwas, kuma ya kasance limamin garin. An ƙara da bayyana cewa, a nan Dallaje ne aka haifi Malam Ummarun Dallaje.

    Malam Ummarun Dallaje, ya fara karantunsa a gidansu wajen mahaifinsa kafin daga baya ya fita yawon neman ilimi. Ya yi karatu a wajen malamai da dama har da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da kansa da kuma ɗansa Muhammadu Bello. Bisa ga shakuwarsu da waɗannan manyan malamai ta sanya ya riƙa bin su garuruwa daban-daban na ƙasar Hausa wajen gudanar da wa’azin addinin Musulunci ciki har da Birnin Katsina. Haka kuma, Malam Ummarun Dallaje na daga cikin dakarun da suka gudanar da yaƙe-yaƙen jihadin da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya jagoranta.

    Kamar yadda bayanai suka gabata, Malam Ummarun Dallaje na daga cikin waɗanda Shehu Ɗanfodiyo ya ba tuta don ya zo Katsina ya yaƙi sarakunan Haɓe na Katsina. Kafin Malam Ummarun Dallaje ya baro Sakkwato, sai ya roƙi Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rubuta masa wata maƙala wadda za ta zama jagora gare shi wajen aiwatar da mulkin al’ummar ƙasar Katsina. Sarkin Musulmi ya aminta da bukatar Malam Ummarun Dallaje inda ya rubuta masa shahararriyar maƙala wadda ya sanya wa sunanUsul Al-Siyasa wadda ta ƙunshi manyan manufofi guda bakwai waɗanda suka rataya a kan kowane shugaba na Musulmi don gudanar da mulki na adalci tsakanin al’ummarsa. An rubuta wannan maƙala kimanin shekara 216 da suka gabata, wato a shekara ta 1806. Duk da daɗewar wannan maƙala idan aka yi nazarin ta a yau, sai a yi tsammanin ba ta wuce shekara biyu da rubutawa ba. Dalili kuwa shi ne, abubuwan da suke ƙunshe cikinta kamar an rubuta su ne saboda al’ummar wannan zamani, ba al’ummar lokacin da aka yi jihadin Shehu Ɗanfodiyo ba. Wannan al’amari ya ƙara bayyana cewa, shi addinin Musulunci addini ne na kowane zamani, wato jiya da yau da kuma gobe.

    Kafin ya shiga cikin bayani a kan manufofin da yake so Malam Umarun Dallaje ya yi amfani da su wajen gudanar da mulki a ƙasar Katsina, sai da Sarkin Musulmi ya fara da yin doguwar shimfiɗa mai ratsa zuciya inda ya fara ambaton Ummarun Dallaji a matsayin daɗaɗɗen aboki wanda yake kamar ɗan’uwa na jini, kuma mutum mai gaskiya da riƙon amana da yin ayyuka domin neman sakamako daga Allah. Daga nan, sai ya yi masa addu’a yana roƙon Allah Ya taimake shi bisa ga gudanar da mulkinsa, Ya ba shi tsawon kwana bisa ga wannan shugabanci da zai yi, sannan kuma ya ƙara da roƙon Allah Ya ƙara nunnuka yawan masu goyon bayansa. Daga nan sai wannan maƙala ta ci gaba da shimfiɗa kamar haka:

     “Daga nan na amsa masa bukatarsa, na nemi taimako daga Allah, don kuwa shi ne tushen dukkan wani taimako. “Ka sani ya kai ɗan’uwa, babbar ƙaddarar da za ta faɗa a kan bawan Allah, ita ce, a ba shi shugabancin jama’a, domin kuwa ka sani, za a tambayi kowane mutum abin da bakinsa ya faɗa, ayyukan da ya yi, da abubuwan da suka biyo bayansu. Idan ya kasance shi shugaba ne, za a ƙara da tambayar sa yadda ya gudanar da mulkinsa tsakaninsa da talakawansa. Idan ya kasance ba ya iya sauke nauyin kansa, to, ta yaya zai iya sauke nauyin jama’ar da take ƙarƙashinsa? Dangane da haka ne wasu suke cewa, dukkan wanda Allah bai ɗora masa wani nauyi na shugabanci ba ya ƙara yi maSa godiya, don Ya sauke masa nauyin da za a tambaye shi yadda ya gudanar da shi. Saboda haka, Allah Ya cece shi daga fitunun duniya, don kuwa babu kome cikinta sai tashin hankali da azabtarwa a gobe lahira”.

    Saboda matsalolin da suke tattare da shugabanci ne, ya kawo wani hadisin Annabi, inda yake cewa:

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya tambayi sahabbansa, “ko kuna son in gaya maku wani abu dangane da shugabanci”? Sai suka amsa masa da cewa: “Ya Manzon Allah muna so”. Daga nan sai ya ce: “Farkon shi akwai kushewa, tsakiyarsa, akwai nadama. Ƙarshensa kuma, akwai azaba a ranar lahira”.

    A wannan maƙala Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ya ci gaba da bayanin cewa:

    “Wanda Allah, Maigirma da Ɗaukaka, Ya ba shi shugabanci, to, ya yi iya ƙoƙarinsa don ganin ya sauke dukkan nauyin da yake a kansa, ta hanyar ba dukkan al’ummomin da suke ƙarƙashinsa haƙƙoƙinsu”.

    Kyawawa da Munanan Abubuwan da Suke Tattare da Shugabanci

    Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya bayyana cewa, duk da yake shugabanci abu ne mai nauyi da wuyar ɗauka, amma duk da haka nan, kyauta ce babba. Dukkan shugaban da ya yi wa Allah godiya, ya kuma sami nasarar sauke nauyin shugabanci, to, zai sami babban rabo wanda ba a iya misalta shi. Haka kuma, dukkan shugaban da bai yi wa Allah godiya ba, ya kasa sauke nauyin shuganci, zai fuskanci matsananciyar uƙuba wadda ba ta misaltuwa.

    Dangane da haka ne ya kawo hadisai masu yawan gaske waɗanda suka bayyana matsayi da hukuncin da ke kan shuganni masu adalci da marasa adalci kamar haka:

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya ce: “A ranar Lahira, babu wata inuwa ko wurin hutawa, sai inuwar Allah. A wannan rana mutane bakwai ne kawai za su sami wannan inuwa; shugaba adali wanda ya gudanar da mulkinsa kamar yadda shari’a ta shimfiɗa, sai saurayi wanda ya girma yana bautar Allah, sai ɗan kasuwa wanda a lokacin da yake gudanar da kasuwancinsa hankalinsa yana masallaci, mutane biyu waɗanda suke ƙaunar junansu saboda bautar Allah da suke yi, sai kuma mutumin da a duk lokacin da ya kaɗaita yana bautar Allah, idan ya tuna Allah, sai ya yi ta zubar da hawaye, sai kuma mutumin da wata mata kyakkyawa wadda yake so, ta kaɗaice da shi, ta kuma bukace shi da ya yi lalata (zina) da ita, amma sai ya ƙi amincewa, ya bayyana mata, ‘ina tsoron fushin Allah Maigirma da ɗaukaka’, sai kuma mutumin da ya ba da sadaka don Allah, ba don riya ba, har ta kai lokacin da zai bayar da sadakar hannunsa na hagu bai san abin da hannunsa na dama ya yi ba”.

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya ce: “Wanda Allah Ya fi so, kuma wanda yake kusa da Allah, shi ne shugaba adali, wanda Allah ba Ya so, kuma wanda yake nesa da rahamar Allah, shi ne azzalumin shugaba”.

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya ce: “Na rantse da wannan wanda rayuwata take a hannunsa, cewa, ayyukan alherin shugaba adali ana tattara su a Aljanna daidai da ayyukan alherin da dukkan talakawansa suka aikata. Haka kuma, idan aka ba da lada ɗaya ga ibadar da talakawansa suka yi, shi ana ba shi lada 70, 000 sakamakon dukkan ibadar aiki ɗaya da ya yi kwatankwacin wadda talakawansa suka yi.

    An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas, Allah Ya yarda da su, ya ce: “Wata rana Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya zo ya tsaya a bakin ƙofar Ka’aba, daga cikin Ka’aba kuma ‘yan ƙabilar Ƙuraish masu yawa, sai ya ce masu, ‘Ya ku shugabanin Ƙuraysh, ku yi abubuwa uku ga waɗanda kuke shugabanta; idan sun bukaci adalci, ku yi musu; idan sun bukaci sasanci, ku sasanta su kamar yadda shari’a ta shimfiɗa a yi; idan kuma kuka yi musu alƙawari, to ku cika alƙawarinku kada ku saɓa. Ya Allah, Kai da Mala’ikunka ku la’anci wanda ya kauce wa wannan tsari. Allah Maigirma da ɗaukaka ba ya amsar ayyukan farilla da na nafila na dukkan mutumin da ya kauce wa wannan tsari”.

    Darussan da Suka Kamata a Koya Daga Wannan Shimfiɗa

    Idan muka nazarci waɗannan bayanai da aka tsakuro daga wannan shimfiɗa, za a fahimci cewa, shugabanci a addinin Musulunci al’amari ne mai matuƙar muhimmanci, wanda idan aka tafiyar da shi kamar yadda shari’a ta shimfiɗa al’umma za ta zauna lafiya a kuma sami ƙaruwar arziki da fahimtar juna. Babbar hanyar da za a sami wannan biyan bukata ita ce, shugabanni su zama masu adalci ga waɗanda suke shugabanta. Dangane da haka, akwai darussa da dama daga wannan shimfiɗa ta kawo. Waɗannan darussa sun haɗa da:

    ü  Wani babban darasi da wannan shimfiɗa ta kawo shi ne, ire-iren tanadin alheri da Allah Ya ajiye wa shigabanni masu adalci, sannan kuma an kawo ire-iren azabar da Allah Ya tanada wa shugabannin da ba su gudanar da ingantaccen shugabanci ba.

    ü  Yana daga ciki darussan wannan maƙala, idan shugabanni suka yi waɗanda suke shugabanta alƙawari su cika kar su saɓa. Cikar alƙawali na daga cikin siffofin da ake a gane mutumin kirki.

    Manufofi Bakwai na Gudanar da Ingantaccen Shugabanci

    Ya fara da bayyana cewa, yana da matuƙar muhimmanci a sani manufofin ingantaccen shugabanci suna tattare da ma’anar dukkan abin da ake kira adalci. Domin shi shugabanci ma’anarsa ita ce adalci ba daɗi ba ƙari. Daga cikin waɗannan manufofi bakwai na shugabanci, biyu suna jiɓanta ne ga shugaba, wato sarki ko gwamna ko limami. Biyu kuma sun jiɓanta ne a kan waɗanda suke taimaka wa shugaba da sauran ma’aikata. Cikon ukun kuma suna jiɓanta ne ga talakawa waɗanda ake shugabanta.

    Manufa ta Farko

    Manufa ta farko ta bayyana cewa, ya zama dole ga dukkan shugaba ya zama:

    1.      Mutum mai matuƙar biyayya ga addininsa da tsoron Allah.

    2.      Mutum mai matuƙar biyayya ga sunnoni Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi.

    3.      Mutum mai tunanin abubuwan da za su kasance a ranar lahira.

    4.      Mutum wanda zai tsaya kan abubuwan da Allah Ya yi ummurnin a yi da waɗanda ba su dace a yi ba.

    5.      Mutum wanda yake kauce wa dukkan abubuwan duniya.

    6.      Mutum wanda yake kawar da zuciyarsa daga sha’awar shugabanci ko ta halin ƙaƙa.

    Idan ya kasance shugaba ba wanda yake tsoron Allah a cikin addininsa, kuma bai damu da sakamakon ranar lahira ba, zai jefa kansa da waɗanda yake shugabanta a mummunar turba wadda ta yi saɓani da sunnonin Annabi. Wannan ita ce babbar matsalar da ta dabaibaye shugabannin wannan zamani kuma kowa ya san haka. Mafi yawancin shugabanni sun gina tilasta shugabantar al’ummominsu bisa tsari na al’adun gargajiya da suka gabata, sannan kuma suka dauwama cikin rayuwa ta cin hanci da rashawa kamar yadda mahaifansu da magabatansu suka gudanar. Sun ci gaba da shugabantar al’ummominsu bisa wannan tsari ba tare da la’akari da koyarwar shari’a ba. Haka kuma, ba su amfani da cancanta wajen ba da amanar da Allah Ya ɗora a ba masu ilimi da tsoron Allah, maimakonsu sai su ba da ta ga jahilai na kusa da su waɗanda ba su san kome na addini da tsoron Allah ba.

