Ticker

6/recent/ticker-posts

Ranar Malamai ta Duniya, 2023

Marubuci: Mukhtar Kobi (08100358411)

Tayani nemo malamai
Masu zance muhimmai
Sun iya tausasa kalamai
Dole ambaton su jarumaii

Tun kana dan karami
Yake koyar dakaii ilimi
Baii zama shine hadimi
Yabo dolene gun malami

Yaje gari har cikin daji
Ilimi ga mace da namiji
Ya ratsa inda aketa gunji
Muradinsa ilimi kowa yajii

Ya dau 'yan wasu nasa
Babu son zuci ko siyasa
Ilimi baya son yaji anrasa
Bishiya na albarka ya dasa

Lokacin zafi ko na sanyi
Cikin lafiya ko ana juyayii
Bai nawa ilimantarwa keyii
Burikan yara gaskatasu yayi

Ya kyautu abasu hakki
Kan lokaci babu jan jikii
Gidajen wasu ba lantarkii
Koyarwa suke cikin shauki

Ilahi albarkaci Ulama'u
Masu jinya basu shifa'u
Dalibai kara musu haya'u
Lahira hadamu da Zahra'u

Ameen Ya Allah🙏

Za a iya tuntubar Mukhtar ta garbakobim@gmail.com
Ranar Malamai ta Duniya, 2023

Post a Comment

0 Comments