Photolab Ko Yaudawa

    Wani abu da yake faruwa a kwanakin nan a kan sha'anin gyara hoto ta amfani da manhajar PHOTOLAB wanda mata suka fi yi.

    Wannan al'amari ne na ci gaban zamani, sai dai a wurin mu, ci gaban, na mai haƙar rijiya ne, domin idan aka lura da abin da zai kai ya komo, haihuwar ɗa mara ido kawai ake yi.

    Mako biyu da suka wuce wani abokina ya zo min da maganar yarinyar da suka haÉ—u da ita a kafar sadarwa ta zamani, kuma ya nuna amincewarsa da ya aure ta, har ma yana shirin tura iyayensa garin su (Jigawa). Ya nuna min hotunan da ta turo masa. Tsakani da Allah, ko ki da na ga hotunan yarinyar, in dai maganar zubi da diri da kyawun fuska ne, to sai dai mutum ya yi ta makaho, wai da aka ce masa "ga ido' sai ya ce wari yake yi, saboda ya san ba zai samu ba. Ni ma dai ba domin kada ace wani abu ba, da na ce lallai Æ™irar halittar da Buwayi gagara-misali ya yi mata, sai dai a ce Ma Sha Allah.  Amma dai kafin na goyi bayansa akan wannan Æ™uduri, sai da na matsa masa da ya yi tattaki ya je garin ya gan yarinyar ra'ayal aini domin ai garin masoyi, masoya suka ce ba ya nisa.

    Aka yi sa'a kuwa ya amince da shawarar. Ranar Asabar da ta gabata ya niƙi gari zuwa Jigawa tarin Allah, domin ganin sahibar tasa. Ta riga ta sanar da iyayenta cewa za ta yi babban baƙi daga Zariya birnin Shehu (Allah ya ji ƙansa). Aka shirya tarbar surukin gobe, 'yan uwa da ƙawaye suka yi ta dakon jiran angon Maryam na gobe. Ya isa garin, ya hau acaɓa aka kai shi har ƙofar gidansu amaryarsa da yake mafarki. Ya kira waya ya sanar da ita isowarsa, jimawa kaɗan 'yan mata guda uku suka fito tarbarsa, dukkanninsu cike da fara'a da nuna murna da zuwansa, ai sun kyauta, domin shimfiɗar fuska ta fi ta tabarma. Abinka da sunduƙin namiji, da yake ba makeup yake yi ba, kallo ɗaya suka yi masa suka gane shi, saboda hotunansa da suka saba gani. Amma shi gogan naka fa a tsammaninsa, waɗannan masu masaukin baƙi ne. Ashe amaryar ita ce a gaba, ko gane ta bai yi ba.

    Aka shiga da shi turakar mahaifin, suka yi gaisuwa cikin mutunci da tarba mai kyau, daga nan aka gaggaisa da sauran 'yan uwa da maÆ™wabta, daga Æ™arshe aka kai shi wani É—aki da aka Æ™awata da labulen bango, ga kuma kayan Æ™walam da maÆ™ulashe ne suna masa maraba. Ya sha ruwa ya tanÆ™washe Æ™afa sannan yace wa ita mai yi masa rakiyar ta je ta kira Maryam É—in, shi a tsammaninsa wannan Mero ce. 

    Na taƙaice muku labari dai, Maryam ɗin sa ta hoto ba ita ba ce Maryam ɗin Allah da Annabi, ya yi rantsuwa cewa ita ta zahirin ko tashe aka fita da ita a watan azumi ba ƙananan kuɗi za a tara ba. Yadda ya gan ta ya ce kamar wadda aka yi ɓarin mota da ita. Yanzu dai maganar tura iyaye babu ita, saboda ɓacin rai ma, ko tukwuicin abin arziƙin da aka kawo masa bai bayar ba, wai kuɗin ma da ya kashe na mota ya isa.

    Daga jiya zuwa yau, ya yi mata Allah ya isa ta fi É—ari, ban san yawan wadda ya yi a zuci ba.

    Da wannan nake yi wa mata nasiha, ku ji tsoron Allah ku riƙa bayyana asalin halittar fuskar ku wadda Allah ya yi muku. Wannan PHOTOLAB ɗin ba zai sa ku sami mijin aure ba, yaudara ba ta da rana. Mu kuma maza, mu daina ruɗuwa da kyawun fuska musamman a hoto, mu nema wa 'ya'yanmu iyaye nagari, ba wai mu nemawa kanmu mata kyawawa ba.

    ABOKINA, ALLAH YA ƘARA DANGANA 

    SAI ANJIMA

    Imrana Hamza Tsugugi

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.