Ticker

6/recent/ticker-posts

Saki Don Ƙanƙantar Al’aurar Miji

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ina hukuncin macen da take neman miji ya sake ta saboda ƙanƙantar alaurarsa, shi kuma ya ce wai sai ta mayar masa da rabin sadakinsa da rabin kayan lefe?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

A cikin littafan Fiqhu (kamar Tamaamul Minnah: 3/75-78), malamai sun tabbatar da cewa akwai wasu cututtuka ko larurori da idan aka samu ɗaya daga cikin ma’aurata da su a bayan auren, to an bai wa abokin zama zaɓin neman a warware auren, idan dai ba shi abokin zaman ne ya yi haƙuri, ya amince ba.

1. Wanda yake da yankakken azzakari.

2. Wanda ba ya iya saduwa kwata-kwata.

3. Wanda aka yanke masa maraina.

4. Wanda marainansa suka tsiyaye.

5. Wadda gabanta ya toshe.

6. Wadda wani nama ya toho a cikin gabanta.

7. Wadda mafitsara da gabanta suka haɗe.

8. Wadda naman da ke tsakanin mafitsara da gabanta ya kumbura.

9. Mace ko namijin da aka gano yana da cuta, irin: Hauka ko kuturta da makamantansu.

10. Sai kuma cuta irin na zamani, kamar HIV AIDS da Sikila da Hanta da Kansa da makamantansu ko mafiyansu.

Idan a bayan tarewa aka gano abokin zaman aure yana da ɗaya daga cikin waɗannan larurorin, to ya halatta ya nemi a warware auren a tsakaninsu. Kuma mijin ba shi da haƙƙin neman a mayar masa da sadakinsa matuƙar dai ya riga ya sadu da ita. Amma idan waliyyinta ya yaudare shi ne, ya ɓoye masa larurar to shi ne zai biya shi sadakin.

Amma ƙanƙantar alaura - kodayake wasu sun ambace shi a cikin fassarar Inneen - amma dai sahihiyar fassararsa ita ce: Wanda ba ya iya saduwa da mace kwata-kwata. Domin malamai irin su - As-Shaikh Ibn Al-Uthaimeen (Rahimahul Laah) - sun yarda cewa, har wanda ke iya saduwar ko da sau guda a shekara ma ba za a ce masa ‘Inneen’ wanda matarsa take da ikon neman a warware aurenta da shi ba. Don haka, ƙanƙantar alaura ba matsala ce irin ta mutuwar alaurar ba, matuƙar dai yana iya yin amfani da ita a wurin saduwa.

Sannan kuma wannan matsalar ba ta daga cikin larurar da za a zargi miji ko maɗaurin aurensa da laifin ɓoye shi daga matarsa, balle a neme shi da biyan sadaki. Tun da dai kafin ɗaura aure da tarewa babu yadda shi kansa mijin zai san cewa al’aurarsa za ta dace ko ba za ta dace da matar da zai aura ba.

Amma idan a bayan tarewa mace ta gano cewa mijin bai yi mata yadda take so ba, to matakin farko dai shi ne ta yi haƙuri kawai a cigaba da zama da shi a haka har zuwa shiganmu cikin Aljannah. Saboda hadisin Annabi (Sallal Laahu Alalihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya ce:

الْمُخْتَلِعَاتُ هُنَّ الْمُنَافِقَاتُ

Mata masu neman khul’i, su ne munafukai. (Sahih Al-Jaami’: 6681)

Idan kuma ba za ta iya jurewa ba, to tana iya ɗaukar matakin rabuwa da shi ta hanyar khul’i. Tun da dai shari’a ta halatta mata yin hakan a lokacin da ta ƙyamaci ɗabi’a ko halittar mijin, kuma ta ji tsoron afkawa a cikin saɓon Allaah ta dalilin rashin yin biyayya ga mijin.

Al-Imaam Al-Bukhaariy ya riwaito (lamba: 5276) daga Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) cewa:

Matar auren Thaabit Bn Qaysin Bn Shummaasin ce ta zo wurin Annabi (Sallal Laahu Alalihi Wa Alihi Wa Sallam) ta ce: Ya Manzon Allaah! Ba na sukan Thaabit a kan sakaci da addini ko munana wata ɗabi’a, amma dai ina tsoron kafirci ne a bayan Imani. Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alalihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« فَتَرُدِّينَ عَلَيْهِ حَدِيقَتَهُ »

To, za ki mayar masa da lambunsa?

Ta ce: E. Sai ta mayar masa.

Kuma sai ya umurce shi da ya rabu da ita.

Sannan malamai sun sha bamban a kan ko zai iya karɓar fiye da sadakin da ya ba ta? Waɗansu sun amince, saboda ayar Surah Al-Baqarah: 229 Musamman idan ya zama babu wani cuta a fili da yake yi mata, kuma idan ya zama a halin da sadakin aure ya yi tsada ne.

الطَّلَاقُ مَرَّتَانِ ۖ فَإِمْسَاكٌ بِمَعْرُوفٍ أَوْ تَسْرِيحٌ بِإِحْسَانٍ ۗ وَلَا يَحِلُّ لَكُمْ أَنْ تَأْخُذُوا مِمَّا آتَيْتُمُوهُنَّ شَيْئًا إِلَّا أَنْ يَخَافَا أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ اللَّهِ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ اللَّهِ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا فِيمَا افْتَدَتْ بِهِ ۗ تِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ فَلَا تَعْتَدُوهَا ۚ وَمَنْ يَتَعَدَّ حُدُودَ اللَّهِ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ ٩٢٢۝

Saki sau biyu yake, sai a riƙa da alheri, ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka bã su, fãce fa idan su (ma´auran) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba. Idan kun (danginsu) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to, bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne sabõda haka kada ku ketare su. Kuma wanda ya ƙetare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne azzãlumai. (Surah Al-Baqarah: 229)

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments