Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
243. Ita
dai mallaka nufi naka na kanka,
Wanda gare shi babu mai iya kore ka,
Ba a hana ka babu mai iya tauye ka,
Kuma an yadda kai kaÉ—ai ad da abinka,
Ko
wani can ya mallakai babu musawa.
244. In
aka mallakar da komai a wuyanka,
To kai ad da shi ka san ba a hana ka,
In kuma an ka ce a damƙa maka ɗauka,
To ka mallakai, gari
ba ka da tamka,
Ko
aka ba waninka duk rinƙa kulawa.
245. Ita dai mallakar ga zan zo da irinsu,
A misalansu dan ya
zan ka gane su,
Ga su misalce sai
ka duba ka riƙe su,
Dangoginta nawa,
naka, ka gane su,
Kana
muna da naku, ga namu daÉ—awa.
246. Sa
muna nasu, nata, naki, ka ƙirga su,
In da yawa suke da
shi ya zama nasu,
In ko macce ce ta
mallakai nata irin su,
Ko kuma naki yanzu
ke ce da kalar su,
Nasa, da nashi, duk ana iya
zanawa.
247. Dukka
irinsu mallaka sun ka kasance,
Nan zan faÉ—aÉ—a ga jimlar mu ta zance,
Ta sungumi nawa ga idon nata makauce,
Nawa gidan da nasa sai an yi kwatance,
Naka gidan da nata sauƙin
ganewa.
248. Naki da nata ga su nan dai a tsugunne,
Nasu da namu,
duk su ne zaune,
Nashi yana
ga mai ja masa kunne,
Nawa gari da naku
bakin hanya ne,
Nasu garin yana dawa sai ratsewa.
249. Na gano taku malama ga ta a kwance,
Tamu a
yanzu Tanko yaya ta kasance?
In kuma tasu
ta ka gan su suna ƙwace,
Nashi hali haƙiƙa
sai dai a yi dace,
Ko yatsa a baki bai taɓa cizawa.
250. Dokokin ga yanzu kam mun gane su,
Don mun zo da su,
had da misalinsu,
Kalmominsu mun
saka har jimlarsu,
Kalmomin
na mallaka ga bayaninsu,
Biyu-biyu
ne gaɓansu ba mai zarcewa.
251. Za ka ji gun faÉ—i kamar fa a ware su,
Ga su rubuce tare nan an ka game su,
Za ka ji gun fitar su tamkar biyu ne su,
Ga
rubutun dukansu tare ake sa su,
Ka kiyaye dukansu don ba a rabawa.
252. Kar
ka rubuta ‘na’ gabas ‘wa’ na yamma,
Nawa haÉ—e ta za ka yi na sheda ma,
Haka nan namu, nasu, du na ƙara ma,
Nasa, da nashi, tasu, duk na jera ma,
Ba tazara tsakansu can ga rubutawa.
253. Ka kiyaye da Æ™a’ida bari ruÉ—a ni,
Matuƙar
kar raba su ka ƙwaɓe bayani,
Ka barkata mai karatu ya shiga ruÉ—ani,
Shi ya shiga dama
kai ko ka koma hauni,
Ma’anar
duk da kan nufa ba ta fitowa.
254. A misalai da mun ka kawo sheda ni,
Ita dai mallakar
ga nan ba saɓani,
Mun yi ta daki-daki gaba É—ai da bayani,
DaÉ—a na bar ka yanzu
je kai ta tunani,
Na misalan irinsu don tantancewa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.