Shin Zan Iya Amsa Kiran Iyayena Ina Cikin Sallah?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne ingancin maganar da'ake cewa idan kana sallah iyayenka suka kiraka za ka katse sallar ka amsa musu, dai-daine da in kana cikin banɗaki shima ka amsa musu?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله.

    Idan Mutum yana sallar farillah ba zai yanke sallar ba saboda kiran mahaifinsa ko mahaifiyarsa, sai dai zai nusar da wanda yake kiransa cewa ya shagalta da Sallah, ko dai ta hanyar tasbihi, ko daga sautin karatun sallar, da makamantansu.

    Yahalatta kuma ya saukaka sallar tasa, idan yagama sallar sai ya Amsa kiran mahaifansa.

    Bukhari ya ruwaito hadisi (707) daka Abiy ƙatada Allah yakara masa yarda daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: ( Hakika zantashi sallah inasan tsawaita ta, sai naji kukan kananun yara sai na sauƙaƙa sallar, dan tsaoran karna tsanantawa mahaifiyar yaron).

    Sauƙaƙa sallah saboda wani dalili da zai shagaltar damai sallah ya halatta, idan sallar nafila ce idan kasan babanka ko babarka ransa ko ranta ba zai ɓaci ba danka karasa sallarka sannan ka Amsa musu, za ka cika sallarka, sannan sai ka Amsa musu bayan kagama.

    Amma idan kasan iyayenka ransu zai ɓaci idan ka ce sai ka gama sallah za ka Amsa musu, to sai ka yanke sallar ka Amsa musu, sai ka sake sallah sabuwa. Wannan idan Sallar ta nafilace, ba farillah ba. Babu komai Akanka. w

    Bukhari (3436) da Muslim (2550) Sun ruwaito hadisi lafazin na Muslim ne.

    Daka Abu huraira Allah yakara masa yarda daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce:( Juraih yakasance yana bauta agurin ibadarsa, sai mahaifiyarsa tazo ta ce: Yakai juraih nice mahaifiyarka kaimun magana, sai ta tarar da shi yana sallah, sai ya ce: Ya Allah sallata zanci gaba ko mahaifiyata zan Amsawa, sai ya zaɓi cigaba da Sallarsa, saita sake dawowa karo nabiyu ta ce: ya juraih nice mahaifiyarka kaimun magana, sai ya ce: Ya Allah Sallata ko Mahaifiyata, sai ya zaɓi sallarsa saita ce: Ya Allah wannan juraih ɗanane nai masa magana yaki Amsa mun, Ya Allah kada ka kasheshi harsai ka nuna masa jarabawa, Annabi ya ce: datai masa addu'ar ya fitinu dasai ya fitinu arayuwarsa...).

    Imamun Nawawi yai Babi ya ce: Babin da zai magana akan gabatar da biyayyar iyaye  akan sallar nafila dawaninta.

    Nawawi Allah yajikansa ya ce: " Malamai suka ce: Abunda yake dai-dai ahakkin juraih shi ne ya Amsawa mahaifiyarsa, domin yana cikin Sallar nafilane, cigaba da yin nafilar kuma ba wajibi ba ne, amsawa mahaifiyarsa dayi mata biyayya kuma dole ne, saɓa mata haramun ne kuma zai iya Sauƙaƙa sallar ya Amsa mata, sannan yadawo yaci gaba da Sallar sa...

    Duba Fat-hul baary na Hafiz ibnu hajar, da Mausu'ah fiƙhiyyaj (20/342) .

    Yazo acikin durrul muktaar - littafin Hanafiyyah (2/54). " idan ɗaya daka cikin mahaifan mutum suka kirashi yana sallar farillah ba zai amsa ba, sai idan agaji suka nema daka gareshi."..

     

    Shaik Usaimeen ya ce: Baza ka amsawa ɗaya daka cikin mahaifanka ba idan suka kiraka kana sallar farillah, koda kuwa zasuyi fushi kaki amsa musu, sai dai idan akwai lalura kamar kaga wani koda ba iyayenkaba zaifada halaka, kamar rijiya ko kogi, ko wuta ko wani hatsari da zai iya faɗawa anan wajibine kayanke sallah kowacce ce danka ceci rayuwarsa.

    Sharhin riyazul saliheena shafi na (302).

    Dan haka maganar ba haka take sakaka ba, Akwai ban-bancewar magana, idan ta nafilace za ka yanke sallah ka amsawa iyayenka.

    Idan tafarillah ce baza ka Yanke ka Amsa musu ba.

    Sannan magana abanɗaki malamai sun yi saɓani wasu suka ce makaruhine.

    Sahihiyar magana idan uzuri kamar kiran iyaye ko wani uzuri daban za kai magana kana cikin banɗaki.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.