Ticker

6/recent/ticker-posts

Ruwa Biyu (:)

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

460. Dole mu je mu gai da Sani ɗan Belɗo,

 A yi waƙa da kwaikwayo sai ɗan Belɗo,

 A bi icce a hau saman nai sai yaɗo,

 Dole ka dole don ruwan sama sai kwaɗo,

  Gafiya ba fita garai sai ɓoyewa.

 

461. Lura da kyau idan ka tashi rubutawa,

 Masu karatu su lura nan ga karantawa,

 An yi alamar cikin rubutun Hausawa,

Lura ruwa biyun ɗigo biyu aka sawa,

Ɗaya zai hau saman ɗayan gun zanawa.

 

462. In ka gan shi an rubuta a rubuce,

 Kai ko ka zo kana karatu a karance,

 Sai ka bi ƙa’idar rubutun Hausance,

Amfaninsu sai wurin buɗe zance,

Don a ruwaito yadda mai shi ke cewa.

 

 

463. In aka sa shi sai alamar buɗewa,

 Ita ce ƙa’idar rubutun Hausawa,

 Sauƙi za ya zo ga masu karantawa,

 Don haka zan kula gabanin zanawa,

  Su biyu za su zo ga kalmar farawa.

 

464. Can ƙarshensa sai alamar rufe zance,

 In ka sa ta duk wuya an magance,

 An cika ƙa’idar rubutu a rubuce,

 Za ka gane su can a ƙarshen rufe zance,

  Su biyu za su sake zowa ga rufewa.

 

465.  Makaɗi shi ka tanadin ‘yan turaye,

 Dubi abin da zan faɗa don ka kiyaye,

 Don ka taho da ‘yan ɗigagganmu tagwaye,

 Sai ka saka su, don ka huta kai waye,

  Yadda ake ganin abin zai dacewa.

 

466. Na ji Alu yana faɗin wannan zance,

 Ya ce: “In ka zo da hankali ka yo dace,

 Za mu tsaya mu ba ka saƙo a rubuce,”

Malam ne ya ce: “Haramun tarko ce,

  Duk mai cin ta tabbata bai morewa”.

 

467. Ai nassi ya ce: “Jikin duk da ka cin ta,

 Matuƙar ya sani ya ƙyale don wauta,

 Ko kuma don yana ganin wai riba ta,

 Bai more ma alƙiyama, ku rubuta,

  Za a saka shi gun wuta mai ƙonewa”.

 

468. Ba ka ganin yawan mutanen da ka cin ta,

 Su ke yin hada-hada don sun manta,

 In aka ce ga haram a nan su ka kiranta,

 Ba su gudun wai a ce da su, su ka jiranta,

  Nan duniya cikinmu su ke holewa?

469. A yi kaurin wuya, da faɗi, ga tunbi,

 Su ci daɗi cikin miyarsu akwai zabbi,

 A shigo manya-manya motoci sabbi,

 Manyan riguna, agogo da madubi,

  Ko tafiya sukai jiɓi na karyowa.

 

470. Ranar lahira idan an tara mu,

 Za a yi bincike a gano aikinmu,

 Wasu ko za a ƙwace ladar su a ba mu,

 Sannan wasu za a gan su duk sun damu,

  Sai sun ce: “Ina wurin don ɓoyewa”.

 

471. Rabbu ya ce: “Zabaniyawa ku tsare su,

 Ku riƙe kar ku bar su yanzu a ɗaure su,

 An masu tanadin wuri don a saka su,

 Zaluncin da sun ka yo da ]ai an kama su.”

  Ga sarƙa a ba su domin ɗaurewa.

 

472. Duk a wurin da mun ka ce, “an ce” lura,

 Za mu taho da ‘yar alamar ga ku lura,

 Mun saka ɗan ɗigo-ɗigo biyu mun ƙara,

 Haka nan inda mun ka sa “sun ce” lura,

Ko “ya ce” a nan ruwan za su tahowa.

 

473. In kuma mun saka su sai buɗe zance,

 Domin wanda yaf faɗa shi ya kasance,

 Ya yo zantukan da an sa a rubuce,

 Don haka mun ka sa alamar a rubuce,

Can ƙarshen mu sa makullin kublewa.

 


 

Post a Comment

0 Comments