Muhimmancin Al’adun Hausawa A Bakin Mawakan Baka Na Hausa: Tsokaci Kan Wakar Al’adun Gargajiya ta Musa Dankwairo Maradun

    Takardar aka Gabatar a Babban Taron Ƙasa da Ƙasa da Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Sashen Koyar da Kimiyyar Harsuna da Harsunan Ƙasashen Waje da Cibiyar Gudanar da Bincike a kan Harsunan Nijeriya, Fassara da Fasahar Harsuna, Jami’ar Bayero, Kano, za su Gudanar a kan Bikin Cika Shekara Talatin akan Tarihi da Gudummuwar Musa Ɗanƙwairo Maradun Wajen Waƙoƙin Baka na Hausa, Daga Ranar 12 Zuwa 15 ga Watan Satumba, 2021

    Muhimmancin Al’adun Hausawa A Bakin Mawaƙan Baka Na Hausa: Tsokaci Kan Waƙar Al’adun Gargajiya ta Musa Ɗanƙwairo Maradun

    Daga

    PROFESSOR BASHIR ALIYU SALLAU
    Sashen Koyar Da Hausa
    Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dutsin-Ma, Jihar Katsina – Nijeriya
    08036194138
    sarkingaska@yahoo. com
    wanzamansafana@gmail. com
    bsallau@fudutsinma. edu. ng 

    Da 

    MUHAMMAD MUSA YANKARA
    Sashen Koyar Da Hausa
    Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dutsin-Ma, Jihar Katsina – Nijeriya 

    TSAKURE

    Bunƙasar kowace al’umma da ci gabanta yana da matuƙar alaƙa da irin yadda wannan al’umma ta yi riƙo da kyawawan al’adunta da adabinta. Kowace al’umma tana da ire-iren al’adun da take bi domin cimma burinta na rayuwa. Waɗannan al’adu sun haɗa da tsarin matakan rayuwa waɗanda suka haɗa da aure da haihuwa da mutuwa. Bayan waɗannan akwai sassan rayuwa waɗanda suke da alaƙa ta kusa da kusa da matakan rayuwa. Ire-iren su sun haɗa shugabanci da tarbiyya da hanyoyin tattalin arziki da zamantakewar wannan al’umma. Bisa la’akari da muhimmancin waɗannan tsare-tsare da kuma irin yadda al’ummomin Tarayyar Nijeriya suke bin su sau da ƙafa ya sa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta shirya gasa kan al’adun gargajiya a shekara 1977. A wajen wannan gasa kowace jiha daga jihohi daga jihohi goma sha biyu na wannan ƙasa sun gabatar da ire-iren al’adunsu na gargajiya waɗanda suka shafi sutura da abinci da kaɗe-kaɗe da raye-raye da dai sauran fannonin rayuwa. Makaɗa da mawaƙa daga ƙasar Hausa sun shiga wannan gasa. Daga cikinsu akwai Sarkin Taushin Katsina da Musa Ɗanƙawairo Maradun wanda ya rera waƙa mai amshin “Kar mu sake mu mance, ku bi al’adunmu na gargajiya”. Wannan waƙa ta taɓo batutuwa masu muhimmanci waɗanda suka danganci al’adun gargajiya na Hausawa, musamman abin da ya shafi tarbiyya da abinci da sutura da sauran fannonin rayuwar Hausawa.

    Dangane da haka, maƙasudin wannan takarda shi ne, ta fito da manyan turakun al’adun Hausawa kamar yadda Musa Ɗanƙwairo Maradun ya waƙe su. Bayan haka, za a danganta baituttuka wannan waƙa don kwatanta su da halin da muke ciki a yanzu. Yin haka, zai sa mu fahimci shin al’ummar Hausawa a wannan zamani sun ji kiran da Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi na mu riƙe al’adunmu? Ko kuwa mun yi sake muka watsar da su. Idan mun yi sake muka watsar da su wane sakamako muka samu a yau?

     

    Gabatarwa

    Tun kafin zuwan wannan zamani al’ummar Hausawa suna da hanyoyin da suke isar da saƙo don nishantarwa ko don faɗakarwa ko don yin gyara ko yin hannun-ka-mai sanda ga al’umma yadda za a daidaita al’amuran da al’umma za ta zauna lafiya da samun ci gaba mai ɗorewa da ƙaruwar tattalin arziki. Babban ginshiƙin da ake amfani da shi don isar da wannan saƙo shi ne adabin gargajiya ko na baka. Adabin baka na Hausa kamar yadda masana suke kiran sa yana da manyan rassa waɗanda suke taimaka masa wajen isar da waɗannan saƙonni. Masana da manazarta da ɗalibai irin su Ɗangambo, 2008, da Ibrahim, da Gusau, 2003 da 2008, da Yahaya, 2016, sun yi muhimmin ƙoƙari wajen bayyana asalin adabin Hausa, ginuwarsa, rabe-rabensa da hanyoyin nazarinsa da sauransu. Daga cikin rabe-raben adabin baka na Hausa akwai kiɗa da waƙa. A nan ma, ba su yi ƙasa a gwiwa ba, don kuwa sai da suka yi ingantattun bayanai a kan rabe-raben makaɗa da mawaƙan baka na Hausa waɗanda suka haɗa da makaɗa da mawaƙan sarauta da na sana’o’i da na maza da na jama’a da na sha’awa da kayan kiɗan da ake amfani da su wajen kiɗa da waƙa da sauransu. Dukkan waɗannan makaɗa da mawaƙan baka na Hausawa suna rera waƙoƙinsu ne ga nau’o’in mutane dangane da matsayinsu a wajen al’ummar Hausawa. Misali, daga cikin waɗannan rabe-rabe na makaɗa da mawaƙan baka na Hausa akwai waɗanda sarakunan ƙasar Hausa kaɗai suke yi wa kiɗa da waƙa, amma kuma a wasu dalilai masu girma tare da izinin iyayen gidansu sukan yi wa wasu ko wani abu wanda ya shafi al’umma kiɗa da waƙa. Daga cikin makaɗan fada na ƙasar Hausa akwai Musa Ɗanƙwairo Maradun wanda ya yi wa sarakuna a ƙasar Hausa da ma wajen ƙasar Hausa kiɗa da waƙa. Bai tsaya a nan ba, don kuwa ya yi wa attajirai da ma’aikatan gwamnati da malamai da masu sana’o’in gargajiya na Hausawa da ‘yan siyasa da kuma na faɗakar da al’umma abubuwan da suka shafi rayuwarsu da sauran fannoni.

    Dangane da haka, wannan takarda za ta yi nazari ne a kan wata daga cikin waƙoƙin da ya yi na faɗakar da al’umma, wato waƙar, “Kar mu sake mu mance, ku bi al’adunmu na gargajiya”. Dalili kuwa shi ne, adabin baka na Hausa yana da alaƙa ta tsoka da jini da al’adun Hausawa, don kuwa kowanensu ba ya yin tasiri sai da taimakon ɗan’uwansa. A taƙaice suna da danganta mai kyau wadda take taimaka wa junansu. Haka kuma, Musa Ɗanƙwairo ya fahimci matasa da wasu daga cikin al’ummar Hausawa sun ɗauki wata sabuwar rayuwa wadda ta kama hanyar ruguza ingantattun al’adun Hausawa masu nagarta na asali. Domin ya jawo hankalin al’umma ta koma bisa ingantaccen tsari, ya rera wannan waƙa don al’umma ta dawo cikin hankalinta. A taƙaice, a wannan waƙa Musa Ɗanƙwairo yana kira ga dukkan al’ummar Hausawa da kar mu sake mu mance, mu bi al’adunnmu na gargajiya waɗanda suka shafi sutura da abinci da zamantakewa da shugabanci da sauran hulɗoɗin rayuwa ta yau da kullum bisa tafarkin addinin Musulunci.

    Salsalar Waƙar Al’adun Gargajiya ta Musa Ɗanƙwairo Maradun

    Waƙar, “kar mu sake mu mance, mu bi al’adanmu na gargajiya, wadda Musa Ɗanƙwairo Maradun ya rera, ta samo asali ne daga bikin raya al’adun baƙaƙen fata wanda aka gudanar a Tarayyar Nijeriya lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon. A wannan biki an gayyato dukkan al’ummar baƙar fata waɗanda suke zaune a Nahiyar Afirika da sauran Nahiyoyi na wannan duniya. Babban dalilin gudanar da wannan biki shi ne, shugabannin ƙasashen Afirika sun fahimci mulkin mallaka wanda Turawa suka yi wa mafi yawancin ƙasashen Afirika, ya sa matasa da wasu daga cikin al’ummomin baƙar fata suna ƙoƙarin mantawa da al’adunsu da ɗabi’unsu waɗanda suka shafi abinci da sutura da zamantakewa suka ɗauki ire-iren na Turawa. Don a faɗakar da al’umma ya sa Gwamnatin Mulkin Soja ƙarƙashin Janar Yakubu Gowon a shekara 1977 ta gayyaci dukkan shugabanni da wasu daga cikin al’ummomin baƙar fata na duniya suka haɗu a Lagos da Kaduna aka gudanar da wannan biki da taken Bikin Al’adun Gargajiya na Baƙar Fata. Wanda da Turancin Ingilishi aka kira shi da: Black African Festiɓal of Arts and Culture, a taƙaice FESTAC 77. Abubuwan da aka gabatar a wannan biki sun haɗa da baje kolin kayayyakin fasaha na al’ummomin baƙar fata waɗanda suka haɗa da sutura, kayan kwalliya waɗanda aka yi da kaba ko da ɓawo ko da ganyaye. An kuma gabatar da kayan abinci iri daban – daban, sannan kuma sarakunan gargajiya sun yi ado suka yi hawan durbar da dawaki da raƙuma. Bayan waɗannan abubuwa, an gayyaci makaɗa da mawaƙa da ‘yan rawa inda kowanensu ya baje kolin irin fasahar da Allah Ya ba shi. Daga cikin makaɗa da mawaƙan ƙasar Hausa waɗanda waƙoƙinsu suka fi shahara akwai wadda Musa Ɗanƙwairo Maradun ya rera mai amshin, “kar mu sake mu mance, ku bi al’adunmu na gargajiya” (Soja, 2020: 67-68).

    An rera wannan waƙa a shekara ta 1977 a garin Kaduna ta Tarayyar Nijeriya. A cikin wannan shekara ne kuma Hukumar Gidan Rediyon Tarayya ta Kaduna ta gayyaci Musa Ɗanƙwairo ya zo da jama’arsa don su sake rera wannan waƙa a Sitidiyo wadda ita ce ake sauraro har a wannan zamani.

    Waƙar “kar mu sake mu mance, ku bi al’adunmu na gargajiya”, tana da ɗiya goma sha takwas tare da amshi, waɗanda mafi yawancinsu jagora da ‘yan amshi kan kawo dogayen ɗiyan waƙa da dogon amshi (Gusau, 2019: 448-451).

    Waiwaye a kan Al’adun Gargajiya

     

    Masana irin su Ibrahim, (1982) da Bunza, (2006), sun gabatar da bayanai dangane da asali da ma’anar kalmar al’ada. A dunƙule kalmar al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗan’Adam tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa. Dangane da wannan batu da ake magana a kai, al’adun gargajiya na nufin tsarin rayuwar Hausawa wadda ta shafi abinci, da sutura, da zamantakewa, da shugabanci bisa koyarwar addinin Musulunci.

    Ta la’akari da bayanin da ya gabata, a iya cewa dukkan al’ummomin da suke zaune a Tarayyar Nijeriya kafin shigowar Turawan Mulkin Mallaka suna da ire-iren al’adunsu mabambanta. Ire-iren waɗannan al’adu ne suke zama jagora ga kowace al’umma dangane da abubuwan da suka dace a yi da kuma waɗanda ba su dace a yi ba. A wasu fannoni ana samun wasu wuraren da al’ummomi suke yin tarayya a kan wasu al’amura waɗanda suka shafi yadda suke gudanar da harkokin al’adunsu, musamman ta fuskar tarbiyya da aure da haihuwa da mutuwa da zamantakewa da shugabanci da addini da sauran fannonin rayuwa. Daga cikin waɗannan fannoni na al’ada za a tarar mafi yawanci al’ummomi suna koya wa ‘ya’yansu yin cikakkiyar biyayya ga abin da suke bautawa da koya musu sana’o’insu na gargajiya da ƙulla danƙon zumunci da gaskiya da riƙon amana da biyayya ga shugabanci da taimakon juna da kara da nuna alkunya da sauransu (Sallau, 2018).

    Taƙaitaccen Tarihin Musa Ɗanƙwairo Maradun

    An haifi Musa Ɗanƙwairo Maradun a cikin shekara ta 1909 a garin Ɗankadu ta gundumar Bakura a jihar Zamfara ta yau. Bisa asali na wajen uwa da uba Ɗanƙwairo Bazamfare ne. Ya gaji kiɗa da waƙa daga wajen mahaifinsa Usman Ɗankwanagga wanda shi ma ya gaji wannan sana’a daga kakan Ɗanƙwairo Makaɗa Kaka. Bisa aikin gado wannan zuri’a ta Ɗanƙawiro sun gaji noma da kiɗan noma da kuma kiɗan sarauta musamman ga sarakunan masarautar Bakura. Wajen kiɗan noma suna amfani da farar ganga, a kiɗan sarauta kuma suna amfani ne da kotso (Gusau, 2019:2-3).

    Musa Ɗanƙwairo Maradun ya sami sunan Ɗanƙwairo ne a matsayi na alkunya daga sunan wani daga cikin barorin mahaifinsa da ake kira Ƙwairo. Kasancewar Allah Ya ba Musa murya wasai wadda ake jin ta sosai ba gura-gura ba shaƙewa. Haka shi Ƙwairo wanda aka yi wa Musa da alkunyarsa yana da murya sosai wadda ake ji ko’ina. Wannan dalilin ne ya sa Usman Ɗankwannaga wato mahaifin Musa Ɗanƙwairo ya ce an sami wanda ya maye gurbin Ƙwairo. Tarihi ya bayyana Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya tashi a gaban mahaifinsa da sauran danginsa musamman Abdu Kurna wanda yake wa ga Ɗanƙwairo wajen aiwatar da kiɗa da waƙa a ƙasar Maradun. Lokacin da girma ya cimma mahaifinsu Usman Ɗankwannaga, sai ya je wajen Sarkin Maradun ya sanar da shi zai yi murabus a naɗa babban Ɗansa Abdu Kurna a Matsayin wanda zai gaje shi. Sarkin Maradun ya naɗa Abdu Kurna suka ci gaba da yin aikin da suka gada na kiɗa da waƙa tare da ɗan’uwansa Musa Ɗanƙwairo. Kasancewar Sarkin Makaɗa Abdu Kurna ya fahimci basira da fahimta da riƙe tarihi da Allah Ya ba ƙanensa Musa Ɗanƙwairo ya sa ba shi sarautar Ɗangaladimansa da sunan Daudin Kiɗa (Gusau, 2019:5-7).

    Daga baya sai Musa Ɗanƙwairo ya sami cin gashin kansa ya kafa tasa ƙungiyar wadda ta haɗa da ‘ya’yansa da ‘ya’yan danginsa da kuma barori. Wannan ƙungiya ƙarƙashin jagorancinsa ta yi waƙoƙin da dama waɗanda suka shafi rayuwar al’ummar ƙasar Hausa ta fuskoki da dama. Don kuwa bayan sarakuna da attajirai da malamai da ‘yan siyasa maza da mata, sun yi waƙoƙi masu yawa don faɗakarwa da wayar da kan al’umma kan dukkan wani abu da ya shafi rayuwar Hausawa da Arewacin Nijeriya. Wani abin ban sha’awa da burgewa cikin jagorancin ƙungiyar Ɗanƙwairo, shi ne ‘yan amshi na taimaka masa ta hanyar yin ƙari a cikin waƙoƙinsu. Kamar yadda yake cewa a waƙar ‘Yandoton Tsahe Aliyu II (1960-1991) mai gindin waƙa “Shirya kayan faɗa Maigida Tsahe, Ali ɗan Iro bai ɗauki raini ba”, inda yake cewa:

     

    Jagora: Ga makaɗi ya ƙulla waƙatai,

    ‘Y/Amshi: Sai a amsa mashi ba a ƙara mai,

       : In na ƙulla waƙa a ƙara man,

       : Mu huɗu duk azanci gare mu,

    : Shin a’a mutum guda za ya radde mu,    : :

    :Shirya Kayan faɗa Maigida Tsahe.

    (Gusau, 2019:101-102).

     

    Ta fuskar iyali Allah ya albarkaci Musa Ɗanƙwairo Maradun da haihuwar ‘ya’ya goma sha bakwai (17) goma maza (10) sai bakwai (7) mata. Daga cikinsu akwai Sanin Ɗanƙwairo Zaƙin Murya da Mamman Ɗanmakaɗa Daudu I da Alhaji Garba Zwacin kiɗi da Audu Adodo Wakilin Kiɗa da Amina da Sa’adatu. Allah ya yi masa rasuwa a shekara ta 1991. Allah Ya gafarta masa, Ya albarkaci zuri’arsa, Ya sa Aljannah Firdausi ta zama makomarsa da dukkan al’ummar musulmi.

    Turken Waƙar Al’adun Gargajiya ta Musa Ɗanƙwairo Maradun

    Gusau, (2008: 370) ya bayyana cewa, “turke a ƙa’idar masu nazarin waƙar baka na nufin saƙon da waƙa take ɗauke da shi. Idan kuma an ce saƙo kuma ana magana ne kan manufar da ta ratsa tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta, ba tare da karkacewa daga ainihin abin da ake zance a kansa ba”.

    Bisa la’akari da bayanin da ya gabata, a iya cewa, faɗakarwa ita ce turken waƙar al’adun gargajiya ta Musa Ɗanƙwairo Maradun. Dalili kuwa shi ne, tun daga farkon waƙar har zuwa ƙarshenta Musa Ɗanƙwairo Maradun yana faɗakar da al’ummar Hausawa da su yi riƙo da al’adunsu na gargajiya waɗanda suka shafi sutura da abinci da shugabanci da zamantakewa bisa koyarwar addinin Musulunci. Domin ƙara tabbatar da haka, za a yi tsokaci kan wasu daga ɗiyan waƙar don bayyana cikakken turken wannan waƙa.

    Faɗakarwa kan Sutura

    Bayan ɗiyan farko na buɗe waƙar ɗiyan da suka biyo bayansu na bayyana abubuwan da suka dace Ɗan’arewa ya yi dangane da sutura, wadda idan ya sanya ta zai fito a siga ta kamala wadda za ta sa a dube shi da mutuncin kuma cikakken mutum. Kamar yadda yake cewa:

    Jagora: Kar mu sake mu mance,

    : Ku bi al’adunmu na Gargajiya.

     

    Jagora: Mu bi al’adunmu na Gargajiya.

    ‘Y/Amshi: Kar ku sake ku mance,

    : Mu bi al’adunmu na Gargajiya.

     

    Jagora: Niyya kai!

    Y/Amshi: Kar ku sake ku mance,

    : Mu bi al’adunmu na Gargajiya. Ɗ3

    Jagora: Kyawaon Ɗan’arewa babbar riga,

    : Ga rawani da taggo,

    Y/Amshi: Mu bi al’adunmu na gargajiya.

     

    Jagora:: Kyawaon Ɗan’arewa babbar riga,

    Y/Amshi: Ga rawani da taggo,

    Jagora: Ko ranar suna,

    : Ko Juma’a ka ɗauka,

    : Mu bi,

    Y/Amshi: Mu bi al’adunmu na gargajiya,

    : Kar mu sake mu mance,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya (Gusau, 2019: 449).  

     

    Idan muka nazarci waɗannan ɗiyan waƙa da suka gabata, za a fahimci cewa, Musa Ɗanƙwairo Maradun yana faɗakar da ‘Yan’arewa muhimmancin satura a wajen rayuwarsu. Dalili kuwa shi ne, duk lokacin da mutum zai je wajen raɗin suna ko sallar Juma’a, idan ya sanya babbar riga da taguwa ya kuma yi rawani za a fi ganin sa da ƙima da daraja.

    Ba ga maza kawai Musa Ɗanƙwairo ya tsaya ba, don kuwa ya faɗakar da mata ire-iren suturar da ya kamata su sanya don tsare mutuncinsu. Ga gargaɗin da ya yi wa mata:

     

    Jagora: Ku ko matan ƙasarmu,

    : Waɗanda suke ɗiyan Musulmi,

    : Ku zanka yin lulluɓi,

    : Ban da sayen ‘yar kanti,

    : Kuna ta yawo rarira-rariya,

    : Abin ga,

    Y/Amshi: Ya ba da kunya,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya,

    : Kar mu sake mu mance,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya.

     

    Jagora: Ku ko matanmu Arewa,

    : Waɗanda aɗ ɗiyan Musulmi,

    : Ban da sayen siket da ‘yarkanti,

    : Kuna yawo rariya-rariya, abin ga ya ba,

    Y/Amshi: Mu kunya,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya,

    : Kar mu sake mu mance,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya (Gusau, 2019: 449).

     

    A waɗannan ɗiyan ɗiyan waƙa za a fahimci Musa Ɗanƙwairo Maradun yana faɗakar da matan Arewa musamman Hausawa waɗanda suke ‘ya’yan Musulmi su riƙa sanya sutura irin ta kamala wadda dukkan wanda ya gansu, ya san ba matan banza ba ne. Sanya siket da ‘yarkanti waɗanda Ɗanƙwairo ya ɗauka suturu ne na matan banza, matan bariki.

    Faɗakarwa kan Muhimmanci Addinin Musulunci a Waƙar Al’adun Gargajiya

    Kasancewar Musa Ɗanƙwairo mabiyin addinin Musulunci ne, ya sa koyarwar addinin ta yi naso cikin waƙarsa ta al’adun gargajiya. A cikin waƙar ya yi horo ga ‘yan’arewa waɗanda suke ɗiyan Musulmi su riƙe manyan shika-shikan addinin Musulunci kamar haka:

    Jagora: ‘Yan’arewa da an nan,

    : Waɗanda aɗ ɗiyan Musulmi,

    : Ƙwairo na gargaɗinmu,

    : Ku zan azumi da sallah,

    : Ku zan kono da zakka,

    : A zan azumi da sallah.

    Y/Amshi: Ku bi al’adunmu na gargajiya,

    : Kar mu sake mu mance,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya (Gusau, 2019: 449).

     

    Addini al’amari ne wanda yake da matuƙar muhimmanci a zuciyar mai yin shi. Kasancewar Musa Ɗanƙwairo mabiyan addinin Musulunci ne, kuma ya san matsayin shika-shikan addinin Musulunci ga dukkan wanda ya yarda da cewa shi Musulmi ne, ya sa shi yi wa dukkan ‘yan’arewa waɗanda suke Musulmi ciki har da shi gargaɗi da a riƙa tsayar da sallah, a riƙa yin azumi, a riƙa ba da zakkar fid-da-kai da ta dukiya don samun rahamar Allah Maigirma da ɗaukaka.

     

    Faɗakarwa kan Muhimmancin Sutura a Addinin Musulunci

    A wasu ɗiyan waƙa Musa Ɗanƙwairo ya kawo muhimmancin sutura a addinin Musulunci kamar haka:

    Jagora: Abin ga da ban takaici,

    : Sai ka ga ɗan Musulmi,

    : Da ɗan wandon yadi guda,

    : Ga ‘yar shat ya sa ga wuyanai,

    : Ba hula ga kai nai,

    : Aljihu nai ba tasbaha sai,

    Y/Amshi: Sai kwalin sigari,

     

    Jagora: Aljihu nai ba tasbaha,

    Y/Amshi: Sai kwalin sigari,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya.

     

    A waɗannan ɗiyan waƙa an bayyana illar ƙananan suturu wajen yin salla, kuma kasancewar suna ƙanana saboda nason zamananci ya sa mafi yawancin masu sanya ire-iren waɗannan kaya ba su damu da yin ayyukan addini ba musamman Salla wadda ake yin ta sutura irin ta kamala. Maimakon a sami tasbaha a cikin aljihunsu sai dai a sami kwalin taba sigari.

    Faɗakarwa kan Muhimmancin Abincin Gargajiya na Hausawa

     A faɗakarwar da Musa Ɗanƙwairo Maradun yake yi, ya yi wa matasa hannunka-mai-sanda. Ya bayyana cewa, matasa idan har ba su son sutura ta Hausawa ta kamala, ai ba su mance hura da nono ko tuwo da nama. Ga yadda ya yi wannan faɗakarwa:

    Jagora: ‘Yan’arewa Musulmi,

    : Kun ce ba ku son babbar riga,

    : Ina ganin ku,

    : Kun ce ba ku son babbat tago,

    : Ina ganin ku,

    : Kun ce ba ku son babban wando,

    : Ina ganin ku,

    : To, in haka gaskiya ne,

    Y/Amshi: Ku mance hura da nono,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya,

    : Kar mu sake mu mance,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya.

     

    Jagora: In haka gaskiya ne,

    Y/Amshi: Mu mance hura da nono,

    Jagora: Sannan a mance tuwo,

    Y/Amshi: Tuwo da nama,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya,

    : Kar mu sake mu mance (Gusau, 2019: 449).

     

    Bisa la’akari da irin muhimmancin da al’ummar Hausawa suka ba hura da nono da tuwo da nama, ya sa Ɗanƙwairo yi wa al’ummar Hausawa waɗanda suke ƙyamar suturun gargajiya na Hausawa shaguɓe da gugar-zana ta hanyar bayyana idan sun mance da babbar riga da babbar taguwa da da babban wando, ai ba su mancewa da hura da nono da tuwo da nama.

    Muhimmancin Doki a Al’adar Hausawa

    Doki yana daga cikin dabbobin alfarma da ake amfani da su a ƙasar Hausa musamman ga sarakuna da attajirai. Dalili kuwa shi ne, ana amfani da su don hawa lokacin bukukuwa na aure da na Salla da sukuwa da kilisa da kuma durba. Sakomakon shigowar Turawan mulkin mallaka a ƙasar Hausa sun kawo nau’o’in abubuwan hawa waɗanda suka haɗa da mota da babur da keke waɗanda kowa na iya saye domin biyan bukatarsa. Ɗanƙwairo ya fahimci wasu daga cikin al’ummar ƙasar Hausa sun mayar da hankali wajen sayen waɗannan nau’o’in ababen hawa saboda saurin biyan bukata. Duk da haka, Ɗanƙwairo bai yi ƙasa a guiwa ba wajen bayyana muhimmancin doki a wajen Hausawa. Ga abin da yake cewa:

    Jagora: Ko da kana da mota,

    Y/Amshi: Ka sai dokinka ka ɗaure,

    Jagora: Ko da kana da mota,

    Y/Amshi: Ka sai dokinka ka ɗaure,

    Jagora: Wurin mota daban ne,

    : Kuma,

    Y/Amshi: Wurin doki daban ne,

    Jagora: Wurin mota daban na,

    : Kuma,

    Y/Amshi: Wurin doki daban ne,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya.

     

    Jagora: In ka tashi hawan doki,

    : Ka hau ka yo,

    Y/Amshi: Kilisa,

    : Ka dawo gida ka ɗaure,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya,

    : Kar mu sake mu mance,

    : Mu bi al’adunmu na gargajiya (Gusau, 2019: 449-450).

     

    A waɗannan ɗiyan waƙa kamar yadda Ɗanƙwairo ya kawo su, yana ba da shawara idan Allah ya yi maka arziki ka sayi mota, kuma ka yi ƙoƙari ka sayi doki don kowanensu da wurinsa. Wannan magana haka take, don kuwa duk da kasancewar sarakuna da attajirai da masu sana’o’in gargajiya, misali wanzamai da makaɗa da mawaƙa da maroƙa wasunsu suna da motoci, amma akwai wuraren da suke amfani da dawaki kamar zuwa kilisa da hawan sallah da sauran bukukuwa inda doki ya fi mota daraja a wajen.

    Tsokaci kan Darussan da aka Koya a Waƙar Al’adun Gargajiya

    Tabbas! Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi faɗakarwa mai matuƙar amfani ga al’ummar Hausawa mazauna Arewacin Nijeriya musamman waɗanda suke Musulmi kan riƙo da al’adunsu na gargajiya waɗanda suka gada iyaye da kakanni. Waɗannan al’adu waɗanda suka shafi dukkan rayuwar Hausawa tun lokaci mai tsawo da ya gabata, har zuwa karɓar addinin Musulunci da Hausawa suka yi, sun taimaka matuƙa gaya wajen kawo wa al’ummar Hausawa zama lafiya, da kwanciyar hankali, da daraja, da bunƙasar tattalin arziki a idanun dukkan mutanen da a yau suke zaune a Tarayyar Nijeriya da Afirika da ma sauran sassan duniya. Waɗannan dalilai sun taimaka wajen karɓar al’adun Hausawa ga maƙwabtan Hausawa na kusa da ma na nesa.

    Shigowar Turawan mulkin mallaka ƙasar Hausa ya kawo babban sauyi wajen tafiyar da waɗannan al’adu, don kuwa sun kawo wata sabuwar rayuwa wadda ta shafi sutura, inda mafi yawancin suturun da suka kawo ƙanana ne waɗanda ba su dace da rayuwa irin ta Musulmi Bahaushe ba. Maza da mata idan suka saka ire-iren waɗannan suturu za a gan su kamar tsirara suke musamman mata. Haka kuma, ire-iren abincin da suka kawo bai kai darajar abincin Hausawa ba wato hura da nono da tuwo da nama. Sakamakon fahimtar da Musa Ɗanƙwairo ya yi na illolin wannan sabuwar rayuwa ne, ya sa shi faɗakar da al’ummar Hausawa mazauna Arewacin Nijeriya waɗanda suke ɗiyan Musulmi da, kar su sake su mance, su bi al’adunsu na gargajiya.

    A zamanin da aka yi wannan waƙa, ta yi matuƙar tasiri a rayuwar al’ummar Hausawa, domin kuwa a wancan zamanin mafi yawancin Hausawa a duk inda suke za a tarar suna sanya babbar riga da babbar taguwa da babban wando. Haka kuma suna matuƙar riƙo ga dokokin addinin Musulunci ta hanyar tsayar da sallah da bayar da zakkar fid-da-kai da ta dukiya da sauran abubuwan da addinin Musulunci ya yi horo a yi, da waɗanda ya hana a yi. Sannan kuma, a mafi yawancin gidajen ƙasar Hausa za a tarar akwai dawaki waɗanda ake kiwatawa don biyan bukatun rayuwa.

    Kash! A wannan zamani da muke a yau, wannan faɗakarwa da Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi, ta fita kunnen mafi yawancin al’ummar wannan zamani. Dalili kuwa shi ne, mafi yawancin al’ummar wannan zamani sun karɓi sabuwar rayuwar da Turawa suka kawo musamman matasa maza da mata, a wani lokaci har da dattawa. Ƙananan sutura sun zama abin ado a wannan zamani. Faɗakarwar da Musa Ɗanƙwairo ya yi wa maza ba ta shiga kunnensu. Yanzu matan Arewa sun wuce siket da ‘yarkanti da ya gargaɗe su da kar su sanya, sun kai matakin sanya ƙananan ƙaya waɗanda suke matse jiki su fito da dukkan sigar mace yadda za a ga abin da ya dace a gani da ma wanda bai dace a gani ba, wai ado da kwalliya ne, don jawo hankalin maza. Irin wannan ado al’adar Hausawa da addinin Musulunci sun yi hani mai tsanani a kan su.

    Kammalawa

    Waƙar al’adun Gargajiya ta Musa Ɗanƙwairo Maradun duk da kasancewar gajeruwa ce, ta yi kyakkyawar faɗakarwa da gargaɗi ga al’ummar Hausawa waɗanda suke ɗiyan Musulmi da su yi riƙo da kyawawan al’adunsu na gargajiya, kuma kar su mance da su. A wancan zamani da aka yi riƙo da su al’ummar Hausawa sun sami zaman lafiya da ɗaukaka da bunƙasar tattalin arziki. Allahu Akbar! A wannan zamani bayan rasuwar Musa Ɗanƙwairo Maradun a shekara 1991 zuwa yau, wannan faɗakarwa da yi yi, ba ta shiga kunnen al’ummar wannan zamani ba, don kuwa, a yau ba kowa ne yake sauraren ire-iren waɗannan waƙoƙi ba, bare ya ji ire-iren saƙonnin da suke ɗauke da su ba. A taƙaice sabuwar rayuwar da Turawa suka kawo ta maye gurbin kyawawan al’adu da muradu da adabin baka na al’ummar Hausawa, suka ɗauki rayuwar sanya ƙananan kaya da kaɗe-kaɗe na Turawa waɗanda ba su koyar da wata inganttatar tarbiyya sai fitsari da Rashin kunya da rashin ladabi.

     

    Manazarta

     

    Bunza, A. M. (2006), Gadon Feɗe Al’ada: Lagos, TIWAL-Nigeraia LTD.

    Bunza, A. M. (2008) “Religion and the Emergence of Hausa Identity: (An Inƙuiry into the Early Traditional Religion in Hausa land)”, being a paper presented at an International Conference titled: “Hausa Identity: Religion and History”, organised by AHRC and ESRC held at University of East Anglia Norwich.

    Gusau, S. M. (1996) Makaɗa da Mawaƙan Hausa I. Kaduna: Fisbas Media Serɓices.

    Gusau, S. M. (2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka, Kano. Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano. Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2017) Ƙamusun Kayan Kiɗan Hausa. Kano: Century Research and Publishing Company. Century Research and Publishing Company.

    Gusau, S. M. (2019) Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i na Huɗu.

    Ibrahim, M. S. (1982) ”Dangantakar Al’ada da Addini:Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Sallau, B, A. (2018)Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa a Jami’o’in Arewacin Nijeriya: Ƙalubale ga Tsarin Koyo da Koyarwa a Ƙarni na 21”, KADAURA, Journal of Hausa Multidisciplinary Studies, Vol. 1. No. 4, January, 2018

    Soja, F. L. (2020) “Turken Faɗakarwa a Waƙoƙin Baka na Zamantakewar Hausawa”, Kundin Digiri na Biyu. Katsina: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa Yar’adua.

    Yahya, A. B. (2016) Salo Asirin Waƙa. Sokoto: Guaranty Printers.

    www.amsoshi.com

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.