Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba A Aurar Da Yarinya Sai Da Yardarta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salamu Alaikum, ’Yar makaranta ce, suna tare da saurayinta yau kusan shekaru uku, sai kuma aka ce za a yi mata haɗi da wani danginta. Mahaifiyarta ma ba ta amince ba. Bayan wannan sai kuma yayar mahaifiyarta ta bugo waya cewa, ta yi mata miji, za ta turo shi su gaisa! Shi ne take neman shawara: Idan ta amince, ba ta bi son-zuciya ba? Ba ta zalunci saurayinta na-farko ba? Kuma ba ta zama maciyar-amana ba? Tana neman a taimake ta da mafita.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

 Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

[1] Da farko ya kamata iyaye su san cewa, ba a yi wa yarinya budurwa aure a addini sai da amincewarta da yardarta, kuma da wanda take so. Dalilai a kan haka suna da yawa, kamar wannan:

Abu-Sa’eed (Radiyal Laahu Anhu) ya ce: Wani mutum ne ya zo wurin Manzon Allaah (Sallal Laahu ’Alaihi wa Alihi wa Sallam) da wata ’yarsa, ya ce: Wannan ’yar tawa ta ƙi yarda ta yi aure!

Sai Annabi (Sallal Laahu ’Alaihi wa Alihi wa Sallam) ya ce: Ke kuwa ki bi maganar mahaifinki mana!

Sai ita kuma ’yar ta ce: A’a! Har sai ka gaya mini: Menene haƙƙin miji a kan matarsa!

Ya ce: Haƙƙin miji a kan matarsa: Ko da yana da ƙazzuwa a fatar jikinsa sai ita kuma matar ta sa harshenta duk ta lashe shi, ko kuma ko da wata tsutsa ko jini yana gangarowa daga cikin hancinsa, sai ita kuma ta sa harshenta ta lashe shi, to da kuwa ba ta biya haƙƙinsa ba!

Da ta ji haka sai ’yar ta ce: Na rantse da wanda ya aiko ka da gaskiya! Ba zan yi aure ba!

A nan ne sai Manzon Allaah (Sallal Laahu ’Alaihi wa Alihi wa Sallam) ya ce:

لَا تُنْكِحُوهُنَّ إِلَّا بِإِذْنِهِنَّ

Kar ku aurar da su sai da yardarsu.

 (Ibn Abi-Shaibah: 17116 ya riwaito shi kuma Hasan ne, in ji mai littafin Sahih Fiq-his-Sunnah: 3/71).

Wannan ya nuna:

1. Ba dole ne sai mace ta yi aure ba, matuƙar dai ta iya kare kanta daga alfasha.

2. Ba a yarda iyaye su tilasta yarinya a kan yin aure ba.

3. Ba a aurar da yarinya sai da yardarta.

Don haka, idan aka samu iyaye ko wani maɗaurin auren mace ya nemi takura mata a kan sai ta auri wanda ba shi take so ba, to bai yi daidai ba. Ya saɓa wa irin waɗannan nassoshin na addini.

Matakin ɗauka a nan shi ne: Alƙalin kotun musulunci mai adalci ya fitar mata da haƙƙinta, a lokacin da dukkan hanyoyin sulhu suka gagara.

Amma kuma abu ne mummuna a wurin jama’armu ’ya ta kai ƙaran mahifinta kotu a kan komai. Saboda a alada - ba a addini ba - an ɗauka wulaƙanci da cin-mutunci mafi girma shi ne: Ka kai mutum ƙara kotu! Don har yana aukar da gaba tun daga kakanni har zuwa ga iyaye da yaya da jikoki!

Shiyasa a nan, dole ita mace ta yi taka-tsantsan a kan wannan al’amarin, don kar kilu ta jawo bau!

[2] Sannan dole ita ma yarinyar ta tambayi kanta: Shin wannan saurayin da suka yi shekaru uku suna tare iyayenta sun san da shi? Ta kawo shi wurinsu a matsayin wanda za ta aura? Iyayen sun amince kuma sun yarda da halayensa da ɗabi’unsa a matsayin miji na-gari ga ’yarsu? Ko kuwa dai ita ce kaɗai da wasu ƙawayenta suka san wannan ƙullin soyayyar a tsakaninsu? Idan haka ne, to gaskiya ba za a zargi iyaye ba, idan suka nemi su aurar da ita ga wanda suke ganin ya dace. Tare da sanin cewa sai sun nemi izininta da yardarta kafin auren.

A kullum shawarar da muke bayarwa ga samari da ’yan mata ita ce: Su daina gaggawar ƙulla soyayya a tsakaninsu da juna ba tare da sani da amincewar iyayensu da manyansu ba. Domin ko ba komai ai abin da babba ya hango daga zaune, yaro ko rimi ya hau ba zai iya hango shi ba, kamar yadda ake cewa.

Kin mutunta kanki da iyayenki a wurin kowa idan kika fara sanar da iyayenki kafin ki amince da duk mai nemanki a lokacin da ya gabatar da kansa a wurinki. Sannan kuma a kullum gara ki auri wanda ya fi sonki fiye da wanda kika fi sonsa, domin shi zai fi yin haƙuri da juriya a kan wasu yan kura-kuranki da munanawarki gare shi fiye da wanda kika fi so.

[3] A gaskiya! In dai tun farko iyayenki ko maɗaura aurenki ba su san maganar saurayinki a tsawon shekaru uku da kuke tare ba, to kun yi kuskure, kun faɗa a cikin laifi.

Don haka, yanzu sai ki gaya musu halin da kike ciki. Idan kuma suka kafe a kan matsayinsu, to ni ina ganin ki yi haƙuri ke kanki, sannan ki ba saurayinki haƙuri shi ma, ki dawo ki bi maganar iyayenki, don a zauna lafiya.

Kuma shi kansa saurayin naki ba zai ƙi yarda da hakan ba: Ba zai ce kin bi son-zuciya ba, kuma ba ki zalunce shi ba, sannan ba ki zama maciyar-amana ba! Maƙukar dai yana son ki da gaske ne. Tun da dai ya san ba za ki iya ɗaura auren kanki gare shi da kanki ba tare da yardar iyayenki ba. Shi ma kansa ba zai iya aurenki ba da yarda da amincewar iyayensa ba, in dai har shi ɗin na-kirki ne da gaske.

Allaah ya taimake mu gaba-ɗaya, ya datar da mu ga abin da yake so kuma yake yarda da shi a cikin maganganu da ayyuka.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments