Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakafi Mai Ruwa(;)

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

450. Waƙafi mai ruwa kamar waƙafi ne shi,

 Duba ka gani wurin faɗi ko sunan shi,

 Ai sun yi guda cikin misalin furta shi,

 Sai dai wanga har ruwa ne ƙarin shi,

  Za a ɗigo samansa don bambantawa.

 

451. Ba a saka shi sai ga jimla tsakiyarta,

 An yo tanadin muhalli na saka ta,

 In aka sa ta ko’ina an ɓata ta,

 Za a saka ta nan ga jimla a rubuta,

In ta kasance mai tsawo mai burgewa.

 

452. Za a saka shi nan ga jimla a gaɓarta,

 Sa ta wurin da zai fi dace a saka ta,

 Doka ce ta sa ta don ba a hana ta,

 Dole a sa ta nan ga jimla tsakiyarta,

Ka ga tsawonta nan wurin bai damewa.

 

453. Jimlolin da za su zo fa misali ne,

 Ado a ƙoƙari fa ya zarce mutane;

 Duk da ƙafa guda garai don gurgu ne,

 Tamkar dai ka ce: “abin nan da yawa ne;

  Amma nai zaton suna iya canyewa.

 

454. Babbar kasuwar garin nan ta Maƙarfi;

 Ba kaya na marmari sai dai kifi.

 A misalin da anka yo ba shi da laifi,

 Haka ma kasuwar garin na Karofi;

  Ba inuwar da ɗan mutum zai hutawa.

 

455. In ba ka gane ba ga misalai ƙari na,

 Na zabura na ga sun kama buguna;

 Kar na biye su har ya zam an yo ɓarna.

Na ga abin yawansa ya wuce ilmina;

  Tsoro yar rufe ni nak kasa taɓawa.

 

456. Duk tsarin da za ka yi ai an yi shi;

 Sai dai gyare-gyare don inganta shi.

 An yi guda sama a nan ƙasa ma ga shi,

Duk maganar da ba ta amfanin mai shi;

  Ban da baƙin jini Alu me taka sa wa?

 

457. Jimlolin ga duk idan kuka rege su,

 Ɗangon fari anka fara bayaninsu,

 Sai na biyunsa za ya zo don ƙare su,

 Lura da kyau akwai alama tsakiyar su,

Za ku ga sun tsawo ga jimlar Hausawa.

 

458. Mun san ƙa’idar rubutu ak kara,[1]

 Don haka wajibin mu sa in mun lura,

 An yi alamar da za ta zamto jagora,

Can tsakiyarsu kan gaɓa in kuka lura,

  Waƙafi mai ruwa ya zo don gyarawa.

 

459. Ba don shi ba da abin ya lalace,

 Ita ce ƙa’idar da taz zo a rubuce,

 In aka sa ta to da sauƙi a karance,

 Duk kuma wanda yaƙ ƙi to ya dabirce,

  Jimlolin zubinsu zai gurɓacewa.[1] Kalmar “kara” na nufin “ado” ko “kwalliya.” An fi amfani da ita a Sakkwato da Kebbi.


Post a Comment

0 Comments