𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam
Alaikum. Idan Sujudul Ƙabliyyah
ta samu mutum, kuma ya manta bai yi ba har sai da ya yi sallama, yaya zai yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Ramatul Laah:
Asali dai idan
mutum ya yi ƙari a cikin sallah Sujada Ba’adiyyah yake yi. Idan kuma ragi ne ya yi, ko ragi da ƙari
a haɗe sai ya yi
Sujada Ƙabaliyyah.
Sannan idan
mutum ya manta da Sujadar Ba’adiyyah malamai sun yarda cewa, lallai ya yi ta a
duk lokacin da ya tuna. Haka ma Ƙabaliyyah
da ya manta bai yi ba sai a bayan sallama ya tuna, malamai sun yarda ya yi ta a
bayan sallamar, ta zama Ba’adiyyah kenan.
Ko ba komai
dai, akwai malaman da suka yarda da halaccin yin kowanne daga cikin Sujadar ko Ƙabaliyyah ko Ba’adiyyahi
a kan kowace irin Rafkanuwa:
Al-Haafiz Ibn
Hajr ya ce:
وَرَجَّحَ الْبَيْهَقِيُّ طَرِيقَةَ التَّخْيِيرِ فِي سُجُودِ السَّهْوِ قَبْلَ السَّلَامِ أَوْ بَعْدَهُ وَنَقَلَ الْمَاوَرْدِيُّ وَغَيْرُهُ الْإِجْمَاعَ عَلَى الْجَوَازِ وَإِنَّمَا الْخِلَافُ فِي الْأَفْضَلِ وَكَذَا أَطْلَقَ النَّوَوِيُّ.
Al-Baihaƙiy ya rinjayar da hanyar
zaɓi a cikin Sujudar
Rafkanuwa kafin sallama ko a bayan sallama. Kuma Al-Maawardiy da waninsa daga
cikin malamai sun ciro ijma’in malamai a kan halaccin hakan. Sun yi saɓani ne kawai a kan wanda
ya fi. Haka kuma shi ma An-Nawawiy ya faɗi
maganar a sake. (Fat-hul Baariy: 3/94).
Shi kuma
An-Nawawiy ya ce:
قَالَ الْقَاضِي عِيَاضٌ رَحِمَهُ اللَّهُ تَعَالَى وَجَمَاعَةٌ مِنْ أَصْحَابِنَا: وَلَا خِلَافَ بَيْنَ هَؤُلَاءِ الْمُخْتَلِفِينَ وَغَيْرِهِمْ مِنَ الْعُلَمَاءِ أَنَّهُ لَوْ سَجَدَ قَبْلَ السَّلَامِ أَوْ بَعْدَهُ لِلزِّيَادَةِ أَوِ النَّقْصِ أَنَّهُ يُجْزِئُهُ وَلَا تَفْسُدُ صَلَاتُهُ وَإِنَّمَا اخْتِلَافُهُمْ فِي الْأَفْضَلِ، وَاللَّهُ أَعْلَمُ .
Al-Ƙaadiy Iyaadh (Rahimahul
Laah) da waɗansu
daga cikin malaman mazhabarmu sun ce: Babu saɓani
a tsakanin waɗannan
malaman da suka saɓa
wa juna da waɗansunsu
cewa, ya wadaci mutum idan ya yi sujada kafin ko a bayan sallama domin ƙari
ko ragi, kuma sallarsa ba ta ɓaci
ba. Saɓaninsu dai
kawai a kan wanda ya fi ne. (Sharhun Nawawiy: 5/56-57).
WALLAHU A'ALAM
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.