Ticker

6/recent/ticker-posts

Sauyawar Harufa Cikin Kalmomi

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

609. Nahawun Hausa ya amince da rubutun,

 Hausawa ko sun bi tsarin tun-tun-tun,

 Sun yadda su kyautata wa masu karatun,

 Kuma sun ce a zo da tsari na rubutun,

  Wasu harufa cikin gaɓa mai sauyawa.

 

610. Wasu harufa sukan shige wasu halaye,

 Dus sanda ka gan su malam ka kiyaye,

 Kai azama ka lura, inda sun kai tawaye,

 Don da yawa waɗansu ka gan su a sauye,

  Sai su fito daban-daban tun farawa.

 

611. Sauyawar cikin gaɓa ɗaya aka yin ta,

 Malam lura ka ga sauyi a cikinta,

 Ƙari za ya zo ka duba, ka rubuta,

 Tai daidai ya zan gaɓar an sauya ta,

Kuma ta zamo gaɓa ta ƙarshen ƙarewa.

 

612. Duk harufan da wagga doka tas shafa,

 Tilas su kasantu sun bi tsari ba ƙanfa,

 Babu guda wanda zai zame bai da madafa,

 Matuƙar dai baƙi yana nan bagiren fa,

Wasula masu bin ta su za su gwadawa.

 

613. Doka ta aminta in za a rubutu,

 Sai a kula kar a duba tsarin sabbatu,

 Ba ma’ana gare su, su masu karatu,

 Ko sun ga abin da an ka zana na rubutu,

A riƙa kula da sauye-sauye da ka zowa.

 

614. Ga su guda-guda a nan zan kawowa,

 Babu hayaniya, a bar zance kuwwa,

 Malam bari hanzari ka bar yin gaggawa,

 Zan zano su yadda ba sa rikitarwa,

  Sai a kula da hankali don ganewa.

Post a Comment

0 Comments