Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta Nayi Istighfari Sama Da Ɗari A Rana?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Hadisai sun yi bayanin a kan Istighfaarin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam): Waɗansu sun ce a kullum fiye da saba’in (70), waɗansu kuma ɗari (100) suka ce yana yi. To, ko mutum zai iya yin fiye da ɗari?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Abin da aka rawaito Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana istigfari sau saba'in a rana kamar yadda ya zo a hadisi kuma yana yin guda ɗari hadisi ne sahihi

Abin da malamai sukace shi ne idan mutum lissafawa zai yi, sai yayi koyi da sunnar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yayi yadda Annabi yayi, amma idan mutum ba lissafawa zai yiba ba'a iyakance masa adadin dazai yiba sai yayi sama da ɗari har dubu ko sama da hakama abune budadde Ku nemi gafarar ubangijinku Ku nemi tsarinsa don haka mutum zai iya yin adadi dayawa amma basai ya lissafaba saboda kada riya ta shiga kuma gururi ya shiga cewa shi yakai wani.

Addini dai a asali shi ne addinin Allaah wanda Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya zo da shi, kuma ya koyar da shi ga Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum). A kan shi ya wajaba kowane musulmi ya tsaya babu ƙari a kansa kuma babu ragi. Kuma shi ake koyarwa da karantarwa ga mutane ban da duk abin da ba shi ba.

Amma bayan tabbatar da haka da kuma yin aiki da hakan idan wani mutum shi ga kansa ya ga yana da karsashi da sha’awa a kan wani aikin alkhairi, kamar yawaita nafilolin sallah ko azumi ko tilawa ko zikiri da makamantansu, don haka sai ya ƙara wa kansa fiye da yadda ya ke a cikin nassi, to babu laifi, in shaaal Laah. Matuƙar dai bai ci karo da wani hani da ya zo kai-tsaye a kan hakan ba, kuma wannan aikin bai shagaltar ko ya sa aka tawaye wata farilla ba, kuma bai ɗauke shi muhimmin abin da yake ƙoƙarin shaharta shi da yayata shi a cikin jamaa, kamar ta koyar da shi gare su ba, ta yadda daga baya zai zama kamar kishiya ga koyarwar Sunnah ba.

Domin an samu waɗansu daga cikin malamai a da sun yi irin waɗannan ayyukan ga kansu, kamar yadda wani daga cikinsu ya sauke Alqur’ani a cikin ranaku uku ko biyu ko ɗaya. Wani ma an ce a tsakanin Azahar da La’asar ya sauke, wani kuma a tsakanin Maghriba da Isha’i. (Dubi: An-Nawawiy a cikin At-Tibyaan Fee Adaabi Hamalatil Qur’aan, shafi: 59-60)

Bayan kuwa duk mun san maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:

« لَمْ يَفْقَهْ مَنْ قَرَأَ الْقُرْآنَ فِى أَقَلَّ مِنْ ثَلاَثٍ »

Duk wanda ya karance Alqur’ani a ƙasa da kwanaki uku, to bai fahimce shi ba. (Sahih Ibn Maajah: 1458)

Haka kuma an samu wanda yake yin sallah a cikin dare ba da lissafin adadin raka’o’inta ba. Sai ya yi ta zubawa kawai, idan ya gaji ko idan Asubah ta yi sai ya yi raka’a guda a matsayin Wutri. Duk kuwa da hadisai sahihai sun zo suna tabbatar da cewa:

مَا كَانَ رَسُولُ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - يَزِيدُ فِى رَمَضَانَ وَلاَ فِى غَيْرِهِ عَلَى إِحْدَى عَشْرَةَ رَكْعَةً

Ko a Ramadan ko ba a Ramadan ba, Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba ya ƙarawa a kan rakaoi goma sha-ɗaya. (Sahih Al-bukhaariy: 1147)

Wani daga cikinsu kuma a kullum Azumin nafila yake yi, in ban da ranakun Idi. (Al-Mustadrak: 3/353)

Duk kuwa da hadisin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗi cewa:

« أَحَبُّ الصَّلاَةِ إِلَى اللَّهِ صَلاَةُ دَاوُدَ - عَلَيْهِ السَّلاَمُ - وَأَحَبُّ الصِّيَامِ إِلَى اللَّهِ صِيَامُ دَاوُدَ ، وَكَانَ يَنَامُ نِصْفَ اللَّيْلِ وَيَقُومُ ثُلُثَهُ وَيَنَامُ سُدُسَهُ ، وَيَصُومُ يَوْمًا وَيُفْطِرُ يَوْمًا »

Mafi soyuwar sallah a wurin Allaah ita ce sallar Annabi Daawud (Alaihis Salaam), kuma mafi soyuwan azumi a wurin Allaah shi ne azumin Annabi Daawud (Alaihis Salaam). Ya kasance yana yin barcin rabin (1/2) dare, kuma ya tsaya sallah na sulusin (1/3) dare, kuma ya yi barcin sudusin (1/6) dare. Kuma yana yin azumin yini guda, kuma ya ajiye azumin yini guda. (Sahih Al-Bukhaariy: 1976)

Duk waɗannan ayyuka ne na ɗaiɗaikun malamai a za munan da suka shuɗe, wanda kowannensu ya yi ne ga kansa, amma ba tare da yin kira ga jama’a cewa a yi koyi da shi a cikinsu ba.

Maƙalƙale wa irin waɗannan ayyukan na malamai, da koyar da su ga mabiya, da ƙoƙarin kafewa a kansu ban da Sunnah, shi ya kai ga yaɗuwar wurudodi na bidi’a da mabiya ɗariƙoƙi su ke a kansu a yau. Kuma kowa yana ganin yadda suka fi fifita su a kan bin abin da Sunnah Sahihiya ta koyar.

Don haka, nasiha kyakkyawa ta gaskiya ga al’umma ita ce, maimakon nacewa da zaƙewa da wuce wuri a kan irin waɗannan zikirorin gara mutum ya tsare, kuma ya kafe kansa da jama’arsa a kan abin da Sunnah Sahihiya ta koyar kawai. Ya kiyayi zaƙewa ko wuce-iyaka a cikin hakan.

Malamai sun nuna cewa: Duk lokacin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya koyar da wani aikin alkhairi a Sunnah, to akwai hanyoyi biyu da sheɗan yake bi don janye mutane daga bin wannan Sunnar:

(i) Wanda sheɗan ya ga mai lalaci da ragwanci ne, sai ya ja shi ga kasala da nauyin jiki wurin aikin, ta yadda zai hana shi kai wa ga cika abin yadda ake so.

(ii) Wanda kuma ya gan shi mai karsashi da ƙwazo ne sai ya zuga shi, ya ƙara masa ƙaimi, ta yadda zai riƙa ganin sai ya wuce inda Sunnah ta tsayar da shi.

Don haka, dole kowannenmu ya riƙa taka-tsantsan, kuma ya yi hankali kar a shige cikin ƙullin yaudara da makircin sheɗan.

A taƙaice dai, kowane musulmi ya riƙa tuna wasiyyar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) wadda ya riƙa yi wa sahabbansa kusan a kowace ranar Jummaa da kuma farkon kowane jawabinsa gare su, cewa:

« إِنَّ أَصْدَقَ الْحَدِيثِ كِتَابُ اللَّهِ ، وَأَحْسَنَ الْهَدْىِ هَدْىُ مُحَمَّدٍ ، وَشَرَّ الأُمُورِ مُحْدَثَاتُهَا ، وَكُلَّ مُحْدَثَةٍ بِدْعَةٌ ، وَكُلَّ بِدْعَةٍ ضَلاَلَةٌ ، وَكُلَّ ضَلاَلَةٍ فِى النَّارِ »

Haƙiƙa, mafi gaskiyar labari shi ne: Littafin Allaah, kuma mafi kyawun shiriya shi ne: Shiriyar Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), kuma mafi sharrin al’amura shi ne: Ƙirƙirarrunsu, kuma kowace ƙirƙira bidia ce, kuma kowace bidia ɓata ce, kuma kowace ɓata tana cikin wuta. (Sahih An-Nasaa’iy: 1578) Allaah Ta’aala ya tsare mu daga duk aikin da ke kai wa shiga Wuta.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments