Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Kamu Da Matsalar Istimna'i

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam malam. Nayi aure shekaru 3 kenan tun kafin nayi aure nake fama da jarabawa na Istimna'i har yanzu nakasa rabuwa da shi nasan kuma haramun ne abinda ya fi damuna shi ne bansan ta yadda na iya wannan abin ba kawai tsintar kaina nayi aciki kuma dana gama sai in tsinci kaina cikin nadama da kunyar ubangiji na narasa yadda zan rabu da wannan abu kuma ina fama da matsalar namijin dare A dalilin haka nayi ɓari sau uku yanzu inada ciki haihuwa ko yau ko gobe. Amma nakasa rabu da wannan abu kuma yanzu bana mafarki da namijin daren sedai inyi mafarki mata na biya wa junan su bukata to idan ba na dage ba ina farkawa senayi don Allah ataimake ni da addu'a har ruƙya an taɓa yi min amma ba abinda naji.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikis salam wa rahmatullahi.

Istimna'i haramun ne bisa ittifakin Maluman Mazhabin Malikiyyah da kuma mafiya rinjayen Malaman Musulunci, bisa dogaronsu da ayoyin cikin suratul Mũminun da suratul ma'arij wajen da Allah yake bayanin siffofin bayinsa Muminai, ya ce:

وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ ٥۝ إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ ٦۝ فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ ٧۝

Bayin Allah nagari Sune waɗanda dangane da farjinsu suke kiyayeshi. Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka (kuyanginsu) to lalle sũ bã waɗanda ake zargi ba ne. Sabõda haka wanda ya nemi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetarewar haddi. (Suratul Mũminun 5-7)

Da kuma ayar suratun nur inda Allah Subhanahu wa ta'ala yake cewa:

وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ

Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu (daka aikata zina) wannan shi ne abunda ya fi tsafta agaresu (sūratun Nuur: 31)

Kuma tabbas bincike ya tabbatar da cewa istimna'i yana haddasa illoli ga zuciya da dabi'a da lafiyar jikin Ɗan Adam.  Kuma yakan janyo ma masu yinsa matsaloli masu yawa. Tun daga ciwukan jiki da kwakwalwa, har zuwa kan shafar aljanu.

Koda yake bisa fahimtar da nayi wa bayananki, naga alamar tabbas akwai shafar Aljanu tare dake Kuma su suke haifar miki da mafarke-mafarken, tare da ingiza zuciyarki zuwa ga saɓa wa mahaliccinki.

Amma duk da haka ya zama wajibi kiji tsoron Allah Subhanahu wa Ta'ala, ki rika kallon kusancinsa gareki, kuma cewa Shi mai shaida ne bisa ayyukan bayinsa. Yana kallonki duk lokacin da kika ɓuya domin yin wannan mummunan abun. Kuma ki rika tuna ranar gamuwarki da shi.

Cewa anyi miki ruƙyah sau ɗaya ba'a kama aljanun ba, ba hujjah ce dake nuna cewa basa jikinki ba. Domin akwai mutanen da akan shafe sama da shekara guda ana yi musu ruƙyah kafin a samu nasarar kamawa ko Ƙona Shaiɗanun dake tare dasu.

Don haka kije kici gaba da neman magani tare da bin irin shawarwarin da muke bayarwa anan

Yawaita karatun Alƙur'ani da salati da zikirin Allah ko yaushe. Musamman lokutan barci da kuma safiya da maraice.

Ki nemi Man Habbah ki tofa fatiha, ayatul kursiyyi, suratul feel, (Li'eelafi) Ƙul Huwallahu, falaƙi da nasi kamar Ƙafa 3-3. Ki rika shan cokali guda safe da yamma, kina shafe jikinki da shi. Sannan ki rika shan Na'a-Na'a domin samar da lafiya ga jaririn dake cikinki.

Allah ya sawwake, ya shiryeki ya baki lafiya damu baki ɗaya, ameen.🤲

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments