Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
237. Mun
ƙare
baƙi wasulla haka gaɓɓai,
Haɗuwar baƙi, wasal, samun gaɓɓai,
Kalma samuwarta sai an haɗa gaɓɓai,
Ɗauri ma yakan taho
ne kan gaɓɓai,
Mun
ga rawar baƙi da dokar ɗaurewa.
238. Yanzu
taƙaice mun shigo ne a rubutu,
Da akwai
tsare-tsare mai kyau ga rubutu,
Ga kuma ƙa’ida gare shi komi ya kyautu,
Don haka sai mu
duba ƙa’idar nan ta rubutu,
Yadda ake sanin rubutu na haɗewa.
239. Doka mai haɗe rubutu mu gwada ta,
Mui nazari mu sa misalai mu misalta,
Kalmomi
daki-daki za mu fasalta,
Har da waɗansu ‘yan misalai mu rubuta,
Da dalilin haɗe su domin nunawa.
240. Ba a bin abin da duk bai dace ba,
Ba
son rai,
ina gani ne ilmi ba,
Kirdado ba a yi ba, ba ra’ayi ba,
Ba a hawan ƙawara, ba a yo
shirme ba,
Bin doka da ƙa’ida babu laɓewa.
241. Babin
nasu zai fito da fasulla ne,
Za a raba daki-daki ga
bayani ne,
Lura akwai wurin an so a haɗe ne,
Ba a buƙatar rabe shi
domin doka ne,
Bakin
gwargwado ga doka ta haɗewa.
242. Yadda
ake haɗe rubutu hikima ce,
Ita ke rarrabe
rubutu a karance,
Shi ya zam ba kure
da sauƙi a rubuce,
Rubutu ya yi kyau a gane komi a karance,
Don ma’anar abin ta zan daidaicewa.
0 Comments
Post your comment or ask a question.