    Idan ya kasance shugaba mai son shugabanci ko ta wane hali, zai iya kawo wa kansa da al’ummar da yake shugabanta abubuwa marasa kyau waɗanda za su iya cuta musu. Dangane da haka, ya kamata a fahimci cewa, hanyoyin magance matsalolin shugabanci sun haɗa da, a ba da shugabanci ga mutumin kirki mai tsoron Allah. Idan wani mutum daga cikin al’umma ya bayyana yana son shugabanci ko ta wane hali, ya kamata mu fahimci bai cancanta ba. Dukkan wanda ya yarda ya ba shi shugabanci, ya sani ya yi babban kuskuren da ya saɓa wa shari’a, don kuwa ya ɗora wani abu a wurin da bai dace ba. Duk da kasancewar shugabanci al’amari ne wanda ake aiwatarwa ta hanyar yi yau da kullum, kuma ana iya fuskantar matsaloli, amma duk da haka, babban maƙasudi shi ne, a tabbatar da tsare doka da oda yadda dukkan al’ummar duniya za su zauna lafiya ta hanyar tsare dokokin Allah.

    Ya zama dole a fahimci cewa, matuƙar babu ingantaccen shugabanci a tsakanin al’umma wadda take fuskantar matsaloli, babu mutumen da zai zauna lafiya gidansa, ko garinsu ko ma ƙasa baki ɗaya. Bisa wannan dalili ne babu wanda yake da izinin karɓar kuɗin ƙasa daga manoma. Domin biyan bukatun al’umma ya zama dole a zaɓa musu shugabanni a ko’ina cikin duniya waɗanda ake da yaƙinin za su yi shugabanci na adalci a tsakanin al’ummominsu. Matuƙar babu shugabanci al’ummomi za su zauna kara-zube kowa ya yi abin da ya ga dama, don ya san ba wanda zai tsawata masa. Wannan zai haifar da mutane su riƙa kashe junansu ba tare da tunanin wani zai tuhumce su ba. Sakamakon haka ne, masana suka bayyana cewa, babu wanda ke da hakkin kashe wani sai hukuma wadda za ta bincika ta gano laifi kuma laifin ya kasance hukuncin shi a kashe wanda ya yi laifin.

    Darussan da Suka Kamata a Koya

    Wannan manufa ta fito da bubuwa da dama waɗanda suka dace shugabanni su yi koyi da su kamar haka:

    ü  Darasi na farko shi ne dole shugabanni su zama masu tsoron Allah wajen gudanar da dukkan al’amuransu na duniya da lahira.

    ü  Darasi na biyu shi ne dole shugabanni su riƙa yin koyi da sunnonin Annabi wajen tafiyar da dukkan abin da ya shafi rayuwarsu ta duniya da lahira.

    ü  Wani darasi da wannan maƙala take koyarwa shi ne, kar a nemi mulki bakin-rai-baki-fama, idan Allah Ya ba mutum mulki, ya yi adalci tsakaninsa da waɗanda yake shugabanta.

    ü  A tsare dokokin Allah sau-da-ƙafa ba tare da kauce wa dukkan abin da Shari’a ta yi hani a yi. Dukkan wanda ya saɓa dokokin Allah a hukunta shi kamar yadda sharia’a ta tsara ba tare da nuna fifiko tsakanin al’umma.

    Manufa ta Biyu

    Manufa da biyu ta bayyana cewa, dukkan shugaba dole ne ya zama:

    1.      Yana da halayen zamantakewa masu kyau.

    2.      Ya zama yana zaune lafiya da al’ummarsa kuma ya zama mai yafiya.

    3.      Ya zama ba shi da saurin fushi.

    4.      Ya zama yana da alkunya da karimci da dauriya.

    5.      Ya zama yana da kyakkyawan hali.

    6.      Ya zama mai sauƙin hali da fahimtar al’amurra, mai ƙarfin hali da baiwa ga talakawansa.

    Dukkan shugaban da ya kasance zamantakewa tsakaninsa da talakawansa ba ta da kyau, kuma ba ya zaune lafiya da su, sannan ya kasance mai saurin fushi, kuma halayensa ba su da kyau, to ana tsoron talakawansa ba za su gamsu da shugabancinsa ba, kuma ba za su ba shi haɗin kai wajen tafiyar da shugabancin ƙasar ba. Dangane da haka ne, Allah Maigirma da Ɗaukaka Yake cewa:

    “Yana daga cikin rahamar Allah ku yi hulɗa mai sauƙi da su. Idan kuka kasance masu tsanani ko taurin kai, sai su kauce muku. Saboda haka, idan suka yi kuskure ku yafe musu’’.

     

    Idan ya kasance shugaba ba shi da ƙarfin hali, ana tsoron amanar da aka ɗora masa ya sami karayar zuciya wadda za ta sa ya gaza wajen sauke wannan nauyi da aka ɗora masa. Idan kuma shugaba ya kasance mai riƙe hannunsa ne, ana tsammanin ba zai sauke nauyin da aka ɗora masa ba wajen isar da haƙƙin al’umma a kan bukatunsu da suke kansa ba na ayyukan cigabansu da ƙasa baƙi ɗaya. Sakamakon haka, talakawan da yake shugabanta za su yi tunanin ba shi da amfani wajen su, kuma shugabancinsa ba shi da amfani.

    Darussan da Suka Kamata a yi Koyi da su

    Darussan da suka kamata a koya daga wannan manufa sun haɗa da :

    ü  Shugabanni su kasance masu kyawawan halaye da riƙa yin hulɗoɗin rayuwa da waɗanda suke shugabanta.

    ü  Darasi an biyu da ya kamata shugabanni su yi koyi da su shi ne, yana da matuƙar muhimmanci ga shugabanni su zama masu ƙarfin hali wajen shugabantar al’umma.

    ü  Wani darasi da wannan maƙala take koyarwa shi ne, yana da matuƙar muhimmanci ga shugabanni da su riƙa tausaya wa waɗanda suke shugabanta, su kuma ji tausayinsa, su kyautata masu.

    Manufa ta Uku

    Manufa ta uku ta bayyana cewa, ya zama dole ga kowane shugaba da a kowane lokaci ya kasance yana tare da malamai masana addinin Musulunci kusa da shi, ya ajiye hankalinsa wajen sauraren shawarwarinsu kuma ya riƙa amfani da su. Ya nesanta kan shi daga malaman neman duniya waɗanda ba kyautata wa al’umma ke gabansu, abin da za su samu kaɗai ke gabansu. Domin ku sani, su malaman neman duniya za su riƙa kambama shugaba suna yaba masa, suna nuna babu kamarsa domin kawai su sami wani abu daga gare shi. Su kuwa malamai masana addini ba suna shawartar shugaba don ya ba su wani abu ba, suna yi ne don su tabbatar shugaba na gudanar da shugabanci tsakanin al’ummarsa bisa koyarwar shari’ar addinin Musulunci.

    An bayyana cewa, Shaƙeeƙ Balkhi, Allah Ya yi rahama a gare shi, a wata rana ya ziyarci Sarki Haruna Rashid, sai Sarki Haruna ya ce, “kai ne Shaƙeeƙ, mutum mai kamala da tsan-tsan da abin duniya, wanda ya kauce wa aikata dukkan wani saɓo saboda tsoron Allah da kuma biyayya ga addinin Allah”. Daga nan sai ya amsa masa da cewa, “ba haka nake ba”. Sai Sarki Haruna ya ce masa, “ka ba ni shawara mai kyau”. Sai ya ce ce da shi, “Ka sani ya kai wanna shugaba, Allah Maigirma da Ɗaukaka, ya ɗora ka bisa kujerar mulki irin wadda ya ɗora Sayyidina Abubakar saboda ya kasance mai gaskiya da tausayi, don kai ma ka yi haka. Haka kuma, Allah Ya ɗora maka girma irin na Sayyida Umar don ka tantance tsakanin ƙarya da gaskiya kamar yadda Umar ya yi. Sannan kuma Allah Ya ba ka shugabanci irin wanda ya ba Usmanu Zul-Nurayn, saboda ka zama mai kara da alkunya da kyautatawa kamar yadda Usmanu ya yi. Bayan nan Allah Ya aza ka a matsayin Sayyidina Aliyu Ɗan Abi Talib, don ka kasance mai ilimi wanda zai ba kowa haƙƙinsa kamar yadda Ali ya yi”. Daga nan, Sarki Haruna Rasheed ya ƙara ce masa, “ƙara min wasu shawarwarin masu kyau . Sai Shaƙeeƙ ya amsa da cewa, “Ka sani ! Fahimci cewa, Allah Maigirma da Ɗaukaka, yana da wata madauwama wadda ya kira da sunan Jahannama, sannan kuma Ya ba ka ƙofofin shiga wannan madauwama. Haka kuma, Allah Ya ba ka abubuwa uku:

    1.      Baitulmali don ajiye dukiyar al’umma.

    2.      Bulala.

    3.      Takobi.

    Ya ƙara da bayyana cewa, “Allah Ya ba ka damar da za ka tseratar da al’ummarka daga shiga Jahannama ta hanyar waɗannan abubuwa uku da aka kawo a sama. Saboda haka, dukkan mutumen da ya zo wajen ka neman taimako kar ka hana shi don maganin kar ya taɓa kayan da ba nasa ba. Dukkan wanda ya saɓa dokar Allah, ka hukunta shi da bulala. Dukkan wanda ya kashe wani ba tare da hukuncin shari’a ba, ka sare kansa da takobi bisa amincewar waɗanda aka kashe wa ɗan’uwa. Idan ka ƙi amfani da waɗannan shawarwari, ka sani, kai za ka zama jagoran waɗanda za su shiga Jahannama, kuma na gaba-gaba cikin waɗanda za su dauwama a cikinta”. Sarki Haruna ya ƙara ce masa, “ka ƙara ba ni wasu shawarwarin”. “Hakika a wannan duniya, sha’awar ka za ta zama kamar ruwan da yake ɓuɓɓugowa, sannan kuma sauran ma’aikata masu taimaka maka, za su zama kamar ƙoramu ko ƙananan hanyoyin ruwa. Idan ya kasance ruwan da yake ɓuɓɓugowa ya zama fari mai kyau, kuma bai gurɓata da kome, zai kwarara cikin ƙananan ƙoramu ko hanyoyin ruwa ba tare da ya sauya kamanni ko ɗanɗano ko ƙamshi ba. Dangane da haka, idan shugaba ya ɗauko masu taimaka masa waɗanda suke da ilimi na tsoron Allah, amma ya ƙi ɗaukar shawarwarinsu, daga nan zai zauna a wajen gudanar da shugabancinsa cike da malamai masu neman duniya, waɗanda za su ɗora shi kan hanyar rashin adalci da cin dukiyar al’umma ba tare da la’akari da yadda shari’a ta yarda a yi ba. Ana sanin nauyin addinin mutum ta hanyar abokinsa da yake hulɗa ta yau da kullum da shi. Haka shi ma shugaba, ana sanin matsayin shugabancinsa ta hanyar waɗanda suke ba shi shawara. Idan mutanen kirki ne suke tare da shi, za su ba shi shawarwari masu kyau, ya rage wurinsa ya yi aiki da su don samun ingantaccen shugabanci ga al’umma”.

    Darussan da Suka Kamata a yi Koyi da su

    ü  Ya zama dole ga shugaba ya jawo masu ilmin addinin Musulunci da masana harkokin shugabanci da na tattalin arziki na wannan zamani don su ba shi ingantattun shawarwari don inganta shugabancinsa.

    ü  Shugabanni su gudanar da mulkinsu ta hanyar koyi da Halifofi Huɗu na Manzon Allah, wato, Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, Allah Ya ƙara yarda da su.

    ü  Shugaba ya yi ƙoƙarin ganin ya ɗora al’ummar da yake shugabanta bisa kyakkyawar turba ta addinin Musulunci yadda Allah zai yi masu rahama su shiga Aljanna ba wutar Jahannama ba.

    ü  Shugaba ya gudanar da ingantaccen shugabanci yadda mataimakansa da talakawansa za su yi koyi da shi, kamar yadda idan ruwa mai kyau ya ɓuɓɓugo daga ƙasa zai kwarara gwanin kyau cikin ƙananan ƙoramu ko magunanun ruwa

    Manufa ta Huɗu

    Bayanin manufa ta huɗu na cewa, abu na farko da ya dace ga kowane shugaba shi ne, adalci da ƙwarewa su zama su ne zai ba fifiko wajen ɗaukar waɗanda za su taimaka masa wajen gudanar da shugabanci. Ya tabbatar da ya zaɓo ƙwararrun masana masu gaskiya da riƙon amana don ba su muƙamai. Haka kuma, ya riƙa ziyartar wuraren ayyukansu don tabbatar da suna gudanar da ayyukansu kamar yadda aka ɗora masu. An bayyana cewa, Asim ɗan Bahdha, ya ce, “a duk lokacin da Sayyidina Umar ɗan Khattab ya ba wani shugabancin al’umma, zai ɗora masa wasu dokoki waɗanda suka haɗa da; kar ya yi rayuwa irin ta kece-reni da sayen abubuwa masu tsada, kar ya riƙa saka sutura mai tsananin tsada, kar ya riƙa cin abinci mai matuƙar tsada, sannan kuma ya buɗe ƙofofinsa ga masu neman taimako, domin kuwa wannan ne zai ƙara danƙon soyayya tsakaninsa da waɗanda yake shugabanta. Umar zai ƙara faɗa masa cewa, ban zaɓe ka ba don ka zama mai cuta wa talakawa ko cin dukiyarsu ba. Dangane da haka, na zaɓe ka ne don ku yi bautar Allah tare, ku yi sasanci tsakaninsu, ba ka raba kawunansu ba, ka ci ka sha tare da su ba tare da nuna fifiko tsakaninsu ba”.

    Umar ɗan Khattab ya rubuta wa ɗaya daga cikin shahararrun gwamnonin Musulunci na zamaninsa, wato Abu Musa al-Ash’ari, inda ya bayyana masa cewa, gwamnan da ya fi kowane gwamna kwanciyar hankali, shi ne wanda al’ummarsa suke cikin kwanciyar hankali. Matalaucin gwamna kuma shi ne, wanda jama’arsa suke cikin talauci saboda irin yadda yake gudanar da shugabanci bai kawo hanyoyin da za a warware matsalolin tattalin arziki ba. Ka yi hankali da rashin adalci, don kuwa mabiyan ka za su yi koyi da kai. Yana da matuƙar muhimmanci a sani, ya zama dole a dogara ga Allah, a kuma yi hankali wajen tafiyar da shugabancin al’umma. Domin kuwa matuƙar an biye wa jin daɗin duniya zai jefa shugaba aikata rashin adalci, wanda sakamakon haka shi ne wutar Jahannama. Ka sani cewa, wani al’amari mai firgitarwa kuma babban maƙiyi wanda yake ruguza shugaba, shi ne na kusa da shi, wato ma’aikaci ko mashawarci ko ɗan’uwa wanda zai jefa shi cin dukiyar al’umma saɓanin yadda shari’a ta tsara a yi amfani da dukiyar. Ka sani ire-iren waɗannan mutane babu abin da yake gabansu, sai abin da za su samu na biyan bukatunsu ba bayan bukatun al’umma ba. Idan suka fahimci shugabanci zai kuɓuce daga wanda suke yi wa biyayya, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci za su ƙaurace masa su koma wurin wanda suke ganin zai maye gurbin wancan shugaban. Haka kuma, ire-iren waɗannan mutane, idanunsu na wurin da ke da ni’ima, sai su ƙasƙantar da kansu, su durƙusa, su yi biyayya don su samu rabonsu”.

    Darussan da Suka Kamata a yi Koyi da su

    ü  Darasin farko da ya kamata a yi koyi da shi a nan shi ne, ya zama dole ga shugaba wajen ɗaukar ma’aikatan da za su yi aikin gwamnati, ya tabbatar da yin adalci da ɗaukar waɗanda suka dace a ɗauka, ba son zuciya ko alfarma ko a sayi takardar ɗauka aiki.

    ü  Yana da matuƙar muhimmanci ga shugabanni su kauce wa yin ashararanci da dukiyar al’umma ta hanyar gina manyan gidaje a cika su kayan alatu da sayen manya-manyan motoci da dai sauran almubazzaranci da dukiyar al’umma.

    ü  Yana da matuƙar muhimmanci ga shugabanni su nesanta kansu daga sharrin magulmanta waɗanda suke liƙe da mai riƙe da mulki don neman biyan bukatarsu ba ta al’umma ba.

    Manufa ta Biyar

    Manufa ta biyar tana bayyana cewa, yana da matuƙar muhimmanci ga kowane shugaba ya jagoranci mabiyansa ta hanyar yin adalci wanda kowa zai amfana da shi, kuma a kauce wa zalunci. Sannan kuma shugaba ya riƙa gudanar da bautar Allah tattare da waɗanda yake shugabanta, ya nuna musu kyakkyawar soyayya da ƙauna, ya tausaya musu a lokacin da suka shiga wata fitina. A taƙaice hulɗoɗinsa da halayensa da zamantakewarsa, su tafi daidai da hulɗoɗi da halaye da zamantakewar waɗanda yake shugabanta. Idan waɗanda ake shugabanta suka kasance waɗanda suka damu da bautar mahaliccinsu bisa gaskiya da amana, Allah Maigirma da Ɗaukaka zai ƙara ƙarfin hali da jajircewa ga waɗanda suke jagorantar su ingantaccen shugabanci na adalci da kyautata wa waɗanda ake jagoranta. Idan kuwa ya kasance waɗanda ake shugabanta da waɗanda suke shugabantar su, suka yi wa dokokin Allah tawaye da saɓa Masa, Allah zai ba su azzaluman shugabanni marasa tausayi. Allah Maigirma da Ɗaukaka na cewa, “shin ban ɗora a kansu shugabanni azzalumai ba”. Yadda kuke haka za ku sami waɗanda za su shugabance ku. Ma’ana, idan kun kasance masu biyayya ga dokokin Allah, waɗanda suke tsoron aikata laifuka, za ku sami waɗanda za su jagorance ku bisa gaskiya da amana da adalci da kyautatawa.

    Darussan da Suka Kamata a yi Koyi da su

    Wannan manufa tana ƙunshe da darussa da dama waɗanda ya kamata a yi koyi da su kamar haka:

    ü  Shugaba ya zama mai adalci ga waɗanda yake shugabanta yadda al’umma za ta goya masa baya a zauna lafiya.

    ü  Talakawa masu bi su kasance suna yi wa shugabanninsu biyayya da yi masu kyakkyawar addu’a yadda za a sami ingantaccen shgabanci. Idan ya kasance waɗanda ake shugabanta ba su da kyawawan halaye, Allah zai ba su shugabanni irin su.

    ü  Talakawa su kasance masu yin biyayya ga dokokin Allah da kuma bin sunnonin Annabi. Matuƙar suka kauce masu Allah zai ba su azzaluman shugabanni.

    Manufa ta Shida

    A wannan manufa an bayyana cewa, yana da matuƙar muhimmanci da dukkan shugaba, ya samar da abubuwan da za su taimaka wa jin ɗadin rayuwa wajen tafiyar da al’amurran duniya da bautar Allah. Haka kuma, ya ƙara bunƙasa sana’o’i da ayyukan hannu da hikimomin al’ummarsa, irin su noma da kiwo da ƙira da saƙa da ɗunki da jima da masu bayar da magunguna da mahauta da massasaƙa da sauran fannonin da za su taimaka wa rayuwa don samun cigaba mai ɗorewa. Ya tabbatar da cewa, a kowane birni da ƙauye da lungu da saƙo akwai masu gudanar da ire-iren waɗannan sana’o’i. Ya kuma ƙara wa mabiyansa damar adana wadataccen abinci don amfani da shi gaba. Ya tabbatar da cewa, ƙauyuka na cikin hali mai kyau ta hanyar samar da ingantattun hanyoyi da magudanun ruwa da gadoji yadda za a sami damar zuwa kasuwanni ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba. Bugu da ƙari, ya buɗe hannuwansa don taimaka wa mabuƙata, kuma ya zama mai karimci ga waɗanda yake shugabanta.

    An bayyana a cikin Jawhara cewa, Ali ɗan Abi Talib, ya ce: “Na hango Umar ɗan Khattab a cikin tsananin rana, Sai na ce masa: Ya kai shugaban muminai, ina za ka? Sai Umar ya amsa masa da cewa: “Ina neman wani raƙumi ne na gwamnati wanda ya tsere”. Sai Ali ya ce masa: “Ka bayyana wani babban al’amari wanda zai zama babban ƙalubale ga dukkan wanda zai gaje ka a matsayin halifa”. Sai Umar ya amsa da cewa: “Ya kai Baban Hassan, kar ka zarge ni. Na rantse da wannan wanda Ya aiko Muhammadu a matsayin Annabi kuma manzo, idan har ‘yar tunkiya ta ɓata a gefen Tekun Maliya, Umar za a zarga a ranar tashin ƙiyama. Babu zaman lafiya ga dukkan wanda ya yi sakaci har dukiyar musulmi ta salwanta”.

    An samo bayani daga Shabrakheeti inda yake cewa: “Wani Annabi daga cikin Yahudawa ya tambayi Allah Maigirma da Ɗaukaka, dalilin da ya sa bunƙasar Daular Farisa duk da kasancewar ta yi shekaru masu yawa a duniya”. Sai Allah Maigirma da Ɗaukaka, Ya amsa masa da cewa: “Sun bunƙasa albarkar ƙasa da na ba su”. Dangane da haka, bai dace ga shugaba ba ya cusa wa mabiyansa abubuwan da ba su da amfani a gare su. Yana daga cikin nauyin da yake kan shugaba ya ɗauki alƙalai da masana waɗanda za su ilmantar al’umma kan yadda za a yi bautar Allah da kuma hanyoyin da za a sami dukiya wadda ba ta saɓa wa shari’a ba. Haka kuma, ya ɗauki malaman makaranta waɗanda za su koyar da yara ilimin Alƙur’ani. Ya ɗauki limamai waɗanda za su riƙa jagorantar jama’a sallah da sanar da su abubuwan da suka dace da waɗanda ba su dace da shari’ar addinin Musulunci ba. Ya ɗauki waɗanda za su riƙa karɓar zakka da waɗanda za su riƙa gudanar da bincike don gano waɗanda aka zalunta don a karɓar masu haƙƙoƙinsu.

    An bayyana cewa, Umar ɗan Khattab, Allah Ya yarda da shi, a kowane lokaci yana bincika ayyukan waɗanda ya ba shugabanci dangane da dangantakar da take tsakaninsu da waɗanda suke shugabanta. An bayyana a cikin Jawhara, inda Al-Hassan al-Basri, ya ce: “Sayyidina Umar, a wasu lokuta yana zagayawa cikin garin Madina da dare. A wata rana sai ya gamu da wata mata daga cikin matan Madina tana ɗauke da salkar ruwa. Sai ya tambaye ta dalilin fitowa da dare don ɗaukar ruwa. Sai ta amsa masa da cewa, ba ta da ɗa ko wani ɗan uwa ko bara wanda zai ɗauko mata. Wannan dalilin ne ya sa ta fita da dare don ta ɗauko ruwa ba tare da wani ya gan ta da rana ba. Daga nan sai Sayyidina Umar ya ɗauki wannan salkar ruwa ta wannan mata ya kai mata gidanta”. Daga nan sai ya ce: “Ki yi wa Umar alƙawari za ki amshi taimako daga gare shi. Sai wannan mata ta ce: Na yi alƙawari”. Sai ya sake ce mata ki tabbatar da alƙawarinki. Daga nan ne wannan mata ta gane Sayyidina Umar ne ya ɗaukar mata salkar ruwa zuwa gidanta. Daga wannan rana Sayyidina Umar ya samar mata da wani wanda ya riƙa kai mata ruwa a kullum.

    Darussan da Suka Kamata a yi Koyi da su

    A nan ma wannan manufa ta kawo muhimman darussan da suka kamata a yi koyi da su waɗanda suka haɗa da:

    ü  Shugabanni su ƙara bunƙasa sana’o’i da ayyukan hannu waɗanda talakawansu ke yi. Ire-iren waɗannan sana’o’i za su taimaka wa al’umma samu hanoyin da za su yaƙi talauci da rashin aikin yi.

    ü  Shugabanni su gyara hanyoyin ƙauyuka da karkara don samun sauƙin zuwa kasuwanni don saye da sayarwa.

    ü  Ya zama dole ga shugabanni su kare mutunci da dukiyar talakawansu, da kuma ƙwato dukiyar talakawansu ga dukkan wanda ya zalunce su a duk inda take matuƙar suna son shiga Aljanna.

    ü  Shugaba ya riƙa zagaya a dukkan ma’aikatu don ganin yadda ma’aikata suke gudanar da ayyukansu.

    ü  Haka kuma, yana da matuƙar muhimmanci ga shugaba ya riƙa ziyara cikin garin musamman da dare don ganin halin da talakawa suke cike, don taimaka wa waɗanda suke bukatar taimako.  

    Manufa ta Bakwai

    Manufa ta bakwai tana bayyana cewa, yana da matuƙar muhimmanci ga dukkan shugaba ya riƙa hulɗa da waɗanda yake shugabanta ta hanyar mutunta su, da fahimtar su, da ba kowane darajar da Allah Ya ba shi. Wannan na nufin ya ɗora waɗanda suka san haƙƙoƙin shugabanci daga cikin talakawansa a kan manyan muƙamai na tafiyar da harkokin addini a duk wuraren da suke. Haka kuma, sauran talakawa bai dace a ɗora masu wani nauyi wanda zai cuta masu ba wajen tafiyar da harkokin rayuwarsu ta duniya da ta lahira. Haƙƙin shugaba ne ya sanar da talakawansa abubuwan da suka zama dole game da mahaliccinsu. Haka kuma, ya ummurce su yin waɗannan abubuwa na dole waɗanda shari’a ta bayyana. Sannan kuma ya hana su aikata abubuwan da ba su da kyau waɗanda shari’a ta hana aikata su.

    Bugu da ƙari, bai kamata shugaba ya tsaurara kan wasu dokoki da hani waɗanda akwai shakku cikinsu ba. Abin da ya kamata ga shugaba shi ne, ya tilasta wa talakawansa yin cikakkiyar biyayya ga dokokin Allah. Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, shi ne wanda ya fi kowa ilimin sanin Allah kuma yana tsoron saɓa wa dokokin Allah. Saboda haka ne, yake jure halayyar mutane da al’adunsu matuƙar ba su saɓa da dokokin Allah ba. Ya kasance yana jure wautar Larabawan ƙauye da munafukai da suke saɓa masa. Wannan al’amari ya yi tsanani har ta kai ga mutanensa suka ce masa: “Ya kamata ka ɗauki mataki mai tsanani a kansu!”. Ya yi haƙuri da su saboda ya sami damar haɗuwa da manyansu. A wasu lokuta yakan ba su wani ɓangare na dukiyar gwamnati don ya ƙara jaddada imani a cikin zukatansu.

    Darussan da Suka Kamata a yi Koyi da su

    Daga cikin darussan da za a yi koyi da su a nan akwai:

    ü  Shugabanni su riƙa hulɗatayya da waɗanda suke jagoranta yadda talakawan za su fahimci shugabannin su mutanen kirki ne waɗanda ba su ƙyamar su.

    ü  Yana da matuƙar muhimmanci ga shugabanni da su riƙa haƙuri da talakawansu musamman mazauna ƙauyuka waɗanda ba su da fahimtar al’amura, wasunsu ma idan suka tabka ƙauyanci abin sai addu’a.

    ü  Ya jawo wasu daga cikin talakawansa ya ba sa manyan maƙamai don taimaka masa tafiyar da mulkin ƙasa ko jiha ko ƙaramar hukuma.

    ü  Dole ne shugaba ya kauce wa ɗora wa talakawansa tsauraran dokoki waɗanda za su cuta wa rayuwarsu.

    ü  Ya tausaya wa talakawansa a lokacin da suka yi wani kuskure. Ya jawo su kusa da shi ya nuna masu kurakuransu da illolin da ire-iren waɗannan kura-kurai ka iya haifarwa.

    Zuri’ar Malam Ummarun Dallaje sun gudanar da mulki a ƙasar Katsina daga shekara ta 1806 zuwa shekara ta 1906 lokacin da Turawan mulkin mallaka daga ƙasar Ingila suka karɓe mulki daga wajen su suka ba Muhammadu Dikko daga zuri’ar Sulluɓawa. Wani abin sha’awa shi ne, tun daga Malam Umarun Dallaje har zuwa Sarkin Dallazawa na ƙarshe Malam Yaro, sun gudanar da mulkinsu bisa koyarwar Usul-Al-Siyasa, hasali ma, Turawa da suka tuɓe Sarki Abubakar, ba su tuɓe shi saboda rashin biyayya ko zalunci tsakaninsa da talakawa ba, sun tuɓe shi ne saboda ya ƙi yarda a sauya aiwatar da hukunci da dokokin addinin Musulunci a sauya su da sababbin dokokin da Turawa suka kawo ƙasar Katsina.

    Kammalawa  

    Idan muka nazarci waɗannan bayanan da suka gabata za a fahimci cewa duk wani tsari idan ba na Allah ba ne, to ya zama tsarin banza. Tun daga lokacin da Turawan Mulkin Mallaka na ƙasar Ingila suka karɓe mulkin ƙasar da a yau ake kira Nijeriya, za a ga sun kawo wasu sauye-sauye dangane da yadda ake gudanar da shugabanci a wannan ƙasa har zuwa lokacin da suka ba da mulki ga ‘yan ƙasa a shekara ta 1960. Karɓar mulki da ‘yan ƙasa suka yi sun kawo nasu tsare-tsaren da sauye-sauye amma har zuwa wannan lokaci ba a sami biyan bukata ba, kullum al’amari sai ƙara ɓaci yake. Babban dalilin da ya kai mu halin da muke ciki shi ne, mun ɗauka dabarar mu ko hikimar mu za su taimaka muna samun ingantaccen shugabanci, sannan kuma mun ɗauka wani daga cikin mu saboda wata ƙwarewa da ake tsammanin yana da ita zai iya fitar da mu wannan hali da muke ciki. Wannan ba ƙaramar wauta ba ce, don kuwa dukkan waɗannan abubuwa babu mai iya yi muna smaganinsu sai Allah, wanda shi ne maganin komi na duniya da lahira. Dangane da haka, ya zama dole mu fahimci cewa, shugabanci a addinin Musulunci al’amari ne mai matuƙar muhimmanci, wanda idan aka tafiyar da shi kamar yadda shari’a ta shimfiɗa al’umma za ta zauna lafiya a kuma sami ƙaruwar arziki da fahimtar juna. Babbar hanyar da za a sami wannan biyan bukata ita ce, shugabanni su zama masu adalci ga waɗanda suke shugabanta. Su kuma waɗanda ake shugabanta su riƙa yin biyayya ga waɗanda ke shugabantarsu. Dukkan waɗannan manufofi da za su taimaka muna mu zauna lafiya suna cikin Usul-Al-Siyasa wadda Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Shehu Mujaddadi Usmanu Ɗanfodiyo ya rubuta wa Malam Ummarun Dallaje wanda ya yi yaƙin jihadi a ƙasar Katsina.  

     

    Manazarta

    Adeleye, R. A. (1971). Power and Diplomacy in Northern Nigeria, 1804 –1906, Sokoto Caliphate and its Enemies, London: Longman.

    Adeleye, R. A. (1975) ”Hausaland And Borno, 1600 – 1800”, in Ade Ajayi, J. F. da Crowder, M. History of West Africa, Vol. I, London.

    Adeyemi, O. O. (2019) “Local Government Administration in Nigeria: A Historical Perspectiɓe”, Journal of Public Administration and Goɓernance, Macrothink Institute.

    Alhassan, H. da Wasu, (1982) Zaman Hausawa. Zariya: Institute of Education Press, ABU.

    Antigha, O. B, (2013) “States and Local Government Areas Creation as a Strategy of National Integration or Disintegration in Nigeria, Journal of Educational and Social Research, Vol. 3 (1) January.

    Augie, A. R. (1984) “The Gobir Factor in the Social and Political History of the Rima Basin, C. 1650 to 1808 A. D. Ph. D. Thesis. Zaria: Department of History, Ahmadu Bello University.

    Chidozie, E. (2020) “Local Government Reforms as Instrument for National Deɓelopment in Nigeria, a cikin, International Journal of Trend in Scientific Research and Deɓelopment, Vol. 4, Issue 3.

    Ɗanfodiyo, S. A. (Ba Shekarar Bugu) Kitabul-Niyyati, Kano-Nigeriya.

    Ɗanfodiyo, U. (1407 Hijra) Surajul Ikwani, Bugun Sakkwato.

    Ɗanfodiyo, U. (Ba Shekarar Bugu) Wasiƙatul Ikwani, Bugun Sakkwato.

    Ɗankoussou, I. (1970) Katsina Traditions Historiƙues des Katsina après la

      Jihad, Niamey: Centre Régional de Documentation Pour la Tradition orale.

    Egbe, E. J. (2014) “Natiɓe Authorities and Local Government Reforms in Nigeria Since 1914”. IOSR Journal of Humanities and Social Sciences, Vol. 19, Issue 3.

    Gumi, A. M. (1979/1399A. H. ) Tarjamar Ma’anonin Alƙur’ani Zuwa Harshen Hausa. Beirut-Lebanon: Dar-al-Arabia.

    Gusau, S. M. (2005) Musulunci da Bazuwarsa, Kano: Benchmark Publishers.

    Hammani, M. D. (1975) ”Adar, The Tuareg And Sokoto:Relations of Sokoto With the Hausawa and Tuareg During the 19th Century”, Sokoto Seminar Paper.

    Hogben, J. S. (1967) An Introduction to the History of the Islamic States of Northern Nigeria, Ibadan: Oɗford University Press.

    Ibrahim, M. S. (1982) ”Dangantakar Al’ada da Addini:Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Ikime, O. (1977) The fall of Nigeria, the British Conƙuest, London: Heinemann.

    International Crisis Group, (2010) Northern Nigeria: Background to Conflict, Africa Report No. 168.

    Johnston, H. A. S. (1970) The Fulani Empire of Sokoto, London: Oɗford University Press.

    Laɓers, J. (1997) ”Katsina and the Wider World: Adɓentures in the Historiography of Birnin and Ƙasar Katsina” in Tsiga I. A. and Adamu, A. U. Islam and the History of Learning in Katsina. Ibadan: Spectrum Books Limited.

    Magaji, A. (1986) ”Gudummuwa a kan Ƙoƙarin da ake yi na Samar da Cikakken Tarihin Hausawa da Harshensu”, Maƙala. Kano: Takardar da aka Gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Mani, A. (1966). Zuwan Turawa Nijeriya ta Arewa. Zariya: NNPC.

    Na’iya, M. (1997) ”A Discourse in The Intellectual Legacies of Some Pre-Jihadic Muslim Scholars in Katsina” a Cikin Tsiga, I. A. and Adamu, A, U. Islam and The History of Learning in Katsina. Ibadan: Spectrum Books Limited.

    Olusanya, G. O. (2004) “Constitutional Deɓelopment 1861-1960”, a cikin Ikime, O. Groundwork of Nigerian History, Historical Society of Nigeria. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria) Plc.

    Palmer, H. R. (1914) “An Early Fulani Conception of Islam, ” JAS ƊII.

    Rahim, A. (1981) Islamic History. Lagos-Nigeria: Islamic Publications Bureau.

    Sallau, B. A. S. (2000) ”Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’a a Ƙasar Hausa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Shareef Bin Farid, S. A. A. U. M. (1435/2014) Fassarar Maƙala Mai Taken Usul al-Siyasa, zuwa Ingilishi, ta Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ɗan Usmanu Ɗanfodiyo. Maiwurna-Sudan: Sankore Institute of Islamic-African International Studies.

    Smith, M. G. (1957) "The Hausa System of Social Status" in Africa Vol. ƊƊƁII. No. 1.

    Usman, Y. B. (1972) ”Some Aspects of the Eɗternal Relations of Katsina Before 1804”, Saɓanna Vol. I. No. 2.

    Usman, Y. B. (1981) The Transformation of Katsina: (1400-1883). The Emergence and Oɓerthrow of the Sarauta System and the Establishment of the Emirate. Zaria: ABU Press.

    Yahaya, I. Y. (1988), Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zariya: NNPC.

    Wikipedia, (2022) “Politics of Northern Nigeria”.

    www.amsoshi.com

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.