Ticker

6/recent/ticker-posts

Sa'adatu Sa'ar Mata

In ka kusan jama'a ta bayan ƙauyuka,
To babu shakka za ka hango dala.

So ya fatattaki zuciya har ta dake,
Na ɗau takobi kansa yau zan falla.

Na kauda tsoro zuciyata ta tsike,
Ba na gudun tsawa bare bulala.

Ƙarfi na so shi ne ya sa ni sadautaka,
Ƙarfen digar jirgi da hannu na ɓalla.

Ban ma tunanin nai hakan ko ban yi ba,
Tamkar biredi na yi shi sala-sala.

Ba na jiran barci bare neman tuwo,
Don sun sani a cikinsu ba mai shalla.

In na tuno rabuwarmu ni da Sa'adatu,
Sai in ji tamkar zuciya tai shela.

Ta faɗawa al'umma abin da ya ke ciki,
Ƙunci na ruhi zuciya tai talla.

Wataran idan na tuna ta sai nai murmushi,
Wataran da nai kewarta sai nai ƙwalla.

Ta nuna so tamkar ɗiya a wurin Uwa,
Adu'a take kullum idan tai salla.

Ta faɗa tana "Rai zuciya na bar maka"
Don sonka ya zarce kuɗi da tagulla,

Ya mamaye min zuciya ya sarƙafe,
Koginsa ya cika babu hanyar ɓulla.

Don duk samari sun gaza kan tsaida ni,
Ni kai kaɗai ne zuciya ta walla.

Nima a zuciya ke kaɗai ce zahiri,
Ko da a kan hanya na gansu kala-kala.

Mun farraƙe kowanmu na goge ido,
So ya rufe kan zuci yai mana illa.

Allah ya ban madadinta zan daɗa godiya,
Haskenta ya taɓa zuci tamkar cocila.

Hotonta ne a saman waya ta lokaci-
Kan lokaci sai na ɗaga shi na kalla.

Ita ce kaɗai mai sanya raina yai fari
Yau gashi ba ta nan ta ya zan sam kula

Ita ce Sa'a, Sa'a ta matan duniya,
Kowa ya samu kamarta ya sam daula 

Maisugar Ringim ✍️ ✍️
12/10/2023
ringimmaisugar@gmail.com
09123098967
Soyayya

Post a Comment

0 Comments