𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mun sami saɓani da mijina sai nace da
saki a hannu na yake da na dade da rabuwa da shi, sai ya ce yanzu ma ya bani
dama na saki kaina, sai nace na saki kaina saki 1. Yaya matsayin sakin yake?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Toh Ibnu Ƙudama ya tattauna wannan
matsalar dakyau cikin Almugni harma yakawo zantukan malamai da fatawowin
sahabbai akai, wanda ya ce ijma'ine tsakanin malamai cewa idan miji ya cewa
mace nabaki damar ki saki kanki, sekuwa ta saki kanta anan take awajanda aka yi
maganar bata bari sun rabuba setace ta saki kanta toh duk malamai sunce ta
saku. Amma idan se bayan sun rabu kila mijin yaje masallaci yadawo misali se
kawai ta ce yanzu na saki kaina toh jumhur na malamai suka ce bata saku ba
domin damar da aka bata tariga ta yi sanyi. Amma Imam shafi'i dasu Sayyidina
Aliyu suka ce tasaku domin dama ai mijin bece kisaki kanki anan wajan ba kawai
cewa ya yi ta saki kanta. Kuma Ibnu Ƙuduma
ya ce ba a samu wani sahabi ya taɓa cewa inba anan take ta
saki kantaba sakin beyiba babu wannan maganar daga wajan wani sahabi.
Dan haka dai a
dunkule kawai wannan sakin yasaku in sha Allahu. Kuduba Almugni juzu'i na 7
shafi na 308. Ibnul Usaimin shima ya tattauna wannan matsalar acikin littafinsa
Ashsharhul Mumti
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.