Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Shan Magani Don Rage Girman Halitta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Shin ko akwai laifi idan mutum ya sha magani don ya rage girman wata halittar da Allaah ya yi masa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

A asali sauya halittar Allaah haram ne, kamar yadda ya faɗa a cikin hadisin Al-Bukhaariy (5943) da Muslim (2125) daga riwayar Ibn Mas’uud (Radiyal Laahu Anhu) cewa:

Allaah ya la’anci mata masu yin zane a jiki da masu neman a yi musu zanen; kuma da mata masu aske gashin gira da masu neman a aske musu; kuma da mata masu neman a yi musu wushirya domin ƙarin kyau, masu sauya halittar Allaah.

Al-Haafiz Ibn Hajr a cikin Fat-hul Baariy: 1/372-373 ya ce: Daga nan ake fahimtar cewa abin zargi kawai yana ga wacce ta aikata hakan domin ƙarin kyau ne. Amma idan ta buƙatu gare shi, kamar misali domin yin magani, to ya halatta.

Don haka, duk wanda ya sha wani magani na halal domin ya rage girman wata halittar da Allaah ya yi masa, ba za a ce ya yi laifi ba, matuƙar dai wannan abin yana takura masa yana cutar da shi a rayuwarsa. Kamar wanda haƙora suka fito masa zaƙo-zaƙo, ko kansa ya yi girma sosai fiye da ƙima. A asali abin da ya kamata shi ne mutum ya yi haƙuri da yadda Allaah ya halicce shi kawai, in dai ba abin ya takura masa ko yana cutar da shi a cikin rayuwarsa ba ne. In ko ba haka ba, ya samu ya bi duk wata hanya ta halal wurin maido da halittar yadda ta dace. Wannan ba sauya halittar Allaah ba ce, kuma ba ƙarin kyau ba ne.

Dubi As-Shaikh Ibn Al-Uthaimeen a cikin Fataawaa Ulamaa’il Baladil Haraam, shafi: 185, kamar yadda ya kawo a cikin Tamaamul Minnah: 4/319.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments