Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Miji Zai Iya Bawa Matarsa Iznin Fita A Koyaushe Ba Tare Da Ta Tambaye Shi Ba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Miji yana iya bai wa matarsa tabbataccen izinin fita zuwa duk inda ta san bai kauce wa ƙaidar sharia ba ko wanda ba zai ɓata masa rai ba, watau ba sai koyaushe ta tambaye shi ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Barin mata suna fita kowane lokaci suna yawo a cikin gari bai dace da koyarwar sahihin addini ba. A ƙaidar addini mace tana fita ne kawai idan akwai larura ko buƙatar fitan. Don haka, abin ba ya rataya ne kawai ga amincewa ko rashin amincewar mijinta ko iyayenta ba. Akwai haƙƙin Allaah ma a cikin abin.

Amma idan miji ya bai wa matarsa tabbatacce ko kafaffen izini irin wannan kuma a bisa sharuɗɗan da aka ambata a tambayar, ba za a ce ya yi ba daidai ba. Tun da dai wani daga cikin haƙƙoƙinsa a kanta ne ya sauke ko ya kayar mata.

Sai dai kuma ya kamata a fahimci cewa: Yin hakan ga wata mace ba abin murna da farin ciki ba ne. Sharri ne a wurin masu fahimta da ladabi da biyayya. Domin mu ƙaddara mahaifinta ne ya gaya mata hakan a lokacin tana zaune a tare da shi a gidansa kafin aurenta, yaya za ta ɗauki wannan maganar? Wannan bai nuna kamar rashin damuwa ko rashin kulawarsa da ita ba?! Wannan bai nuna kamar ya ƙyale ta ne ta yi duk abin da take so kawai ba?!

A wurin mata masu kyakkyawar fahimta miji ya zama a duk lokacin da mace ta tambaye shi fita unguwar da ta dace ya riƙa amincewa yana yarje mata, suna ganin wannan kamar alama ce mai nuna ta fara fita a ransa! To, ina kuma ga wacce ya ce mata: Duk lokacin da kika ga ya dace kawai ki fita zuwa duk inda kika ga ya dace?!

Sannan kuma yaya miji yake ji idan misali matarsa ta tambaye shi zuwa Zariya ko Kano ko Gusau, amma kuma sai ya ji ko ya ganta a Abuja? Tsakanin da Allaah! Yaya yake ji? To ina kuma ga wacce kwata-kwata ba ta tambaye shi ba?! Sai dai kawai bugo masa waya aka yi ana gaya masa cewa, an ga matarka a wurin biki a Abuja ko Maiduguri ko Sakoto?! Don Allaah! A nan, ina ƙauna da kishin da aka san mazan musulmi da shi?!

Wannan tsantsar boko ne kawai, da koyi da ɗabi’u da halayen maciya karnuka da aladu, marasa kishi! Amma ba musulunci ne ko al’adarmu ba.

Lallai miji ya tsoron ALLAH kada ya kasance daga cikin DAYYUS domin yazo cikin hadisin da Nasa'i ya ruwaito cewa: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: “Mutane uku ALLAH ba zai kalle su ba aranar alƙiyama, DAYYUS yana daga ciki. DAYYUS shi ne Wanda baya kishi matarsa, baya kishin ɗiyarsa, baya kishin kanwarsa, baya kishin ahakinsa.

Hakanan kuma kada ya manta faɗin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam cewa: “Dukkanku MAKIYAYA ne, kuma tabbas! za'a tambaye ku akan abunda aka baku KIWO.” [Bukhari da Muslim]

Miji na kwarai jagorane ga alkhairi acikin iyalansa. Yana umurtasu da kyakykyawa yana kuma hanasu mummuna, himmarsa shi ne ya tseratar da kanshi dama iyalan nasa daga fushin Allah zuwa ga yardarsa. Kamar yadda Allah Madaukaki Ya fadi :

 يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا قُوا أَنْفُسَكُمْ وَأَهْلِيكُمْ نَارًا وَقُودُهَا النَّاسُ وَالْحِجَارَةُ عَلَيْهَا مَلَائِكَةٌ غِلَاظٌ شِدَادٌ لَا يَعْصُونَ اللَّهَ مَا أَمَرَهُمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ ٦۝

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku (da iyãlinku daga wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã´iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin da ake umunin su. [Suratu Tahrim : 6]

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments