Ticker

6/recent/ticker-posts

Sauyawar Harafin /d/ Zuwa /j/

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

615. Harafin d idan wasullan da ka bin sa,

 Sun shiga inda za su motsa shi dukansa,

 Sun ka amince a ba shi damar furucinsa,

 Wato dai ina nufin wasullan da ya ƙunsa,

‘A’, “O”, “U”, a nan wurin zai nunawa.

 

616. In kalma tana da d can daga ƙarshe,

 Sauyawar akan gane a can tarshe,

 Doka ta aminta sauya gaɓar ƙarshe,

 Ma’ana za ta kumbure, sai ta yi reshe,

  Gun jam’inta nan abin zai sauyawa.

 

617. In ka ce “gado” tilo ne ka kiyaye,

 Kullum ƙudurin sayensa na nan ga iyaye,

 In kuma babu shi amarya sai tai ta hawaye,

 Kalma ce guda, aboki kan ka yana waye,

  Jam’in nasa ko “gadaje” ka biyowa.

 

618. In ka ce “gada” da mota ka hayewa,

 Waggana wadda a’ akwai hanyar Yalwa,

 Can Jaba na gane ta, ta fi misaltawa,

 Kalma ce guda gada mai sauyawa,

  Jam’in nata ko “gadoji” aka cewa.

 

619. Lura da kyau “gida” tilo ne ga zubinsa,

 Duk mai rai a yau yana da muradinsa,

 Ko sun yi yawa gare shi ko ma don gasa,

 Ita kalmar gida guda ce, furucinsa,

  In kuma sui yawa “gidaje” aka cewa.

 

620. Gwadda  na da kyau ga mai buɗin baki,

 Shi mai azumi yana muradin yanka ki,

 Malam sa wuƙa ga gwadda ba birki,

 Na matsu in gane ta in kai ta ga baki,

  Gwaddoji saman tire sai yankawa.

 

621. Farda kasuwar ice aka samunta,

 Had da arakke duk ana ɗaɗɗaurata,

 Bata-bata a kai, a kai ta a saida ta,

 In sun yi yawa ga jam’u nan aka sauyata

  Fardoji ga jam’u shi aka zanawa.

622. Ga misalan ga duk biyar in ka kiyaye,

 An zano tilo da jam’unsu ƙawaye,

 An bayyana kowanensu kai ya waye,

 Lura da kyau waɗanda kag gan su a lauye,

  Da tilo ne gami da jam’i aka sawa.

 

623. Harafin d a gun tilo in ka kiyaye,

 Shi ka zuwa ya girke tanda ya yi toye

 Gun jam’unmu bai zuwa sai ya yi ɓoye,

 Bai ɓoye ba, na ga an sa shi a sauye,

  Ya zama j ga jam’u can gun tsarawa.

Post a Comment

0 Comments