Ticker

6/recent/ticker-posts

Dawowar Garkuwa Da Mutane A Yankin Arewacin Nijeriya

Marubuci: Mukhtar Garba Kobi (08100358411)

 Ta’addancin da wasu miyagun mutane keyi na garkuwa da mutane a Arewacin Najeriya na daya daga cikin manyan abubuwan da ke barazana ga zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki, ‘yan fashin daji suna tafka ta’asa a kan tituna, yankuna sai kuma a 'yan kwanakin nan a manyan cibiyoyin ilimi.  Labarin sace wasu manoma da ba a tantance adadinsu ba a jihar Borno da daliban Jami’ar Tarayya dake Dutsen-Ma ya yadu a ‘yan kwanakin nan, iyalan wadanda abin ya shafa na cikin kaduwa yayin da da yawa suka yanke shawarar janye 'ya'yan nasu daga makarantu;  hakika wannan mummunan abu ne duba da muhimmancin ilimi ga dan Adam da ci gaban kowa. Jama’a a wadannan yankuna na nuna shakku da kokonto kan alkawurran da shugabannin suka dauka na kare rayuka da kuma dukiyoyi.

 A kaf fadin duniya babu wanda ya fi karfin doka, a wasu kasashen da suka ci gaba hatta shugabannin da ke kan karagar mulki ana tilasta musu su fuskanci shari’a domin girbar munanan ayyukan da suka aikata a ofisoshi, amma abin takaici a Afirka, kasancewar rigar kariya ga shugabanni shi ke ba su karfin gwiwa yin yanda suke so.  Daya daga cikin shugabannin  ‘yan fashin daji a Arewacin Najeriya wato Dogo Gide ya fitar da wani sakon sautin murya da wani dan jarida mai suna Bello Mu’azu ya watsa, amma sakone don kara ruruta wutar rashin tsaro.  Dogo Gide wanda ya bayyana cewa ya gwammace ya mutu a matsayin dan fashi kuma ba shi da sha’awar sulhu da gwamnati ko da naira nawa za a ba shi.

 Kasantuwar jajirtattun jami'an tsaro suna da masaniya na mafi yawan maboyar ‘yan fashin dajin, za a iya murkushesu su ( wato ’yan bindigar) cikin ‘yan kwanaki kadan amma hakan na karewa a zantukan baka ne zalla. Jagorori na al'ummu sun yi namijin yunƙuri ta hanyar zama masu shiga tsakanin 'yan fashin daji da Gwamnatoci, abin takaici ƙoƙarinsu ya ci tura saboda rikon sakaina daga bangaren Gwamnati.  Babu yadda za a iya kashe wuta da wuta;  amma hada biyun (wato kai hari da tattaunawa) tabbas zai taimaka matuka. Har ila yau, shiga zauren sulhu zai ba da damar samun zaman lafiya a mafi yawan Jihohin da satar mutane yayi kamari, noma gami da kasuwanci zasu dawo da martabar da suka rasa yayin da dalibai za su cigaba da daukan karatu ba tare da fargaba ba.

 Bugu da kari, wani bincike da SBM wanda kamfani ne na bincike ya gudanar ya nuna cewa a tsakanin watan Yuni na shekarar 2022 zuwa Yulin 2023, mutane dubu uku da dari shida da ashirin (3,620) sun fada komar al’amuran da suka shafi garkuwa da mutane cikin hare-hare sau dari biyar da tamanin da biyu (582) a Najeriya.  An kara gano cewa “Yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya sun fi yawan biyan kudaden fansa. Wannan ya yi daidai da kangin talaucin Najeriya da kuma alakar ta da wuraren ke dasu na yawan bukatar abinci.  Kari akan haka, waɗannan yankuna suna fuskantar karuwar buƙatun babura bisa  amfani da su da akeyi don samun kudade ta hanyar ayyukan ta'addanci".

 Wasu daga cikin abubuwan da ke rura wutar garkuwa da mutane sun hada da tsananin talauci da yunwa; mutum kan wayi gari bashi da ko sisi ko abinci da iyali za su ci kan tilasta wa mutane da  dama shiga wannan aika-aika musamman Fulani makiyaya marasa ayyukan yi. Abu na biyu shi ne zalama da tsananin son samun arziqi yasa wasu suka fara garkuwa da mutane;  mutane masu karamin tunani sau da dama suna kallon garkuwa da mutum a matsayin hanya mafi sauƙi don samun isassun kuɗi don biyan bukatunsu na yau da kullum. Masu garkuwa da mutane suna taka muhimmiyar rawa wajen yin tasiri ga abokansu, suna ba abokan da basa son garkuwa da mutane kwararan hujjujo da kwadaita musu aikin, sannan wadanda ke da raunin tunani sukan amince da tayin ba tare da tunani a kan sakamakon da irin wannan hada-hadar ke tattare dashi ba.

 Za a iya dakatar da sace-sacen mutane da idan aka dauki wadannan matakai kamar haka;  tsare-tsare na daukar matasa aiki ko horar da su sana’o’i yakan bar kauyuka da dama kuma akasarin masu garkuwa da mutane mazauna kauyuka ne; akwai bukatar a saka mutanen kauyuka cikin duk sabon tsari da Gwamnatoci suka zo dasu.  Tunda masu garkuwa da mutane suna da shugabanni, akwai bukatar a yi ganawa ta kafar sadarwa ko ta zahiri da su don sanin dalilin da ya sa suke yin garkuwa da mutane, ya kamata Gwamnatoci su tabbatar sun biya musu bukatunsu. Yin afuwa ga masu garkuwa da mutane da suka tuba zai zama abin marhabun amma kada a mayar da su cikin al'umma kai-tsaye, a kai su gidajen gyaran hali domin horar da su sana'o'i daban-daban don su kasance masu amfani a cikin al'umma.

Na yi wannan rubutu ne daga Bauchi kuma za a iya tuntuɓa na ta garbakobim@gmail.com

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments