Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halata In Nemi Maganin Farin-Jini?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, shin ya halata mace ta nemi maganin farin jini don samun mijin aure?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

A'a wannan baya daga abinda musulunci yakoyar. idan kuka biyewa irin waɗannan abubuwan zaku shiga bin bokaye da makamantansu.

Saboda haka idan har mace tanason aure to tagyara halayyarta kuma taji tsoron Allah, ta yi addu'a  In shã Allahu za ta samu mijin aure.

Sannan yawancin abinda yake kawo rashin samun miji akwai sawa kai buri ko kuma raina wanda Allah yakawo wajanki idan mace za ta yi aure karta sake ta ce sai mai kuɗi za ta aura abinda za ta fahimta aure ibada ne arziki da taulaci duk daga ubangiji suke dan haka idan mace za ta yi aure tasamu ma'abucin addini wannan ne zaisa taji daɗin zaman aure arayuwarta.

Sannan rashin aure da wuri bawai bakin jini ba ne haka Allah yake tsarawa kowa rayuwarsa wata ta yi aure da wuri wata kuma tadade batayi ba Amman ubangiji shi ne masani akan yadda yatsarawa kowa rayuwarsa dan haka kiyi hakuri kiyi addu'a kuma muma muna tayaki addu'a Allah yakawo miki mijin aure nagari dake da sauran matan musulmi baki ɗaya masu aure kuma Allah yabasu zaman lafia amin.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments